Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsirkiya

Tsirkiya

Tsirkiya:- 

Tsirkiya wata ciyawa ce da Allah ya albarkace mu da ita a cikin fadamarmu, wannan ciyawa mai suna tsirkiya ba ta fitowa sai a cikin fadama, a cikin fadamar ma sai wajen da yake da wadataccen sanyi, mafi akasarin a bakin tafki ko baye ko ƙorama ko kuma baƙin gulbi/kogi.
  
 Babu wata dabbar gida da ta daji da bata cin wannan ciyawan ta tsirkiya, tana da juriyan fari kaman ciyawan tofa sai dai tsirkiya bata tashi tsaye ta yi tsaho kaman ciyawan tofa a maimakon haka tsirkiya tana yin yaɗo ne a ƙasa ta bi ƙasa, sayawanta ba sa tsini su shige ƙasa kaman sayawan rogo a'a sayawan tsirkiya suna bin ƙasa ne su yi yaɗo kaman yanda samanta ke yi, tana da ƙananan kara da gaɓoɓi sosai ganyenta ba ya ƙaiƙaiyi haka ma ba ya da kaifi kaman ganyen kunnen nema, takan yi ƙonshi ta fitar da kai ta yi ƙwaya idan ƙwayan ta ƙosa sai ta zube da kanta a nan inda ta girma, takan bushe a lokacin rani amma takan ɗauki dogon lokaci kafin ka ga bushewanta.

Muna ba da shawara ga ma'aikatan aikin gona da su yi ƙoƙarin kawo wani tsari musamman ga masu feshi domin guje wa wata rana mu rasa samun wasu daga cikin ire-iren waɗannan ciyayi masu albarka.

Daga Taskar

Mai Girma Sarkin Rafin Gobir
Mai Girma Isma'il Muhammad Yusuf

Proofread By:
Nafisa Abdullahi
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau

Post a Comment

0 Comments