Ticker

6/recent/ticker-posts

Tana Soyayya Da Tsohon Saurayinta

TAMBAYA (01):

Uncle dama Ina da tambayane shinmene hukuncin wadda take da aure Kuma take cewa tana son wani daban awaje misali aceshidin tsohon saurayintane Kuma Allah baiyi auren nasu yayuwuba hartakaima ayanxu tana da mijin amma Kuma haryanxu batadaina Kiran wance tsohon saurayinnata da masoyiba, Uncle mene hukuncinta shin auran  zai'tabuwa adalilin Hakan? Allah ya Karawa malam sani

AMSA:

Hukuncinta shine mai cin amanace. Domin kuwa anan taci amanar mijinnata saboda kula tsohon saurayinta da takeyi a can waje batareda sanin mijinba. Wannan duk yana daya daga cikin planning da shaidan yake don ya raba aure tsakanin mata da miji

Kuma hakan ya nuna ita din ba mumina bace ba, don haka bazata yi nasara a rayuwarta ba indai har bata tuba ta daina ba, meyasa akace ba mumina bace ba ?

Mu duba me Allah ya ce a cikin Suratul Mu'uminun ayata 8

( وَالَّذِينَ هُمْ لِأَمَانَاتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَاعُونَ )

المؤمنون (8) Al-Muminoon

Kuma waɗanda suke, sũ ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarwa ne

Rashin tsare alqawari da kuma rashin riqon amanar auratayya shine zaisa a kirata da mai cin amana kuma hakan yana nufin bazatayi nasara ba idan bata tuba ba, domin kuwa Allah SWT ya zayyano wasu daga cikin masu nasara a rayuwar duniya da ta lahira a cikin ayar farkon Surar

( قَدْ أَفْلَحَ الْمُؤْمِنُونَ )

المؤمنون (1) Al-Muminoon

Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ

Wanda su wadannan muminan sune masu gadon Aljannatil Firdous kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin ayata 10 zuwa ta 11

( أُولَٰئِكَ هُمُ الْوَارِثُونَ )

المؤمنون (10) Al-Muminoon

Waɗannan, sũ ne magãda

( الَّذِينَ يَرِثُونَ الْفِرْدَوْسَ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ )

المؤمنون (11) Al-Muminoon

Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne

Sannan kuma akwai hadisai sahihai da suka tabbata daga Manzon Allah SAW akan illar cin amana, daya daga hadisan shine hadisin da Bukhari ya kawoshi a cikin littafinsa Al-Adabul Mufrad littafi na 8, volume na 73, mai lambata 117 wanda aka rawaito daga Abu Hurairah RA wanda ya ce Annabi SAW ya ce alamomin munafuki guda 3 ne, na 1 idan yayi zance sai yayi qarya, na 2 idan aka amince masa sai yayi ha'inci na 3 idan yayi alqawari sai ya saba. Anyiwa Shaikh Umar Sani Fagge tambaya akan cin amana, ya ce: A ranar lahira za a kawo amana a dora akan siradi, duk wanda yaci wannan amanar to sai ta dinga zabtare naman jikinsa gwargwadon yawan amanarnan da yaci anan duniyar

To kinga anan mijin ya amince mata da manufar idan ya aureta bazata kula wasu a waje ba ballantana kuma tsohon saurayinta, anan ta zamo munafuka saboda cin amanar da tayi. Don haka Idan har tana son nasara a rayuwar nan da ta can sai ta tuba ta koma ga Allah domin samun rabo fuddunya wal akhira

Muna roqon Allah yasa ta gane tayi taubatun nasuha

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato, Usmannoor_Assalafy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

WHATSAPP👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

https:///

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments