Ticker

6/recent/ticker-posts

Ana Rama Sallah Ce Kamar Yadda Ta Kuɓuce Wa Mutum

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Malam tambayata ita ce, ya sallar matafiyi mai yin qasaru take yayin da yake kan hanya wasu salloli suka wuce shi bai yi ba, sai da ya sauka a gida, qasarun zai yi ko kuma zai cika sallarsa ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, wanda sallah ta kuɓuce masa a halin tafiya zai rama ta ne kamar yadda ta kuɓuce masa, wato idan qasaru ne zai rama ta ne kamar yadda yake yin qasaru, ba zai cika ta ba. Kamar yadda Mal. Abdurrahman ya bayyana cewa:

"Wanda ake bi sallah zai rama ta ne gwargwadon yadda ta kuɓuce masa, idan ta zamo sallar zaman gida ce ta kuɓuce masa zai rama ta ne irin sallar zaman gida, haka idan ta kasance sallar qasaru ce zai rama ta ne irin sallar qasaru, daidai ne ya kasance a lokacin ramuwar a halin tafiya ne ko a halin zaman gida".

Matnul Ahdhariy 51.

Wannan ita ce fahimtar maz'habar Malikiyya da Hanafiyya. Amma wasu kuma suna ganin idan sallar qasaru ta kuccewa mutum har sai da ya dawo gida, to zai cika sallar ce, amma magana mafi rinjaye a wurin mafi yawan malamai ita ce ta Malikiyya da Hanafiyya ɗin can, wato zai rama duk wata sallah da ta kucce masa ne a siffar da ta kucce masa ɗin.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6qgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments