𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam. Don Allah Suratul Lukman, to
Lukman ɗin
wasu sun ce Annabi ne wasu kuma sun ce bawan Allah ne Wanda Allah Swt ya bada
misalin shi a cikin bayaninshi, Don Allah miye gaskiyar lamarin nan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam. Ƴar uwa kamar yadda kika
faɗa ɗin haka ne, tabbas malamai sun yi saɓani game da Luqman Annabin Allah ne ko
wani bawan Allah ne na qwarai, to amma jumhur na malaman Tafsiri sun ce lallai
Luqman Waliyyin Allah ne da Allah ya ba shi hikima yake yi wa Banu Isra'eela
hukunci bisa wannan hikima da Allah ya ba shi, wato dai ba Annabi ba ne, kamar
yadda Imamul Qurɗubiy
ya faɗa a
littafin tafsirinsa.
Duba Aljámi'u Li'ahkamil Qur'an 7/381.
Abin da ya fi kamata a mayar da hankali shi ne
koyi da hikimar da Allah ya ba Luqman, fiye da neman sanin Annabi ne ko ba
Annabi ba ne, saboda rashin sanin haqiqanin matsayinsa ba zai cutar da mu ba.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.