Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sallar Wanda Ya Karanta Surah A Raka'o'i Biyun Qarshe

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Mene ne hukuncin sallar Wanda ya karanta surah a raka'a biyun karshe?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam. Wanda ya qara karatun surah a raka'a ta uku da ta huɗu a sallah mai raka'a huɗu, babu komai a kansa, saboda hadisin Abu Sa'id Alkhudriy da yake cewa: Lallai Annabi ya kasance yana karanta gwargwadon aya talatin a kowace raka'a daga cikin raka'o'i biyu na farkon Sallar Azuhur, a raka'o'i biyun qarshe kuwa yana karanta gwargwadon aya goma sha-biyar a kowace raka'a. A La'asar kuwa yana karanta gwargwadon aya goma sha-biyar a raka'o'i biyun farko, a raka'o'i biyun qarshe kuma yana karanta gwargwadon aya bakwai.

Duba Muslim 452.

Kenan wannan hadisin ya nuna cewa Annabi yakan karanta surah a wasu lokutan a raka'o'i biyun qarshe na Azuhur da La'asar, sai dai Annabi a wasu lokutan ne yake yin hakan, wato ba a duk sallar Azuhur da La'asar ba ne yake yi, saboda hadisin Abu Qatada da Bukhariy da Muslin suka ruwaito da ke cewa: "Lallai Annabi ya kasance yana karanta Fatiha da surah a raka'o'i biyun farko na Azuhur da La'asar, wani lokacin yakan jiyar da mu aya ɗaya, sannan kuma yana karanta Fatiha ne kawai a raka'o'i biyun qarshe".

Bukhariy 759. Muslim 451.

Kenan kuma shi wannan hadisin ya nuna cewa Annabi ba ya karanta surah a raka'o'i biyun qarshe. Saboda haka ne malamai suka tafka saɓani a kan hadisin da ya kamata a yi amfani da shi a game da wannan matsalar, sai wasu malaman suka rinjayar da hadisi na biyu, saboda kasancewarsa Bukhari da Muslim suka ruwaito, wasu kuma suka ce za a iya haɗa duka hadisan a yi amfani da su ba tare da cin karo da juna ba.

Maganar da ta fi zama daidai ita ce za a iya haɗa hadisan a yi aiki da su duka ba tare da sun saɓa wa juna ba, yadda abin yake kuwa shi ne, wani lokacin Annabi yakan yi Fatiha da surah har a raka'o'i biyu na qarshen Azuhur da La'asar kamar yadda hadisin Muslim ya bayyana, wani lokacin kuma ba ya yi kamar yadda hadisi na biyu da Bukhariy da Muslim ɗin suka ruwaito ya bayyana, amma rashin yi ɗin ne a gaba a bisa fahimtar jumhur na Malamai.

Amma a fahimtar malaman da ba sa aiki da wancan hadisi na Muslim da ya ce Annabi yana karatun surah a raka'o'i biyun qarshe, su suna  da fahimtar cewa duk wanda ya yi karatun surah a raka'o'i biyun qarshe zai yi sujjada ba'adiyya, saboda a fahimtarsu ya yi qari ne a cikin sallah.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CQ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

Question and Answers in Islam𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 


Post a Comment

0 Comments