Raba-Gardama: Wakokin Zamani Rubutattu Ne Ko Na Baka?

    1.0 GABATARWA

    Masana, musamman na ɓangaren ilimin addinin Musulunci, sun bai wa sanin abu (ilimi) wasu darajoji hawa-hawa har zuwa hawa uku: daraja ta farko ita ce 'haƙƙul-yaƙini' (ilimin da ke tare da mutum yake jin sa a cikin jikinsa, kamar wata cuta da ke cin sa a cikin jikinsa), daraja ta biyu kuma 'aynul-yaƙini' (ilimin da ka gan shi muraratan, misali idan aka ce maka cuta kaza tana illa kaza kuma sai ka ga illar a jikin na tare da kai), daraja ta uku kuwa ita ce 'ilimul-yaƙini' (shi ne ilimin da za a faɗa maka ko a ba ka labari ko a karantar da kai cewa cuta kaza tana illa kaza ba tare da ka ji illar a jikinka ko ka gan ta ba). Masanan sun kawo misalin bambancin waɗannan darajoji guda uku na sanin abu ta amfani da ƙonannen nama da gasasshe da kuma dafaffe; ƙonannen nama shi ya fi kowane nama sanin wuta domin ya ji ta a cikin jikinsa, daga nan sai gasasshe wanda suka yi ido huɗu da wutar —gasasshen naman da aka gasa daga kan wayar gashi, na ukunsu shi ne dafaffe, wanda kayan miya da ruwan zafi ne suka ba shi labarin zafin wutar.

    A wannan taƙaddama ta shin waƙar zamani tana wane aji ne a waƙoƙin Hausa? Ina kyautata zaton ina da haƙƙul-yaƙini, dalili kuwa ina jaraba yin waƙoƙin zamani, hasali ma ta zame min tamkar sana'a. Wannan dalilin ne ya ƙarfafa min guiwa har nake tunanin zan iya yin kankanbar shiga wannan taƙaddama da masana da manazarta waƙoƙin Hausa suka shafe dogon zango suna yi, da fatar wannan rarraunan hasashen nawa da zan fito da shi ya dace da sadudar duka ɓangarorin biyu: —masu ganin cewa rubutatta ce da masu ganin cewa ta baka ce.

    1.1 WAƘA

    Mafi yawan masana bakinsu ya zo ɗaya wajen bayyana ma'anar waƙa a matsayin wani tsararren zance wanda ake rera shi cikin wata murya ta musamman da nufin sanya wa mai sauraro nishaɗi. Sai dai akan yi waƙa da manufofi mabambanta, ko dai don nishaɗantarwa ko faɗakarwa ko ilimantarwa ko wayar da kai ko soyayya ko siyasa ko dai da nufin isar da wasu saƙonni waɗanda ba waɗanda na ambato ba ga jama'a.

    Waƙar Hausa iri biyu ce: akwai Waƙar Baka da kuma Rubutacciyar Waƙa. Suna da bayyanannen bambanci a tsakaninsu; Waƙar Baka da ka ake yin ta nan take, kodayake wasu mawaƙan sukan tsara waƙar a gida ko a keɓe tare da yaran aikinsu kafin su fito cikin al'umma su rera ta. Gusau (1996). Kuma suna yin waƙar ne ba tare da la'akari da wasu shimfiɗaɗɗun ƙa'idoji irin na Rubutacciyar Waƙa ba, waɗanda suka samo asali daga waƙoƙin Larabawa. Yayin da Rubutacciyar Waƙa kuwa ana rubuta ta ne bisa wasu shimfiɗaɗɗun ƙa'idoji da zubi da tsari irin na Balarabiyar waƙa sannan a rera ta.

    1.2 SAMUWAR WAƘOƘIN ZAMANI

    Waƙoƙin zamani waƙoƙi ne da suka faro daga tsakiyar ƙarni na ashirin zuwa ƙarni na ashirin da ɗaya har zuwa wannan lokaci da nake gudanar da wannan nazari. An kira su da waƙoƙin zamani ne saboda sun saɓa da al'adar tsara waƙa a Hausa, kodayake tarihin samuwarsu ya nuna cewa sun faro ne daga waƙoƙin bege ko waƙoƙin yabon Annabi Muhammad (S. A. W) waɗanda aka fi sani da waƙoƙin Mandiri. Fitattun marubuta irin su Ɗan'azumi Baba da Alkhamis Bature da Sani Yusuf Ayagi da sauransu, su suka buɗe wannan fage na waƙoƙin zamani, inda suka fara buɗe fagen da shirya waƙoƙin finafinai amma bisa tsarin Rubutacciyar Waƙar Hausa. Mandawari (2004) da Hauwa (2014).

    Ke nan za a iya cewa haɗa kiɗa da waƙa ya faro ne a wannan lokacin a ƙoƙarin masu shirya finafinai na samar da waƙa a cikin fim da nufin ƙayatar da finafinan Hausa da bunƙasa su da kuma yunƙurin dakushe finafinan Indiya waɗanda suka cika ƙasuwannin ƙasar Hausa, musamman a tsakiyar ƙarni na ashirin. An fara tsara waƙoƙin fim da ɗora musu kiɗa a tsakanin shekarar 1997 da 1998, misalin fitacciyar waƙar nan ta fim ɗin Daskin Da Riɗi da fim ɗin Badaƙala.

    2.0 TAƘADDAMA

    Masana da manazarta sun sha yin muhawara a tsakaninsu da nufin yi wa waƙoƙin zamani gurbi a waƙoƙin Hausa. Ga wasu daga cikin zantuttukan ba'arinsu kamar haka:

    Gusau, (2008) yana ganin cewa waƙoƙin zamani gabaɗayansu na baka ne ba rubutattu ba, har yake kawo hujjoji kamar haka: “Suna aron karin murya daga rauji na waƙoƙin makaɗan baka na Hausa su ɗora a waƙa. Suna kwaikwayon zubi da karin murya na waƙoƙin baka na Hausa. Suna amfani da sababbin kayan kiɗa waɗanda aka same su ta hanyar hulɗa da Larabawa ko Turawa, kamar abin kiɗa na bandiri da kuma alar kiɗa na fiyano ko jita da makamantansu. Suna surka kayan kiɗan Hausa na gargajiya da kayan kiɗan zamani.”

    Ita kuwa Zainab, (2013) cewa ta yi, “Waƙoƙin zamani na fiyano na Hausa asalinsu rubutattu ne, haɗuwarsu da kayan kiɗa na zamani bai isa ya canza musu mafari ba, kowa dai ya san zamani riga ne. Haka kuma ta fuskar jigo da salo da tsari da salon sarrafa harshe waƙoƙin fiyano suna ɗauke da irin na rubutattu ne.”

    Shi kuwa Abdullahi (2018), cewa ya yi “A wannan zamani an samu sauye-sauye a duniyar Bahaushiyar waƙa, wasu mawaƙan sukan cakuɗa nau'o'in waƙoƙin biyu a wuri ɗaya ta hanyar amfani da kayan kiɗa na zamani kamar su fiyano da jita wajen aiwatar da waƙoƙinsu, kuma su rubuta su ta yadda marubuci ke yi.”

    Usman (2018), shi ma ya kalli waƙoƙin zamani a matsayin masu ruwa biyu a waɗanda suke da sigogin waƙar baka da sigogin rubutacciyar waƙa.

    3.0 ƘWARYAR HASASHENA

    Duk wani fasihi, kafin fasaharsa ta bayyanar masa har ya san yana da ita, sai da ya raini ƙwaƙwalwarsa da irin wannan fasahar ta hanyar bibiyar fasahar fasihan da suka gabace shi a wannan harkar. Misali, duk mawaƙi bai zama mawaƙi ba sai da ya kasance mai sha'awa da bibiyar waƙoƙin mawaƙan da suka gabata. Haka marubucin ƙagaggen labari bai zama marubuci ba sai da ya zama mai sha'awa da bibiyar ƙagaggun labaran da marubuta suka ƙaga.

    Sannan kuma al'adar fasaha ita ce; duk irin fasahar da fasihi ya raini ƙwaƙwalwarsa da ita a kan salonta yake gina tasa fasahar daga farkon lamari, sai dai idan tafiya ta yi tafiya gogewa da bunƙasa su sa ya ƙirƙiro wasu salailan nasa na kansa.

    Idan har inda saniyar gaba ta sha ruwa nan ta baya ke sha, za mu iya cewa mawaƙan zamani na Hausa iri biyu ne su ma: akwai marubuta sannan akwai mawaƙan baka a cikinsu. Dalili kuwa; wasunsu sun raini ƙwaƙwalwarsu ne da waƙoƙin marubuta waƙoƙin Hausa irin su Sa'adu Zungur da Abubakar Ladan da Aƙilu Aliyu da Aliyu Namangi da sauransu. Ko kuma mawaƙan mandiri waɗanda ke bin salon rubutacciyar waƙa irin su Rabi'u Usman Baba da Bashir Ɗanmusa da Bashir Tashi da Rufa'i Ayagi da Auwalu Gawuna da dai sauransu. Wasu mawaƙan na zamani kuwa sun raini ƙwaƙwalwarsu ne da waƙoƙin maƙaɗan baka irin su Dr. Mamman Shata da Musa Ɗanƙwairo da Ibrahim Narambaɗa da Haruna Uji da Sani Aliyu Ɗandawo da sauransu. Sai dai su mawaƙan zamani tasirin zamani da son karɓuwar waƙoƙin nasu a cikin jama'a ya sa kowanne ɓangare ke yin kiɗa da kayan kiɗa na zamani irin su fiyano da jita.

    Idan har bayanan da na yi suna bisa tsari, to kuwa sanya wa rubutacciyar waƙa kiɗa bai wadatar ba wajen sauya ta ta zama waƙar baka, kamar yadda Aminu Ala ya sake rera tare da sanya wa shahararriyar rubutacciyar waƙar nan ta Afirika kiɗa, mai taken 'Allah ya Allah, haɗa kanmu Afirika mu so juna' ta Abubakar Ladan, kuma ban ji wani masani ko manazarci ya ce a yanzu waƙar ta zama ta baka ba. Kiɗa kawai aka sanya wa waƙar ta asali, sai salonta ya saje da salon sauran waƙoƙin Aminu Ala, wanda hakan ke bayyana cewa fasihi Aminu Ala ya raini ƙwaƙwalwarsa ne da rubutattun waƙoƙi, shi ya sa waƙoƙinsa suke da ƙa'idoji irin na rubutacciyar waƙa, sai dai tasirin zamani ya sa yake sanya musu kiɗa kamar yadda ya sanya wa ta Abubakar Ladan.

    Kuma ba za a ce a cikin waƙoƙin zamani babu waƙar baka ba, domin wasu mawaƙan sun raini ƙwaƙwalwarsu ne da waƙoƙin maƙaɗan baka; daga cikinsu akwai Audu Boda Katsina da Sanusi Ano da Ali Burunkuza da Nuhu Ɗan Hausa da sauransu. Suna yin waƙoƙinsu ne ba tare da la'akari da daidaita tsawon layi (ɗango) ba ko daidaita yawansa a cikin baiti. Sannan ba ruwansu da amsa-amo (ƙafiya) na ciki ko na waje, saɓanin 'yan uwansu mawaƙan zamani irin su Aminu Ala da Dauda Kahutu Rarara da Elmu'azu Birniwa da sauran masu rubuta waƙa kafin su rera.

    Kamar yadda na faɗa a baya cewa, su ma mawaƙan zamani iri biyu ne idan aka bi salsalar inda suka gado fasahar waƙa da kuma ƙa'idojin da suke shimfiɗawa a cikin waƙoƙin nasu. Ke nan idan ana so a gane waƙar zamani ta baka ce ko rubutacciya sai dai a saurare ta a ji wane ƙa'idoji ta zo da su, ba wai a yi hukunci da wanzuwar kiɗa kaɗai ko aron rauji da kari ko wasu ƙananan abubuwa da tasirin zamani ya sa aka saka su a cikin waƙar ba. Ba yadda za a yi biri ya haihu a sanya wa ɗan tufafi irin na mutane kuma a ce mutum ne, ko kuma mutum ya haifi ɗa mai yawan gashi a jiki a ce wannan ɗan biri ne, sai dai kamanceceniya. Haka abin yake a wannan zamanin, akwai mawaƙin da bai san waƙoƙin baka ba sai rubutattu da na mandiri, haka zaliki waƙoƙinsa yana yi ne bisa ƙa'idojin waƙar da ya sani, sannan kuma a zo a ce masa wata waƙa ce daban don kawai ya sanya mata kiɗa?

    Ban ƙi ba, idan mawaƙin zamani ya tumbatsa, yakan yi amfani da salailan duka biyu: —wani lokacin ya yi waƙa cikin ƙa'idojin rubutacciyar waƙa, wani lokacin kuma ya yi ta bisa tsarin makaɗan baka, kamar dai yadda Naziru Sarkin Waƙa yake yi.

    4.0 KAMMALAWA

    Babban adalcin da za a yi wa ma'abota wata sana'a ko wani fanni na zamantakewa shi ne tuntuɓar su game da wannan fanni don jin ra'ayinsu a kai, sannan a ɗaukaka wannan ra'ayin nasu bisa kowanne, don su suke da 'haƙƙul-yaƙini' a cikin fannin. Idan mai karatu zai nazarci wannan bincike da kyau, na yi sa ne domin warware taƙadamar da ke tsakanin masana da manazarta game da gurbin da ya kamata a yi wa waƙoƙin zamani na Hausa iri biyu da muke da su. Wannan dalilin ne ya sa na yi ƙoƙarin fito da kowane bayani yadda yake da taimakon bibiyar ra'ayoyin waɗannan masana da manazarta game da ajin da ya kamata a ajiye waƙoƙin zamani. Allah shi ne mafi sani.

    5.0 MANAZARTA

    A tuntuɓi manazarcin a lambar waya kamar haka: 07063828558

    Ko a turo da saƙo ta wannan email: mdasnanic1@gmail.com

    (c) Haƙƙin Mallaka
    MD Asnanic
    03/09/2023

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.