A wannan zamani da muke ciki, an riga an maida aure kamar wata al'ada ba ibada ba, aure ya zama gasa yadda wasu ke yinsa kawai saboda abokai ko kawaye sun yi, dan haka su ma suke ga ya kamata su yi.
Mutane ba sa daukar aure da daraja da mutumci a wannan zamanin, yadda za kaga ana bidi'o'i marasa kyau da ka iya sa Allah ya kwashe albarkar dake cikin auren ya bar ma auratan da halinsu.
Da yawa mutane suna mamakin yadda za su ga an yi soyayya tsakanin mace da namiji kai ka ce idan akai auren ko tari daya in ya yi dayan ma sai ya yi, saboda shakuwa da suka yi kafin a yi auren.
Tabbas akwai so da kauna mai karfi a tsakaninsu. To sai dai a ina gizo yake sakar ne da za ka ga da an yi aure a wannan zamanin da ya lalace?
Na taba jin wata lakca da Dr. Muhd Sani Umar R/Lemo ya yi akan abinda ke ruguza auren wannan zamanin.
Yawancin abinda ya fada ba shi muke gani ya ke kawo sanadiyar rabuwar auren ba. Wannan bidi'o'in na zuwa "Party" ko "Dinner" da irin ta'asar da ake yi idan an je, shi ne ummul-aba'isun da yake janyo aure ya lalace.
Ya ce hudubar auren da aka yi shi da al'adun banza da wanda aka yi shi bisa koyarwar Islama, duk daya ce.
Kawai ana samun matsala ne bayan da aka shirya fitsara da kuma aikata abubuwa da sunan wayewa, da ka iya janyowa Allah ya zare albarka a cikin auren.
Saboda haka, da an yi aure an watse an tare sai kai ta ganin fitintinu na ta fitowa ko ta wanne bangaren har sai auren nan ya ruguje.
Duk wannan bayanin nawa, na yi shi ne game da AUREN babbar yar Ado Ahmad Gidan Dabino wato Fati. Jiya aka daura auren a Masallacin Alfurqan karkashin jagorancin Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar.
Abunda zai burge ka malam shi ne, babu wata bidi'a irin wacce muka saba gani a sauran bukukuwa da aka yi a wannan aure. Kai hatta kida da mata kanyi a cikin gida su dan rausaya, ba'ayi a wannan aure ba.
Da yake ita wannan amaryar yar albarka ta gama haddace Al-Qura'ni gaba dayansa a kanta (ba wai sauka ba, domin sauka daban hadda daban)
Sai ta tara kawayenta da sauran y'an mata y'ay'an gidan mutumci, inda suka zauna suka yi saukar Al-Qur'ani Mai Tsarki a tsakaninsu.
Babu shigar banza babu raye-raye da kade-kade na auren wannan zamani.
Wannan abu ya burge mutane da dama musamman duba da cewa mahaifin Amaryar fitaccen Jarimi ne a cikin shirin Kwana Casa'in, na Arewa24, wato Malam Adamu da ke fitowa a matsayin Gwamnan Garin Alfawa.
Ina adduar Allah yasa sauran y'an mata da samari da ba su yi aure ba, za su yi koyi da wannan aure, Allah Ya sanya albarkarsa, Ya sa mutuwa ce kadai za ta raba shi cikin ikon Allah.
Ameen ameen.
Marubuci: Hassan Auwalu Muhammad
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.