Manufofin Da Suka Sa Aka Haramta Zina.

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam Ina son karin bayani game da manufofin sharia akan haramta zina.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikum assalam, Addinin musulunci ya zo don ya kare tsatson Ɗan Adam da mutuncinsa, don haka ya shar'anta aure kuma ya haramta zina, ga wasu daga cikin hikimomin da haramta zina ya kunsa:

    1. Katange mutane daga keta alfarmar shari'a.

    2. Samar da Ɗan-Adam ta hanya mai kyau, ta yadda za'a samu wanda zai kula da shi, saboda duk wanda aka same shi ta hanyar zina, to ba za'a samu wanda zai kula da shi ba yadda ya kamata.

    3. Saboda kada nasabar mutane ta cakuɗa da juna.

    4. Katange mace daga cutarwa, ita da danginta, saboda zina tana keta alfarmar mace, ta zamar da ita ba ta da daraja.

    5. Kare mutane daga cututtuka, kamar yadda hakan yake a bayyane.

    6. Toshe hanyar faruwar manyan laifuka, miji zai iya kashe matarsa, idan ya ga tana zina, kamar yadda mace za ta iya kashe kwartuwar mijinta, daga nan sai a samu daukar fansa, sai fitintinu, su yawaita.

    7. Zina tana kawo gaba da kiyayya a tsakanin mutane.

    8. Kare mutuncin yaron da za'a Haifa, domin duk yaron da aka Haifa ta wannan hanyar zai rayu cikin kunci.

    WANNAN YA SA BABU WANI ZUNUBI BAYAN SHIRKA DA YA FI ZINA.

    Allah ne mafi sani

    Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.