Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Tsotsar Al'aura Da Baki (Oral Sex)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Allah ya ƙarawa malam lafiya ameen. Malam, Allah yana cewa a cikin Alƙu'ani mai girma:

نِسَاۤؤُكُمۡ حَرۡثࣱ لَّكُمۡ فَأۡتُوا۟ حَرۡثَكُمۡ أَنَّىٰ شِئۡتُمۡۖ

(Mãtanku gõnaki ne a gare ku,bsabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so)

Tunda hakane, toh malam meye hukuncin Oral sex? Saduwar da ake yi ta baki? Malam wannan ya halatta tsakanin ma'aurata?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Eh haka ne. Allah ya fada haka. Amma ba wai ayar tana nufi cewar kuyi jima'I dasu ta kowacce Ƙofa bane.

A'a ayar tana nufin "KUYI JIMA'I DASU AKWANCE, KO AZAUNE, KO ATSAYE, KO DURKUSHE, KO TA-GABA, KO TA-BAYA".

Wannan shi ake nufin "أَنَّىٰ شِئۡتُمۡۖɗin.

Dangane da KOFAR SADUWAR kuwa, idan ka koma ayar da take kafin wannan wacce ka kawo, ai zakaga wajen da Allah yake cewa:

...فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ ۚ ...

Wato: "Kuzo musu (ku sadu dasu) ta wajen da Allah ya umurceku".

To idan kayi nazari, ai zaka ga cewar FARJINSU shi ne wajen da Allah yayi umurni ɗin. Ba wai dubura ba, ba kuma baki ba.

Da akace MATAYENKU GONAKINKU NE, ai farjinsu shi ne gonar. Maniyyin mazajensu kuma shi ne abin shukawar (seeds) kenan.

Don haka idan kazo da seeds ɗinka, awanne waje ya kamata ka shuka?

ABAKI??- a'a shi baki anyishi ne domin zikiri da karatun Alƙur'ani da salatin Annabi  dakuma cin abinci, da furuci.

Don haka bai kamata wajen ambaton Allah kuma ya koma ya zama wajen yin Jima'I ba.

Acikin littafin FATAWAL HINDIYYAH juzu'I na 5 shafi na 372, marubucin yana cewa: Malamai sun kasu gida 2 akan mas'alar ta kowacce fuska.

Idan sumbartar al'aurar juna kawai kake nufi, ba tare da fitar Maziyyi ko Maniyyi ba, to wasu Malaman sunce ya halatta. Amma mafiya yawan Malamai sunce MAKRUHI NE.

(Aduba Tafsirin Ƙurtubee juzu'I na 12 shafi na 231 da kuma AL-INSAF juzu'I na 8 shafi na 33)

Amma idan kana nufin tsotsa sosai harda fitar maniyyi da maziyyi, to wannan Mafiya yawan Malamai sun tafi akan rashin halaccin yinsa. Saboda wadancan dalilai wadanda na lissafa.

An tambayi Shaykh Nasiruddeen albany akan wannan Mas'alar. Sai ya ce: "Haramun ne domin Wannan wani aiki ne wanda koda acikin dabbobi ma, in banda KARNUKA babu masu yi. Kuma sanin kowa ne cewar koda acikin sallah an hana muyi irin durkusowar rakumi, ko kuma irin Koton kurciya dinnan alokacin Sujadah, kuma Manzon Allah  ya umurcemu mu guji yin koyi da Kafirai da mushrikai acikin al'amuran addininmu da rayuwarmu. To kaga kenan bai halatta muyi koyi dasu ayanayin saduwarmu da iyalanmu ba.

Aduba FATAWAL MUHIMMAH shafi na 709.

Kuma likitoci sun tabbatar da cewar ana kamuwa da cutar MOUTH CANCER ta wannan dalilin.

Da fatan mai tambayar ya gamsu.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

Hukuncin Tsotsar Al'aura Da Baki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Menene Hukuncin Ma'aurata Suji Daɗi Da Bakinsu Da Al'aurar Junansu (Tsotsar Al'aurar Juna)?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Miji shari'a ta bashi dama yaji daɗi da matarsa yanda yaso, yaje mata ta inda take haihuwa ta kowanne guri yaso, Kamar yanda Allah Ya faɗa acikin aya ta 223 cikin suratul Baqara

...فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ...

...sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku...

Abu biyu aka haramtawa miji wajan zakkewa matarsa.

1. Saduwa lokacin haila, Kamar yanda Allah yafada acikin ayata 222 cikin suratul Baqara

وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ

Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa.

2. Saduwa ta dubura, Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam Yace: (Tsinanne ne duk wanda yajewa matarsa ta dubura,) Abu dauda da Ahmad suka ruwaito shi, Albani ya Ingantashi acikin Saheehu jami'i (5889).

Duka Ababe biyun Wani hadisin Ya haɗesu baki ɗaya, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Yace: (Ku guji saduwa ta dubura da lokacin Haila). Ahmad Abu dauda suka ruwaito shi, Yana cikin jami'ussaheeh (1141).

Tsotsar Al'aura da baki, Akwai sharudda guda biyu

1. Yakasance hakan baya cutarwa, ko jawo cuta.

2. Kada yazama sababi na wucewar najasa zuwa maqogwaro.

Shaik Abdurrahaman Yace: Ya kamata Nisantarsa dan Kunya da gujewa Abunda ke tattare dashi na qazanta da Saɓawa fidra da yayi, da lura da cewa zai hana mace biyan buqatarta idan miji ya saba mata dashi.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments