Ticker

6/recent/ticker-posts

Jigo A Finafinan Hausa

Daga:

Isa Yusuf Chamo
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Bayero, Kano

1.1 Gabatarwa

 Fim abu ne mai gajaren tarihi idan aka kwatanta shi da sauran ɓangarori na adabin zamani. Misali waƙa da rubutun zube. A wajen Hausawa wasan kwaikwayo shi ne tushen samuwar finafinan bidiyo na Hausa, domin shi aka fara aiwatarwa a dandali kafin a sami na’urar ɗaukar hoto ta majigi wadda daga baya kuma aka sami gidajen talabijin da na’urar bidiyo da ake amfani da ita a yau. Dangane da fim wanda aka fara aiwatarwa a harshen Hausa kuwa shi ne “Baban Larai”. Abdulƙadir (1988: 24).

 Finfinan Hausa na bidiyo kuwa, an fara samun su ne daga shekarar 1980 zuwa 1984. Sakamakon irin hoɓɓasar da ƙungiyoyin marubuta litatttafai da na wasan kwaikwayo na dandamali da na wasan motsa jiki (kareti), suka fara jarraba shiryawa. A shekarar 1990 ƙungiyar Tumbin Giwa ta shirya wani fim mai suna Turmin Danya. To sai kuma a shekarar 1994 suka sake shirya fim ɗin “Gimbiya Fatima”. Kamfanin Gidan Dabino ya shirya In da so da Ƙauna a 1994. Samuwar waɗannan finafinai da wasunsu shi ne ginshiƙin da ya ba wa kamfanoni da ƙungiyoyin ƙasar nan damar yin finafinan Hausa.

A wannan takarda an yi nazari ne, sannan aka fito da nau’o’in saƙonni waɗanda ake ƙulluawa a cikin zubin finafinan Hausa. Domin haka, manufar wannsan takarda ita ce fito da wasu jigogi na finafinan Hausa da kuma bayaninsu tare da kafa hujjoji da misalai daga finafinan Hausa.

1.2 Ma’anar kalmar Jigo

 Kalmar jigo tana da ma’anoni guda biyu wato ma’ana ta lugga da kuma wadda aka ba wani fannin ilimi da ake kira da Larabci ‘isdillahi’.

 Jigo a luggance na nufin abin da ake amfani da shi wajen ban ruwa a lambu. Ganin muhimmancin da jigo yake da shi wajen ban ruwa wadda idan babu shi babu ban ruwa, ya sa manazarta suka yi amfani da kalmar a matsayin manufa ko kuma saƙo. (East da Wasu, 1948:47)

 Malamai da manazarta da kuma ɗalibai sun bayyana ma’anar jigo ta lugga ko isdilahi a rubuce-rubucen da suka yi. Alal misali:

 Ɗangambo, (1981:6) cewa ya yi “Jigo shi ne saƙo ko manufa ko abin da waƙa ta ƙunsa, wato abin da take magana a kai”.

 Gusau (1983:142) Ya bayyana Jigo da cewa “shi ne saƙo wato ainahin gundarin saƙon da waƙa take ɗauke da shi”.

 Shi ma Muktar (1984:1) Ya ce “Jigo wani abu ne da aka yi ko kuma ake so a sadar da wannan ƙuduri ga wani ko wasu, domin wanda aka sadarwa da wannan ƙuduri ya yi aiki da shi, ko kuma ya zamana yana sane da wannan abu shi ma”.

 Buhari (1988:26) Ya bayyana jigo da “Duk wani saƙo ko manufa da marubuci ke so ya isar ko ya gabatar, shi ne jigonsa. Lallai ne wanda duk ya yi irin wannan rubutu ya zamana yana da manufa. Manufar nan ita ce ginshiƙin rubutun shi jigo”.

 Sai kuma Halima, Ɗ. (2002:25) ta bayyana jigo da cewa “Madogari da madosar da ake son nusarwa ga jama’a wadda hakan yana iya zama gyara da kuma maganganu a cikin al’umma baki ɗaya don amfanin gaba”.

 Idan aka duba za a fahimci cewa waɗannan ma’anoni da malamai da manazarta suka bayar kusan abu ɗaya suke magana a kai, sai dai bambancin kalmomi da zurfin zaɓensu na kowane malami ko manazarci ne suke daɗa fito da ma’anar ko daɗa armasa ta.

Jigo a fim na Hausa, kai tsaye yana nufin saƙon da aka sarƙa a zubin labari na fim. Abu ne wanda aka yi wa mutane ishara da a kansa ake son su koyi wani darasi daga abin da aka nuna abin nishaɗi a kansa. Haka kuma jigo ra’ayi ne wadda manazarci zai iya bayyanawa da kare kansa ta hanyar fito da wadatattun hujjoji daga fim ɗin da yake nazari a kai.

Muhimman hanyoyin fitar da jigo daga finafinan Hausa sun haɗa da:

-                     kallon fim

-                     waƙa

-                     sunan fim

i) Kallon Fim

 Kallon fim yana nufin mai nazari ya kalli fim tun daga farkonsa har ya zuwa ƙarshensa. Ta haka ne za a iya gano saƙon da fim ɗin yake ɗauke da shi. Wannan hanya tana ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin da mutum zai iya yanke hukunci a kan wani fim dangane da jigonsa ta hanyar kawo hujjoji daga fim ɗin da ya kallata.

ii) Waƙa

 Waƙa wani zance ne tsararre kuma shiryayye da ake yi da ya bambanta daga magana ko zance na hira da ake yi domin yabon wani ko wata ko kuma isar da wani saƙo. Waƙa ma hanya ce da ake iya fayyace jigo a finafinan Hausa daga zubinta, musamman wasu daga cikin finafinan, manufarsu ba ta fita sai ta hanyar waƙar da take cikinsu. Misali a cikin fim ɗin Sutura da wuya mutum ya iya gane takamaiman jigonsa bayan ya gama kallon fim ɗin, domin ɓangarori na rayuwa da kowannensu za a iya shirya fim a kai, aka gwama su. Amma sai a waƙar ƙarshe ne jigon ya bayyana kansa inda matan da suka fito a cikin shirin suka bayyana matsayinsu wato na 'yar masu kuɗi da mai kyau da kuma mace mai ilimi wadda a cikin shirin aka nuna aurenta ya fi na sauran.

Haka kuma, su ma kansu masu shirya fim sukan sa a rubuta musu waƙa wadda a cikinta za ta bayyana jigon fim kawai. (Sani Sidi Sharifai)

iii) Sunan Fim

 Sunan fim na nufin laƙabin da aka yi wa wani shiri wanda kuma ake kiransa da shi. Wasu finafinan kan bayyana jigoginsu daga sunayensu ma’ana da mutum ya ga sunan zai iya yanke hukunci a kan jigonsa tun akfin ya kallace shi, misali finafinai irin su Nagari da Salihi da Haƙuri da Zato da Lokaci da Sauyi da Mahandama da sauransu. Sai dai akwai finafinai masu yawa da mutum ba zai iya yanke hukunci a kan jigonsu ta hanyar sunayensu ba, misali Khusufi da Khushu’i  da Limaza da Namshaza da Zabari da Gidauniya da Girma da sauransu.

1.3 Nau’o’in Jigo a Finafinan Hausa

 A wannan ɓangare an duba yadda jigo yake fitowa a cikin finafinan Hausa. Akwai abubuwa da yawa waɗanda ake gina jigon fim a kansu waɗanda suka shafi rayuwar al’umma daban-daban tun daga zamantakewarsu da ma’amalolinsu da dai sauran hulɗoɗin rayuwa. An lura a finafinan Hausa a kan gina jigon fim a kan ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa.

 A wannan ɓangare kuma an zo da rabe-raben jigo a cikin finafinan Hausa tare da kawo misalai daga finafinan da suka dace da kowanne rabo kamar haka:

1.3.1   Jigon Haƙuri

Haƙuri na nufin juriya da kawaici da ƙin nuna damuwa a kan wasu abubuwan rashin jin daɗi da kuma da-na-sani. Haƙuri halin manzon allah ne, kuma ya umarci al’ummarsa da su yi shi. Sakamakon ƙarancinsa a zukatan al’umma ya sa masu shirya finafinan Hausa suke shirya fim a kansa, domin tunatar da mutane sakamakon wadda yake aikata shi da kuma illolin rashinsa, don mutane su gyara halayensu.

Misali fim ɗin Haƙuri, an shirya shi ne a kan jigon Haƙuri domin tun daga farkon fim ɗin har ƙarshensa jigon ya ratsa ko’ina.

Babban jigon wannan fim shi ne Haƙuri sai dai akwai ƙananan jigogi da aka yi amfani da su wajen gina babban jigon, waɗanda suka haɗa soyayya kamar yadda ta faru tsakanin Aminu da Asma’u da zumunci kamar yadda Lami take yawan ziyarar Asma’u da kuma cin amana kamar yadda Lami ta juya wa Asma’u baya, lokacin da ta sami haihuwa. Sauran misalan finafinan da suke ɗauke da jigon haƙuri sun haɗa da Madadi da Haƙuri Magani da Ƙaddara da Nagari da Duniya da kuma Umarni da sauransu. 

1.3.2 Jigon Siyasa

 Bisa lugga kalmar siyasa wadda take Balarabiya ce, tana nufin sauƙi ko rangwame ko kuma jin ƙai. A da idan an ce wa mutum “Ɗan siyasa” to ana nufin mutum mai jinƙai mai rangwame mai nasiha wato mutum mai yayyafi ga rayuwar al’umma. Funtua, 2002:4)

 Ƙamus ɗin Turanci na Oɗford, ya fassara siyasa da cewa “hanya ce da mutane suke mulkar kansu ta dimokraɗiyya.

 Mashi (1986:16) ya kalli siyasa bisa isdillahi fuskoki guda uku. Fuska ta farko ya fassara siyasa da cewa kalma ce ta Girkawa (politics) wadda ke nufin salo. Fuska ta biyu da ta uku su ne waɗanda Hausawa suka ba kalmar “siyasa” wadda ke nufin sulhu ko sauƙi, domin ganin cewa siyasa ta kasance hanya ta lallashi da lallaɓawa da neman goyon baya, ko kuma siyasa ta zama yaudara da ƙarya saboda yadda 'yan siyasa kan tsara wani labari na yaudara domin neman biyan buƙata.

 Shi kuma Gusau (1995:13) ya bayyana siyasa da cewa “hanya ce wadda ake amfani da hankali da lafazi mai daɗi a jawo ra’ayin mutane zuwa ga kyautata rayuwarsu. Ta haka ne siyasa ta ƙunshi tsarin tafiyar da mutane, da matsalolinsu da ra’ayoyinsu har ta zama hanyar mulki bisa tafarkin dimokraɗiyya”.

 Kuma ta ita ne ake zaɓen shugabannin bayan kowanne shekaru huɗu. Sannan duk finafinan da aka shirya masu jigon siyasa suna koyarwa ne ko hannunka-mai-sanda ga 'yan siyasa da su gyara halayensu na babakere da almundahana da dukiyar al’umma, su rungumi adalci da kwatanta gaskiya.

 Misali fim ɗin Mahandama wadda kamfanin Mandawari enterprises ya shirya, yana da jigon siyasa kamar yadda aka nuna a fim ɗin, mun ga yadda Gwamna da sakataren gwamnati da kwamishinoni da matayensu suke wacaka da dukiyar al’umma, ban da wani kwamishina guda ɗaya na ayyuka wato Ibrahim Mandawari. Da kuma yadda Ibrahim Mandawari ya tsaya takarar gwamna da zaɓe ya zagayo ya kuma ci saboda kyawawan halayensa na kamanta gaskiya.

 Babban jigon wannan fim shi ne siyasa sai dai akwai ƙananan jigogi da aka gano a cikin fim ɗin waɗanda suka haɗa da soyayya kamar yadda ta faru tsakanin 'yar tsohon gwamna da ɗan sabon gwamna, da muhimmancin riƙe gaskiya kamar yadda kwamishinan ayyuka ya yi da kuma facaka da dukiyar al’umma kamar yadda 'yan siyasa da matansu suka yi.

 Sauran misalan finafinan da ke ɗauke da irin wannan jigo na siyasa sun haɗa da siyasa da Dare Ɗaya da kuma Gaskiya Dokin Ƙarfe.

1.3.3 Jigon Soyayya

 Masana da ɗalibai sun yi ta ƙoƙarin bayyana ko bayanin ma’anar so. Sa’id B. (1982:1-6) cewa ya yi “wani ɗarsashi ne zaunanne a cikin zukatan halittu wanda yakan bayyana a sakamakon bege ko ƙauna ko sha’awa. So yakan sa abu ya kwanta a zuciya a ji ana matuƙar muradinsa.

 Gusau (1995:15) ya bayyana soyayya da cewa “So da ke aukuwa tsakanin masoya guda biyu inda za su dinga ƙaunar juna, suna masu begen saduwa da juna”.

 Buhari (1988:47) ya bayyana soyayya da “wani hali ne na ƙauna da mutane biyu kan shiga tsakanin junansu, musamman mace da namiji. Wato ya zamana wani mutum ko yaro na son wata mace ko wata yarinya. A kuma yi dace wanda yake so ɗin ana sonsa. Wato kana so, ana sonka shi ne soyayya”.

 Sa’id (1982:8) ya karkasa soyayya zuwa kaso shida kamar haka:

i)                  Son da ke tsakanin mutum da Ubangijinsa Mahalicci.

ii)               Son da ake yi wa annabawa musamman annabi Muhammadu mai tsira da aminci.

iii)             Ƙaunar da ke tsakanin uwa ko uba da 'ya’yansu ko kuma akasi.

iɓ) Son da mace ke yi wa namiji ko wanda namiji ke yi wa mace.

ɓ) Ƙaunar da ke tsakanin abokai maza ko ƙawaye mata.

vi)              So irin na ɗabi’a wanda mutum yake yi wa wani abu kamar doki ko wata dabba ko makami ko wani wasa na motsa jiki ko dai wani mutum haka don kawai ra’ayinsa.

 Bayan haka Sa’id (1982:9) ya ƙara bayyana wasu sigogi na soyayya da suka haɗa da:

-         Soyayya mafificiya – wato wadda ake musayarta tsakanin masoya biyu (kana so ina so)

-         Soyayya mafi tsarki wato wadda babu batsa a cikinta. Soyayya ce tsantsa ba tare da tunani ko buƙatar saduwa ta jiki ba.

-         Soyayya gurguwa – Wato wadda ɓangare ɗaya yana matuƙar so, amma ya kasa bayyana son a wajen namiji ko wajen mace.

-         Soyayya mafi muni – Wato wadda ɓangare ɗaya kawai ke so ɗayan ba ya so (wato yana so, ba ta so, ko tana so, shi ba ya so).

 Dangane da irin soyayyar da ake nunawa a finafinan Hausa ta shafi kaso na biyu wato soyayya tsakanin mace da namiji da soyayya mafi muni wadda ɓangare ɗaya kawai ke so ɗayan ba ya so, da kuma soyayyar yaudara da ake yi saboda kuɗin iyayen mace ko namiji.

 Misali a cikin fim ɗin Kallabi da kamfanin H.R.B Production suka shirya an fito da jigon a fili domin tun daga farko har ƙarshe soyayya kawai aka nuna a matsayin babban jigo kamar yadda Ahmad S. Nuhu ya riƙa nace wa Maryam, ita kuma ta yi ta ja masa aji, kafin daga baya ta ba da kai bori ya hau. Sannan ƙananan jigogin da ke cikin wannan fim sun haɗa da taimako kamar yadda ƙawar Maryam ta taimaki Murtala da kuma yaudara kamar yadda 'yanmata da samarin cikin wasan suke yi wa kawunansu.

 Sauran finafinan da suke ɗauke da jigon soyayya sun haɗa da Dawayya da Kushu’i da Ɗansoyayya da Hayaƙi da Wasila da Mujadala da Tsumagiya da hayaƙi da Girma da Masoyiyata da Soyayya Ƙaunar Zuci da In da so da Ƙauna da Rana da Ƙugiya da Ciwon Ido da Isan da Uƙuba da Ina son sa haka da Zabari da Katanga da Dafi da Limza da Sharaɗi da Ƙamshi da Turare da sauransu.

1.3.4 Faɗakarwa

 Wannan na nufin faɗakar da mutane a kan wani abu marar kyau da suke aikatawa da su daina ko su gyara ko a ƙarfafa riƙo da wani aiki mai kyau. Akan shirya fim a nuna wani mutum yana aikata wani hali da bai dace ba kuma a ƙarshe ya wulaƙanta, har yakan nuna ya yi nadama. Irin waɗannan finafinan suna taimakawa wajen canza halayen mutanen da suke aikata ba daidai ba, wala Allah  a bisa dalilin jahilci ko rashin mafaɗi.

 Bargery, (1934:288) ya bayyana ma’anar faɗakarwa da “zaburar da faɗakar da a sa mutum ya fahimta, a sanya mutum ya gano wani abu na haƙiƙa wanda aka rigaya aka mance”. Ya ci gaba da cewa faɗakarwa takan ta da tsimin mutum”.

 'Yar’aduwa (2001:126) cewa ya yi faɗakarwa na nufin “nusar da mutum a kan abubuwna da ya sani tun tuni, amma saboda sakaci ya ƙyale su, ya manta da su. Don haka ne ake yi masa tuni, da yi masa hannunka-mai-sanda, don ya dawo ya yi la’akari da su”.

 Faɗakarwa takan shafi gargaɗi da nasiha da gyran hali da sauran hanyoyin inganta rayuwa da kuma gyara ta.

 Misali a cikin fim ɗin Jankunne an faɗakar da mutane a kan yadda ake kamuwa da cutar ƙanjamau, da kuma irin halin da samari masu neman mata suke faɗawa. Babban jigon wannan fim shi ne faɗakarwa a kan cutar ƙanjamau. Sannan kuma akwai ƙananan jigogi da suka haɗa da illar tallan 'ya mace da haɗarin da ke tattare da neman mata da kuma sakamakon marar ɗaukar shawara.

 Sauran finafinan da suke ɗauke da irin wannan jigo, sun haɗa da Nasaba da Zarge da Aisha da Badaƙala da Dangaye da Sihiri da jahilci ya fi Hausa da Jirwaye da Buri da Halak da Tubali da Darasi da Ƙauli da Ruhi.

 Daga cikin abubuwan da finafinan Hausa kuma sukan yi gargaɗi a kansa, akwai nuni a kan illolin cin amana. Cin amana na nufin yi wa wani abin kirki shi kuma ya saka da na tsiya. Kuma tana faruwa a kowane ɓangare na rayuwa kamar iyali ko abokai maƙwabta ko abokan kasuwanci ko aiki da sauransu. Sannan a wannan zamanin abin ya zama uwan dare, wanda sai mutane ƙalilan en suke kare kansu daga cin amana kuma sakamakon ta ne ya sa mutane da yawa na wannan lokaci suka kasa ci gaba a rayuwarsu. Sakamakon yawaitar cin amana a tsakanin al’umma ya sa ake shirya finafinai a kai domin tunasar da al’umma illolinta da kuma muhimmancin riƙe ta domin a ci gaba da riƙe ta ko a daina aikata ta. Bagery (1934:116) ya bayyana cin amana da “tona asiri ko Baraka”.

 Misali a cikin fim ɗin Maula mun ga yadda sakamakon mai cin amana ya kasance wato Hindatu Bashir da ƙaninta Ali Nuhu wadda ta kai su har da bara a tiit, kuma babban jigon wannan wasa na Maula  shi ne faɗakarwa kan cin amana domin duk sauran abubuwan da aka yi a cikin shirin an yi shi su ne domin su taimaka wajen fito da babban jigon shirin, wato faɗakarwa kan cin amana. Ƙananan jigogin da ke cikin fim ɗin kuwa sun haɗa da taimako kamar yadda Alhaji ya taimaki Ali Nuhu da yayarsa Hindatu Bashir da Makirci kamar yadda Ciroki da Hindatu suka yi da kuma magani kamar yadda Hindatu ta yi wa Alhaji ya saki matarsa.

 Haka zalika sauran finafinan da suke ɗauke da irin wannan jigo na faɗakarwa kan cin amana sun haɗa da Ɗan’uwa da Ɗan’adam da Mukhtar da Jinsi da Juyin Mulki da Ruhi da Furuci da Saura ƙiris da Ayah da Sufuri da Gadar zare da sauransu.

1.3.5 Jigon Wayar da Kai

 Wayar da kai wata hanya ce da ake amfani da ita wajen sanar da mutane a kan wani abu da suke aikatawa ba daidai ba, kuma ana amfani da wayar da kai wajen neman al’umma su karɓi wani abu da ake so su karɓa daga gwamnati ko waɗansu ƙungiyoyi masu zaman kansu.

 Gusau (1995:16) Ya bayyana wayar da kai da cewa “yakan yi ƙoƙari ne ya sanar da mutane wasu abubuwa sababbi da suke aukuwa a rayuwar yau da gobe”. Ta haka ne finafinan Hausa ke taimakawa wajen yi wa jama’a sanarwa da faɗakarwa da gargaɗi kan gyaran rayuwa.

 Misali a fim ɗin Tsautsayin Takaba mun ga yadda aka wayar wa da 'yanmata kai wajen soyayyar gaskiya maimakon ta kuɗi da kuma irin sakamakon da Bebi ta samu na gamuwa da cutar ƙanjamau. Kuma babban jigon wannan fim shi ne wayar da kai, sannan akwai ƙananan jigogi waɗanda suka haɗa da cin amana kamar yadda Bebi ta yi wa Abdul da sakamakon mai kwaɗayi kamar yadda Bebi ta gamu da cutar ƙanjamau da kuma soyayya kamar yadda aka nuna a cikin fim ɗin.

 Sauran finafinan da suke ɗauke da irin wannan jigo na wayar da kai sun haɗa da Inuwar Giginya da Alheri da Linzami da Sutura da Gashin Ƙuma da Gyale da Lokaci da Fito na Fito da Sunduƙi da Sansani da Halacci da Sukuni da Kasko da Ki Yarda da ni da Ƙasarmu ce da Sadaki da Sauyi da sauransu.

1.3.6 Jigon Bandariya

 Bandariya hanya ce da ake amfani da ita wajen sanya mutane su yi dariya da walwala da kuma nishaɗi wanda suke ɗaukar wani darasi ta hanyar dabara.

 Bargery, (1934:76) ya bayyana “bandariya da cewa ta samo asali daga “Bandare wadda take nufin mutum mai bayar da dariya ko mai sa a yi dariya”. Shi kuma Ibrahim M.S. (1976:104), ya bayyana bandariya da irin waƙoƙin da 'yan gambara da 'yan kama da 'yan galura da 'yan ƙoroso suke yi. Amma kuma sun bambanta ta hanyar da suke bi, su bai wa mutane dariya. Misali 'yan kama sukan ba mutane dariya ta wajen kwaikwayo da waƙar abinci. 'Yan gambara kuma ta wajen batsa da ba’a. 'Yan ƙoroso kuma ta wajen shaƙiyanci da alfasha. Haka ma 'yan galura”.

 A finafinan Hausa ana amfani da bandariya wajen isar da wani saƙo ta hanyar wasa, wadda mutane suke koyar da wani darasi ta hanyar nishaɗi, yawancin finafinan bandariya Ibro ne yake shirya su, sannan ya bayyana cewa yana yin su ne domin isar da wani saƙo cikin raha tun da mutane ba wa’azi suke son saurara ba. (Hira da BBC, 2003).

 Misali fim ɗin “Jahilci Ya Fi Hauka Wuyar Magani”. Babban jignsa shi ne bandariya, domin tun daga farkon shirin har ƙarshensa jigon ya ratsa ko’ina kuma ya koyar da hanyar nishaɗi. Akwai kuma ƙananan jigogi da suka bayyana a cikin fim ɗin waɗanda suka haɗa siyasar gargajiya da illar jahilci da tafiye-tafiye.

 Sannan misalan finafinan da suke ɗauke da irin wannan jigo sun haɗa da Ibro Mafiya da Ibro Maitsine da Ibro D.P.O. da Ibro Siniya da Ibro Ɗandaudu da Ibro Maishayi da Kar-ta-san-kar da Ibro Usama da Ibro Shata da Ibro Ɗanƙwaito da Gidauniya da Bobmai da sauransu.

1.4      Naɗewa

Tun a farkon wannan takarda an yi bayanin cewa fitar da jigo a finafinan Hausa ra’ayi ne, da za a iya samun daidaito ko bambanci a tsakanin manazarta a kan wani fim da suka yi nazari a kansa .
Haka a wannan takarda an yi hasashen wasu nau’o’in jigogi da ake iya samu a finafinan Hausa kuma aka kawo misalansu. An yi magana a kan jigon haƙuri da faɗakarwa da siyasa da soyayya da wayar da kai da kuma ban-dariya.

Manazarta

Abdullahi, I.I. (1998). “Nazarin Littattafan Soyayya na Hausa”. Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayero, Kano.

Abdulƙadir, H.M. (1988). “Rayuwar Malam Ibrahim Mandawari ta Fuskar Wasan Kwaikwayo da Yunƙurin Samar da Finafinan Hausa”. Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano.

Adamu, A.U. (2003). The Hausa Home Ɓideo: Media Parenting and Changing Popular Culture in Northern Nigeria (In press)

Adamu, U.A. (2004). Passage to India Media and Construction of African Identities. Essay Report of a Seminar Held in Nairobi, Kenya.

Adamu, Y. (2002). Between the Word and the Screen: A Historical Perspectiɓe on the Hausa Literary Moɓement and the Home Ɓideo Inɓasion, Journal of African Cultural Studies Ɓol. 15. No2. 203-213.

Alfred, E.O. and Opubor, O.E. (1977) .The Deɓelopment And Growth of the Film Industry in Nigeria Lagos. Third Press International.

Bargery, G.P. (1934). Hausa-English Dictionary And English-Hausa Ɓocabslary London Oɗford Uniɓersity Press.

Buhari, M. (1988). “Nazarin Jigon Wasu Littattafan Ƙagaggun Labarai na Hausa”. Kudnin digiri na Biyu, jami’ar Bayero, Kano.

Centre for Hausa Cultural Studies (2004) Hausa Home Ɓideos Technology, Economy and Society, Kano. Gidan Dabino Publishers

Chamo, I.Y. (2002). “Tasirin Al’adun Turawa a cikin Finafinan Hausa”. Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano.

Ɗangambo, A. (1981). “Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa”. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Ɗangambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company.

Ɗangambo, H.A. (2002). “Salon Sarrafa Jigo a Adabin Baka na Hausa: Nazari Kan Jigon Faɗakarwa”, Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano.

 East R.M. da Wasu (1948) Zaman Mutum da Sana’arsa, Kamfanin NNPC, Zaria.

Funtua, A.I. (2002). Waƙoƙin Siyasa na Hausa a Jamhuriya ta Uku: Jigoginsu da Sigogsin”, Takarda da Aka gabatar a Taron Ƙara wa Juna Ilimi, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, jami’ar Bayero, Kano.

Furniss, G. (1977). “Some Aspects of modern Hausa Poetry: Hikima Poetry Circle Club in KanSo” London SOAS.

Gusau, S.M. (1983). “Waƙoƙin Noma na baka: yanaye-yanayensu da sigoginsu Musamman a Sakwkato”. Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayero, Kano.

Gusau, S.M. (1995). Saƙo a Waƙoƙin Baka: Tsokaci Kan Turke da Rabe-Rabensa”. Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna ilimi a Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Kan harshe da Adabi da Al’adun Hausawa, Jami’ar Bayero, Kano.

Ibrahim, M.S. (1976). Kowa Ya Sha Kiɗa: Abinsa ya Bayar, Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano

Inuwa, U.A. (2000). “Tarbiyya cikin Finafinan Wasan Kwaikwayo na Hausa”. Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayero, Kano

Kundila, H.M. (2002). “Yadda Ake shiryawa da Gudanar da Finafinan Hausa” Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano

Mashi, M.B. (1986) Waƙoƙin Baka na Siyasa: Dalilansu da Tasirinsu ga Ryuwar al’umma” Kundin Digiri na Biyu, jami’ar Bayero, Kano.

Muhammad, N.M. (2002). “Mata a cikin Finafinan Hausa, Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayero, Kano

Umar, A.A. (2002). “Gudunmawar Finafinan Zamani a Ɓangaren Adabin Hausa”. Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Bayero, Kano

'Yar’aduwa, T.M. (2001). “Wasan Kwaikwayo: sigoginsa da Jigoginsa” cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies Ɓol. 1, No. 1 Department of Nigerian Languages, Bayero Uniɓersity, Kano.

Post a Comment

0 Comments