Amshi:
Dubun jama’a na
alhinin,
Rashin masanin
dattijon nan,
Mu dau darasin mutuwa
dangi,
Allah ya jikan malam Giro.
1. Tabaraka Sarki Ya
Allah ka amshi batun angon Mero,
Ka min fatahi na yi
‘yan baiti akan mutuwar Malam Giro,
Mazaunin Kebbi na Argungum
fagen da’awa babban kwaro,
Abinda ka yo duka mun
shaida Ilahu Ya Yarda ka yo moro.
2. Abar fahari Sunna
TV tana ta’aziyya gun kowa,
Musulmai harda
kiristoci akan rasa malam dan baiwa,
Mu dau hakuri jama’ar
yankin Arewa da ku na Kudadawa,
Da Ghana da Niger har
Camaru fari da baki duka na jero.
3. Cikin hidimar
da’awar sunna a Burkina Faso ya bar baya,
Ya assasa tushen
alkairi kamar wanka da farin kaya,
Hakan yayi ma a kasar Benin Kwadebuwa basu sahun baya,
Gabon ma ya musu
alkhairi da mai aurensu da ma gwauro.
4. Abin sha’awa a
halin malam abubakari bai son girma,
A duk matsayinsa
abokansa yakan yi makaho har kurma,
Yakan dauko karamin
yaro abokai nai ku sako ni ma,
Hakan ya saka dukkan
jama’a suke kaunar malam giro.
5. Ku duba ma a fagen
da’awa da kaifi dai yaka yin zance,
Kasancewarsa cikin
JIBWIS da su da wasunsu yana dace,
Yakan bi sahun yin
adalci dukan rikicinmu ya magance,
Izala in wani yai
laifi mu kai kara a wajen Giro.
6. Kamar gaushi yake
gun zafi da an taba sunna ba wasa,
Yakan cire dukka
makami nai wukarsa yaje shi ya wawwasa,
Idan ko da shi kaka
yin rigima Sadiqu baza shi ya dau fansa,
Abubakari mutumin
kirki Allah ya jikan malam Giro.
7. Dukan jama’a sun
yo shaida akan mutumin kirki Giro,
Kafafen sada zumunci
kaf da ka shiga sai maganar Giro,
Yana wa’azinsa yana
kuka hisabi dai yaka yin tsoro,
Yana neman afuwar
bayi Ilahu ka haskaka Sheik Giro.
8. Aboki sai ka yi
hankalta abinda ka yo shi za a fada,
Idan ka bar abu mai
kyawu status za a saka mu nada,
Da ka mutu sai a ta
yin fostin ana jama’a ku ga wannan da,
Mala’inku kuwa su
shaidar mutane dai suka sauraro.
9. Akwai wasu wanda a
halinsu sukan yi rawa da kidan ganga,
Mazansu da mata na
shewa tsiraici nasu ana hanga,
Su dauka sai su saka
tiktok da youtube tunda hakan suka ga,
Garesu kamar shine
mafita suna watsi da fadin Giro.
10. Tashar Sunnarmu
tana ta kiran ku dauki halinga na babana,
Ina kuke limaman
sunna da ma mabiyanku abokaina,
Ku taru ku kama irin
tsarin Abubakarinmu masoyina,
Idan kuka zo mutuwa
kuma a dinga yabonku kamar Giro.
11. Ku dau hakuri
‘ya’yan malam da mata nai da abokai ma,
Irin wannan mutuwa
kowa ta shafa dan abu ya girma,
Rashin Malam da akwai
zafi a da can mun rasa Manzo ma,
Kawai sai dai muta
yin adu’a Allah ya jikan malam Giro.
By:
Mahmud Ahmad Musa (Mahmudul Khalam) +234 902 019 4569
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.