Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Kika Kirata A Waya Kukai Fada To A Bakin Aurenki, Sai Ta Kira Da Private Number

TAMBAYA (20)

Assalam (Tambayace) Shigen wanda ya ce in ta fita ta kofar nan abakin auranta

Toshima kusan hakanne Tace seta kirata sunyi fada taci mata mutunchi snn ta fada mata fa tasan meke tsakanin su Shine shikuma ya ce inta kirata tai mata hakan abakin auran ta Ita kuma seta kira da private number batai mgn ba tai tsaki kawai ta kashe

AMSA

Waalaikumussalam. Waalaikumussalam. Wabarakatuhum.

Sakin da aka saka sharadin anyishi silar fita ta kofa shi ake kira "Talaq al-bab" a shari'a wanda an samu sabanin malamai sosai akan tabbatuwarsa

Wasu malaman sukace sakin da miji yayi akan sharadin matar ta fita ta window bai tabbata ba saboda ai sharadin shine sai ta bi ta kofa

Wasu kuma malaman sukace idan ta fita ta window dukda sharadin mijin shine ta kofa to kawai ta saku saboda muhallish shahid din shine fita daga gidan baki daya

Wasu malaman sukace saki daya ne wasu kuma sunce uku ne wasu kuma sukace kamata yayi a tambayi mijin me yake nufi da a bakin aurenta ?

To kamar hakane idan ya zamana ta kira waccan ta private number tunda ba kiranta tayi direct ba

Sai aji ta bakinsa shin saki yake nufi ko kuma gargadi yake mata kada ta kira matar don ya tsoratata

Wannan shine ra'ayin da muka tafi akai, in sha Allah

Domin karin bayani sai a duba Alwajiz Fi fiqhis Sunnah a cikin babin saki (Talaq)

A karshe ina son na ja hankalin matan aure su daina wasa da al'amarin saki. To in banda ma biyewa shaidan da son zuciya menene alfanun kiranta ta private. Kada ku mantafa Aljannar matar aure tana duga-dugan mijinta (ta hanyar yi masa biyayya) Kamar yanda Annabi SAW yabawa Ummu Adiyya RA amsa lokacinda ta tambayeshi maza suna zuwa makabarta an hani mata da zuwa, maza suna yin yaqi mata basayi, ta yaya mata zasu kamo maza a daraja sai ya ce (SAW) biyayya ga mijinta. Yayinda kuketa sabawa umarnin miji wasu suna can mijin suje nema ruwa a jallo basu samu ba. Allah ya shiryemu ya bamu ikon gyarawa

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman D. Mato (Usmannoor_As-salafy)

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments