Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Kallace-Kallacen Fina-Finan Series

TAMBAYA (21)

Assalamu Alaikum warahamatullah mln muna gdy d kokari da kukeyi Allah ya Saka d Alkhairi Tambayata kallan Finafinai fa duba d yanzu mutane sun shagalta da kallace kallecan syris dinnan a wayoyi kullum sabo akeyowa wani sai kaga yana kallan yakai kala goma alokaci daya Allah ya shiya mana zuri'a

AMSA:

Waalaikumussalam. Warahmatullahi. Wabarakatuhum

Dangane da kallon series movies ya danganta da wanne irin video ake kallo. An samu sabanin malamai gameda hukuncin kallo fina-finai. Wasu malaman sunce ba haramun bane indai har babu wani abu da yake nuna rashin tarbiyya ko kuma aikin zunubi kamar kallon fina-finan batsa

Wasu malaman kuma sukace haramunne tunda hakan zai kai mutum ga fadawa tarkon shaidan musamman na idan mutum ya kalla da niyyar sha'awa

A takaice dai hukuncin kallace-kallacen films a addini yanada alaqa da hadisin:

 : إنما الأعمال بالنيات

(Innamal a'amalu binniyyati)

Ibn Abbas, Ibn Mas'ud Ibn Umar, Abu Hurairah da Nana Aisha (RTA) duk sun karbo hadisin

(Sahihul Bukhari Chapter 1 hadisi na 1 da kuma Sahih Muslim Chapter 1 hadisi na 1907)

Idan video ne wanda ya shafi fadakarwa, wa'azantarwa tareda ilimantarwa kamar irinsu YouTube channels: Karatuttukan Malaman Sunnah, da kuma irinsu Rational Believer, One Path Network, Sense Islam, One Islam Production, Towards Eternity, Qur'an and Islam, Allah And The Cosmos, Ink Of Knowledge da dai sauran YouTube channels da suke dora videos domin amfanuwar musulmai to wannan kam abune mai kyau kuma idan mutum yayi koyi da ilimin zai samu lada

Amman idan ya zamana mutum bazai maida hankali wajen kallon videos da zasu ilimantardashi akan addininsa ba to tabbas sai ka tsinceshi a bangaren kallon fina-finan series wadanda bazasu anfana masa komai ba anan duniyar ballantana a lahira

Mutane suna shagaltuwa da son zuciya suna taya shaidan yin nasara akansu, zakaga mutum yana saka sama da N1,000 don kawai ya kalli online series alhalin ga malaman addini can suna da'awa mutum ba tasu yake ba, tareda cewar dukkan second daya na agogo abin tambayane a ranar lahira haka kuma abin da mutum ya kalla, ya saurara kuma ya raya a zuciya to sai an tambayeshi wannan abun kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin al-Qur'ani mai girma:

( وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ ۚ إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَٰئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا )

الإسراء (36) Al-Israa

Kuma kada ka bi abin da bã ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya.

Haka kuma babu danasanin da mutum zaiyi ranar lahira sama da na wanda ya karar da lokacinsa a sharholiyar duniya. Da ace masu bata awanni suna kallon series zasu san falalar dake cikin ibada da sun daina kallon gaba daya. Allah SWT ya ce:

( وَأَقِمِ الصَّلَاةَ طَرَفَيِ النَّهَارِ وَزُلَفًا مِّنَ اللَّيْلِ ۚ إِنَّ الْحَسَنَاتِ يُذْهِبْنَ السَّيِّئَاتِ ۚ ذَٰلِكَ ذِكْرَىٰ لِلذَّاكِرِينَ )

هود (114) Hud

Kuma ka tsai da salla a gfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. wancan ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa.

Ba abin haushima sama da yanda zakiji matar aure tana kafa hujja da wani dan film ko yar film zakiji ana "kamar dai abin da jaruma wance tayi a film din..." A maimakon tace "kamardai yanda matan sahabbai suka yi abu kaza da kaza suka rabauta fiddunya wal akhira"

Tasirin kallace-kallacen fina-finai ba a iya kasarmu ya samu matsuguni ba, hatta gwamnatin kasar Saudi Arabia ma ta karkata akalarta wajen ganin an kashe dollar miliyan dari biyu da talatin da hudu ($234 millions) don gina masana'antar wasan kwaikwayo (film industry), wanda a karkashin Project 2030 da yarima Muhammad Bin Salman ya zartar, za a gina gidajen kallo (cinema theaters) guda 350 da kuma Plasma (TV) guda 2,500 kamar yanda ministan watsa labarai (Awwad al-Awwad) na kasar ta Saudiyya ya fada. Wanda wannan ba karamin ci baya bane a yanda ake yiwa kasar kallon kasa mai kima a idon duniyar musulunci. Wanda hakan zai tabbatar maka da cewar shirye-shiryen yahudawa da nasara sun fara tasiri ga gwamnatin kasar

Yakamata mu dinga tsarkake zukatanmu da ambaton Allah da yawaita Istighfari a kowanne lokaci domin inganta ranmu a maimakon aikata abin da zai bata maka lokaci. Kamar yanda Allah SWT ya ce:

( قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّاهَا )

الشمس (9) Ash-Shams

Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.

Muna roqon Allah ya rabamu da son zuciya ya tabbatardamu akan bin tafarki madaidaici

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments