Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'ar Da Idan Kayi Allah Zai Amshi Buqatarka

TAMBAYA (19)

Dan Allah adduar biyan bukata fah

AMSA

Annabi SAW ya ce duk wanda yayi addu'ar ma'abocin kifi (Annabi Yunus AS) ya roqi Allah wata buqata to za a biya masa

Lokacin da Annabi Yunus yayi hijira daga garinsa batareda umarnin Allah SWT sai ya shiga jirgin ruwa, akayi kuri'a silar tambal-tambal da ruwan tekun yake, kuri'a fa fada kan Annabi Yunus, mutanen jirgin suka wullasa cikin tekun

Ya nutse can kasa, kifi ya hadiyesa kamar yanda Qur'ani ya tabbatarda faruwar hakan:

( فَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ وَلَا تَكُن كَصَاحِبِ الْحُوتِ إِذْ نَادَىٰ وَهُوَ مَكْظُومٌ )

القلم (48) Al-Qalam

Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.

A lokacin da ya tuno musabbabin faruwar hakan sai ya koma ga Allah SWT:

( وَذَا النُّونِ إِذ ذَّهَبَ مُغَاضِبًا فَظَنَّ أَن لَّن نَّقْدِرَ عَلَيْهِ فَنَادَىٰ فِي الظُّلُمَاتِ أَن لَّا إِلَٰهَ إِلَّا أَنتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ الظَّالِمِينَ )

الأنبياء (87) Al-Anbiyaa

Kuma mai kifi a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai."

Nan take Allah SWT ya amsa roqon bawanSa harma ya ce:

( فَلَوْلَا أَنَّهُ كَانَ مِنَ الْمُسَبِّحِينَ )

الصافات (143) As-Saaffaat

To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,

( لَلَبِثَ فِي بَطْنِهِ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ )

الصافات (144) As-Saaffaat

Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.

An karbo daga Abu Dharr al-Ghifari (RTA) ya ce, Annabi SAW ya ce: "Kada kuyi tunanin kunfi Yunus Ibn Matta (AS). Ya kira Ubangijinsa ya ce: "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai.

(Sunan Abu Dawud: 3871 da kuma As-Sifah al-Jami'ah na Imam al-Bayhaqi)

Sannan kuma akwai lokutan amsar addu'a. Kamar lokacin da ladan ya kammala kiran sallah

عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال رسول صلى الله عليه وسلملا يرد الدعاء بين الأذان والإقامة».

رواه أبو داود و الترمذي

An karbo daga Anas Dan Malik Allah ya kara yarda da shi ya ce Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce: «Ba'a maida addu'a tsakanin kiran sallah da tayar da sallah»

(Abu Dawud da Tirmiziy ne suka rawaitoshi)

Don haka da zarar kinji ladan ya kira sallah saiki maimaita abin da ya ce (saidai idan ya ce Hayya alal fala da Hayya alas sala ke kuma zakice "Lahaula wala quwwata illa billah) bayan ya gama saiki karanta "Lailaha illa antas subhanaka inni kuntu minazzalimin" ki yi salatil Ibrahimiyya sannan ki roqi dukkan abin da kike so

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments