Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Sallar Nafila Bayan Wutiri!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam, Allah ya kara maka basira, malam dan Allah tambayata a nan ita ce, ni ce na yi sallar Isha, na kuma yi Shafa'i da Wuturi, to kuma sai Allah ya ba ni ikon tashi cikin dare, shin Wuturi zan sake ko dukka zan sake?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salám, amin na gode bisa addu'o'iku na alheri. Babu laifi ga wanda ya  yi wutiri a farkon dare ko a tsakiyar dare idan ya sake yin wata sallar nafila a daren a bayan wutirin nan nasa, sai dai abin da aka fi so shi ne mutum ya sanya sallarsa ta qarshen dare ta zama wutiri ne, saboda Abdullahi ɗan umar ya ruwaito cewa Annabi ya ce: "Ku sanya sallarku ta qarshen dare ta zama wutiri".

Albukhariy (998), Muslim (751).

Amma wanda ya riga ya yi sallar wutiri, to idan ya sake yin wasu raka'o'in a bayanta ba zai sake maimaita wani wutiri daga baya ba. Saboda hadisi ya tabbata daga Dalq ɗan Aliyu ya ce: Na ji Manzon Allah yana cewa: "Ba a wutiri biyu a dare ɗaya". Attirmizhiy (470), Annasá'iy (1679), Abu Dawud (1439).

Wato dai a taqaice idan mutum ya riga ya yi sallar wutiri sai kuma daga baya ya so ya yi sallar nafila a daren, to hakan ya halasta ba tare da wani karhanci ba, saboda umurnin da Annabi ya bayar cewa a sanya sallah ta qarshe a dare ta zama wutiri, ba umurni ne na wajabci ba, umurni ne na mustahabbanci, sai dai kamar yadda bayani ya gabata, duk wanda ya yi sallar wutiri, kuma ya qara yin sallah a bayanta, to  ba zai maimaita wani wutiri na biyu ba, kamar yadda hadisin can ya bayyana.

Dubi Almuhallá (2/91, 92), da Almajmú'u (4/16).

Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments