Hukuncin Tsotsar Al'aura Da Shan Maniyyi

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene Hukuncin Ma'aurata Suji Daɗi Da Bakinsu Wato Tsotsar Al'aurar Junansu? Shin Ya Halatta Mutum Ya Bawa Matarsa Maniyyinsa Ta Sha, Wai Yana Gyarawa Mata Jiki?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Miji shari'a ta bashi dama yaji daɗi da matarsa yanda yaso, yaje mata ta inda take haihuwa ta kowanne guri yaso, Kamar yanda Allah yafaɗa acikin aya ta (223) cikin suratul Baqara:

    نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ لَكُمْ فَأْتُوا حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ ۖ

    Mãtanku gõnaki ne a gare ku, sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so. (Suratul Bakara: 223)

    Abu biyu aka haramtawa miji wajan zakkewa matarsa.

    1. Saduwa lokacin haila, Kamar yanda Allah yafaɗa acikin ayata (222) cikin suratul Baqara:

    وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ ۖ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ ۖ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ ۖ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ ۚ

    Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. (Suratul Bakara: 222)

    2. Saduwa ta dubura, Manzan Allah (Sallallahu Alaihi wasallam) ya ce: Tsinanne ne duk wanda yajewa matarsa ta dubura,) Abu dawda da Ahmad suka ruwaito shi, Albani ya Ingantashi acikin Saheehu jami'i (5889).

    Duka Ababe biyun Wani hadisin Ya haɗesu baki ɗaya, Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) ya ce: Ku guji saduwa ta dubura da lokacin Haila). Ahmad Abu dauda suka ruwaito shi, Yana cikin jami'ussaheeh (1141).

    Tsotsar Al'aura da baki, Akwai sharudda guda biyu;

    1- Yakasance hakan baya cutarwa, ko jawo cuta.

    2- Kada yazama sababi na wucewar najasa zuwa maqogwaro.

    Idan Mace tana tsõtsar azzakarin Mijintaharyakai ga yin Inzãli (fitar maniyyi) acikin bakinta,  Alal-Haƙiƙa anan Mãlamai sunyi Saɓãni a kan wannan Mas'ala, kuma Saɓãnin nãsu yã ginune a kan Mas'alar cewa Shin Maniyyi najasãne ko ba najasã bane? Mãlaman da suka tafi a kan fahimtar cewa Maniyyi najasane sukace Harãmunne Mace tasha, domin baya halatta ga Mutum Musulmi yaci ko yasha dukkan abinda yakasance najasãne.

    Saidai Magana mafi Inganci kamar yadda wasu daga cikin Mãlamai suka rinjayar ita ce, cewa Maniyyi ba najasa bane, to amma Saidai Mãlamaisukace duk da kasancewar Maniyyi abune Mai-tsarki ba najasaba, sukace bai kamata ace Mutum yãsha Maniyyiba, domin yin hakan yana daga cikin ​ƙazanta, kamar yadda bai kamataba aga Mutum yana shan Mãjina ba, duk dacewa Majina ba najasa bace amma ko shakka babu cewa shanta ɗin ​ƙaƙazantane.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    HUKUNCIN SHAN MANIYYI

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin Ya Halatta Mutum Ya Bawa Matarsa Maniyyinsa Ta Sha, Wai Yana Gyarawa Mata Jiki?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Idan ​Mace tana tsõtsar azzakarin Mijinta​ haryakai ga yin ​Inzãli (fitar maniyyi)​ acikin bakinta, ​Alal-Haƙiƙa anan Mãlamai sunyi Saɓãni​ akan wannan ​Mas'ala,​ kuma ​Saɓãnin​ nãsu yã ginune akan Mas'alar cewa ​Shin Maniyyi najasãne​ ko ba najasã bane? ​Mãlaman​ da suka tafi akan fahimtar cewa ​Maniyyi najasane​ sukace Harãmunne Mace tasha, domin baya halatta ga ​Mutum Musulmi​ yaci ko yasha dukkan abinda yakasance najasãne.

    ​Saidai ​Magana​ mafi Inganci kamar yadda wasu daga cikin ​Mãlamai suka rinjayar itace,​ cewa ​Maniyyi​ ba najasa bane, to amma Saidai ​Mãlamai​ sukace duk da kasancewar Maniyyi abune ​Mai-tsarki ba najasaba,​ sukace bai kamata ace ​Mutum​ yãsha ​Maniyyiba,​ domin yin hakan yana daga cikin ​ƙazanta,​ kamar yadda bai kamataba aga ​Mutum​ yana shan ​Mãjina ba,​ duk dacewa ​Majina​ ba najasa bace amma ko shakka babu cewa shanta ɗin ​ƙaƙazantane.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.