Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Iyayen Annabi Muhammad ﷺ Suna Wuta Ne Ko Aljannah?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Menene Matsayin Iyayen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Tunda sun rasu kafin aiko Annabi, domin naji wasu sunata zagin wani malami wai ya ce sun mutu kafirai suna wuta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

An ruwaito hadisi daga Annabi Sallallahu Alaihi wasallam wanda yake nuna iyayensa suna wuta, Muslim yaruwaito hadisi (203) daga Anas Allah yakara yarda da shi wani mutum ya ce: Ya manzan Allah, ina mahaifina? sai ya ce: yana wuta lokacinda yabada baya (yatafi) sai ya kirashi sai ya ce: Lallai babana da babanka suna wuta.

Nawawi rahimahullahu ya ce: acikin hadisin akwai dalilin a kan duk wanda yamutu a kan kafirci yana wuta, kusancinsa dawani ba zai amfaneshiba, acikin hadisin akwai dalili a kan wanda ya mutu kafin aiko manzo a kan abun da larabawa suke na bautar gumaka shima yana wuta, wannan baya kan waɗanda suke sakon wani addinin Allah baikai garesuba, amma waɗannan larabawa sunkasance kiran Annabi ibrahim dasauran Annabawa yaje garesu, Amincin Allah da salati yakara ninkuwa agaresu.

Muslim yaruwaito hadisi (976) daka Abu huraira Allah yakara masa yarda ya ce: Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya ce: Na nemi izini agurin Ubangijina yayimun izini in nemawa mahaifiyata gafara baimun iziniba, na nemi izinin Ubangijina yayimun izini inziyarci kabarin mahaifiyata sai yaimin izini..

Yazo Acikin Aunul ma'abuud { Baimun iziniba) ya ce: saboda kafirace nemawa kafirai gafara kuma bai halatta ba.

Imamun Nawawi rahimahullahu ya ce: acikin hadisin akwai hanin nemawa kafirai gafara.

Shaik Bin baaz ya ce: Annabi sallallahu Alaihi wasallam lokacinda yacewa mutuminda yatambayeshi ( Lallai babana da babanka suna wuta) yafadane abisa ilimi (yaqini tabbas) saboda shi Annabi sallallahu alaihi wasallam baya furuci a kan son zuciya kamar yanda Allah yafada acikin suratul Najmi ayata 1-4

وَالنَّجْمِ إِذَا هَوَىٰ ١۝

Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.

مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمْ وَمَا غَوَىٰ ٢۝

Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.

وَمَا يَنْطِقُ عَنِ الْهَوَىٰ ٣۝

Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.

إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْيٌ يُوحَىٰ ٤۝

(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.

Da'ace Abdullahi bin Abdulmudallib mahaifin Annabi sallallahu Alaihi wasallam ba'a tsayar masa da hujjaba da Annabi bai fadi abun da yafaɗa akansaba, watakila sako ya isar masa wanda za a tsayar masa hujjah da shi na addinin Annabi ibrahim, domin sun kasance a kan addinin Annabi ibrahim, Alaihissalamu, har Amru bin luhayyi Alkuza'iy yafarar da abun da yafarar na bautar gumaka da kiransu darokonsu ya yaɗu acikin mutane, watakila hujja tajewa Abdullahi abun da larabawa suke kai na bautar gumaka abune batacce sai ya bisu akai, saboda haka aka tsayar masa da hujja, haka abun da yazo acikin hadisi Na Annabi yanemi izini Ubangiji daya bashi izini yanemawa mahaifiyarsa gafara amma baiyi masa izini ba, yanemi yaziyarceta anan yai masa izini, watakila abun da zai zama hujja akanta yaje mata, ko saboda mutanen jahiliyyah, suna mu'amala irinta kafirai a hukunce hukuncensu na duniya baza'ai musu addu'a ba, baza'a nema musu gafara ba, domin zahirinsu kafiraine, zahirinsu tareda kafirai suke, sai aka mu'amalancesu mu'ala takafirai Al'amarinsu yana wajan Allah alahira,.

fatawa Nurun Alar-darbi

Imamu suyudi rahimahullahu yatafi a kan iyayen Annabi za su tsira daka wuta, Allah ya rayar dasu da shi Annabin bayan mutuwarsa sukai imani dashi, amma wannan zancen dukkan malamai sunyi inkarinsa, sukai hukunci a kan hadisan da'aka ruwaito a kan haka dukkansu hadisan ƙarya ne da masu rauni sosai.

Yazo acikin Aunul Ma'abuuud duk Abun da aka ruwaito na rayar da iyayen Annabi Sallallahu Alaihi wasallam da imanin dasukai da shi dakuma tseretarsu daka wuta mafiya yawansu na ƙarya ne, kir-kirarsu akai, wasu masu raunine sosai basu ingantaba, da ittifaqin malaman hadisa wajan cewa kir-kirarsu akai, kamar darul qudny da jauzaqany da ibnu shasheen, da kadeeb da ibnu asakir da ibnu nasir da ibnul jauziy da suhaily da qurduby da muhibbul dabary da fat-huddeen bin sayyidinnasi da ibrahim halby dawasu jama,a

Hakika Allama ibraheem halby yafadada bayani a kan rashin kubutar iyayen Annabi daka wuta acikin risalarsa takaitacciya, da Allamah Aliyul qary acikin sharhun fiqhul akbar..

Abun da zai shaidi wannan matsaya shi ne hadisi ingantacce wanda ya ce: ( Babanka da babana suna wuta) shaik jalaluddeen suyidi ya saɓawa malaman hadisi da malamai tabbatattu a ilimi, yatabbatar da iyayen Annabi cewa sun tsira daka wuta yakuma tabbatar musu da imani, sai aka rubuta risaloli masu yawa a kan haka daka cikinsu akwai ( Risalatul ta'azeem walminnah a kan iyayen Annabi sallallahu Alaihi wasallam suna Aljannah).

An tambayi Shaikul Islam ibnu taimiyyah shin ya inganta daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Allah madaukakin sarki ya rayar da iyayensa harsuka musulunta ahannunsa sannan suka mutu bayan haka?

Sai ya Amsa: wannan bai inganta daka wani koda mutum dayane cikin malaman hadisi,  malamai da masana sunyi ittifaqi a kan wannan karyace kir-kirarriya, babu jayayya tsakanin malamai yana cikin hadisin karya wanda yafi tumbatsa wajan karyarsa kamar yanda malamai suka ambata, saboda baya cikin litattafai waɗanda suke madogarane a ilimin hadisi, baya cikin Bukhari ko muslim ko sunan ko a cikin Musnadai da makamantansu da litattafan hadisi sanannu, haka masu litattafan yakuna datafsiri duka basu ruwaito ba, duk da suna ruwaito hadisi mai rauni da ingantacce, domin bayyanar karyan hakan bata ɓõyuwa awajan mai addini, domin irin wannan da'ace yafaru daya kasance abun da mutane za su bashi muhimmamci dakuma kira wajan ciroshi domin yana cikin manyan Al'amura wanda al'ada da addini suka koresu ta fuska biyu:

Tafuskar rayarda matattu, dakuma tafuskar imani bayan mutuwa, dasai ya kasance nakalto irin wannan sai yafi samada nakalto waninsa, amma babu wanda yaruwaitoshi cikin malaman hadisi Amintattu zakasan ƙarya ne, sannan wannan ya saɓawa Alqur'ani da sunnah ingantacciya, da ijma'in malamai Allah maɗaukakin sarki ya ce:

إِنَّمَا التَّوْبَةُ عَلَى اللَّهِ لِلَّذِينَ يَعْمَلُونَ السُّوءَ بِجَهَالَةٍ ثُمَّ يَتُوبُونَ مِنْ قَرِيبٍ فَأُولَٰئِكَ يَتُوبُ اللَّهُ عَلَيْهِمْ ۗ وَكَانَ اللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا ٧١۝

Lallai tuba yana ga wanda suka aikata mummunan aiki abisa jahilci sannan suka tuba da gaggawa wadannan sune Allah yake karban tubansu Allah yakasance masani kuma mai hikimah. (Suratul Nisa'i: 17)

وَلَيْسَتِ التَّوْبَةُ لِلَّذِينَ يَعْمَلُونَ السَّيِّئَاتِ حَتَّىٰ إِذَا حَضَرَ أَحَدَهُمُ الْمَوْتُ قَالَ إِنِّي تُبْتُ الْآنَ وَلَا الَّذِينَ يَمُوتُونَ وَهُمْ كُفَّارٌ ۚ أُولَٰئِكَ أَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا ٨١۝

Bã tũba ba ce ga waɗanda suke aikatãwar mũnanan ayyuka har idan mutuwa ta halarci ɗayansu ya ce: "Lalle ne ni, na tũba yanzu," kuma bã tũba ba ce ga waɗanda suke mutuwa alhãli kuwa sunã kãfirai Waɗannan mun yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi (Suratul Nisa'i:18)

Sai Allah ya bayyana babu tuba gawanda ya mutu kafiri.

Allah madaukakin sarki yace

فَلَمْ يَكُ يَنْفَعُهُمْ إِيمَانُهُمْ لَمَّا رَأَوْ بَأْسَنَا سُنَّةَ اللَّهِ الَّتِي قَدْ خَلَتْ فِي عِبَادِهِ وَخَسِرَ هُنَالِكَ الْكَافِرُونَ ٥٨۝

Imanin mutum ba zai amafaneshi ba lokacinda yaga azabar Allah, wannan sunnar Allah ce data wuce a kan bayinsa, wadannan kafirai suntabe sunyi asara. (Suratul Ghaafir: 85)

Sai Allah yabada labari cewa sunnarsa acikin bayinsa ita ce imanin mutum bai amfana masa komai lokacinda yaga azaba, yaya kuma bayan mutuwa? damakamantan irin waɗannan daka cikin dalilai.

Sannan Sai shaikul Islam Abul Abbas Abduhaleem bin taimiyyah ya Ambaci hadisai biyunda muka Ambata afarkon bayaninmu.

Majmu'u fatawa (4/325)

Saboda haka wannan malami sharri ne irin na jahilai da ma'abota sanzuciya suke masa, wanda suka sabayi, komai malantar malami dayanda duniya tashaida malantarsa da tsoran Allansa idan yafadi abun da yake shi ne shari'a cikin aqida ko ibada ko tauheedi wanda hankalinsu ko tunaninsu bai daukaba saisufito suyita zage zage dacin mutunci wanda wannan bakomai bane awajan masu da'awa da ma'abota ilmi.

Allah yai mana tsari da sharrin jahilai da jahilci da san zuciyar masu son zuciya.

WALLAHU A'ALAM .

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments