Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Yayi Sallah Ba Zuwa Ga Alqibla Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Meye hukuncin mutumin da yayi sallah, sai bayan ya gama sannan ya fahimci cewa wannan sallah da yayi ba Alqibla ya fuskanta ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Yana daga cikin sharadin sallah mutum ya fuskanci Alqibla matukar ba wata matsala aka samu ba wadda zata hanashi hakan, inhar ko mutum yaki fuskantar Alqibla alhalin yana da dama toh sallarsa batacciya ce, sabida Allah ya ce:

قَدْ نَرَىٰ تَقَلُّبَ وَجْهِكَ فِي السَّمَاءِ ۖ فَلَنُوَلِّيَنَّكَ قِبْلَةً تَرْضَاهَا ۚ فَوَلِّ وَجْهَكَ شَطْرَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ ۚ وَحَيْثُ مَا كُنْتُمْ فَوَلُّوا وُجُوهَكُمْ شَطْرَهُ ۗ وَإِنَّ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ لَيَعْلَمُونَ أَنَّهُ الْحَقُّ مِنْ رَبِّهِمْ ۗ وَمَا اللَّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا يَعْمَلُونَ

Lalle ne, Muna ganin jujjũyãwar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu jũyar da kai ga Alƙibla wadda kake yardã da ita. Sai ka jũyar da fuskarka wajen Masallãci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance, to, ku jũyar da fuskõkinku jiharsa. Kuma lalle ne waɗanda aka bai wa Littãfi, haƙĩƙa su, sunã sanin lalle ne, shĩ ne gaskiya, daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatãwa. (Baqara 144).

Da umarnin da annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yayi ya ce “Sannan ka fuskanci alQibla kayi kabbara) Bukhari 6667.

Maluman sun tafi akan cewa wanda yayi sallah ba zuwa ga Alqibla ba da gangan ko a halin mantuwa zai sake, sabida bai cika sharadinta ba.

An tambayi maluman ‘Lajnatudda’imah’ kan hukuncin matafiyi da ya isa gari, yayi sallah ba zuwa ga alqibla ba, kuma bai tambaya ba, baiyi bincike ba, suka bada amsar cewa zai sake wannan sallar, sabida rashin bincike da baiyi ba, ko kokari wurin gano alqiblar, (Lajnatudda’imah Majmu’ah ta biyu 5/294).

Dan haka, ya wajaba akan wanda yayi sallah ba zuwa ga Alqibla ba yana mai mantuwa ya sake sallansa, amma in ya rasa gane Alqibla sabida rashin wanda zai tambaya, ko kuma wasu dalilai, toh mafi yawan Malamai suna akan bazai sake ba. kuma hakan shine daidai….

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments