𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malam mun gode Allah saka da
alheri da abunda kake mana. Mallam nine nayi NYSC na a Jos plateau state Mallam
sai na haɗu da
wata yer christan mallam sai Shaiɗan ya
shiga tsakaninmu har mukayi zina sai tazo tayi aure mallam da tayi aure sai muka
sake saduwa har muka kwana agidana amma kafun na kwana da ita bayan aurentan
sai abokina ya ce mun tunda ita christan ce ba komi zayyu na kwana da ita sai
na sadu da ita da aurenta mallam yanzu mene hukunci na mallam. ina cikin
matsala ayi hakuri agaya mun naji hukunci na nagode ALLAH saka da alheri.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam.
Hukuncinka daidai yake da na kowanne
mazinaci. Da farko dai kaci amanar kanka
Kuma kaci mutuncin addininka amatsayinka na Musulmi. Sannan kaci amanar hukumar
Qasarka wacce ta turaka domin yin bautar Qasa acikin al'ummar wani yankin da ba
naka ba, tunda ka aikata irin wannan laifin.
Zinar da ka aikata da ita kafin aurenta da bayan
aurenta duk laifin yana nan akanka. Shi abokin naka da ya baka wannan gurguwar
fatawar, shin mecece hujjarsa acikin shari'ar musulunci?. Kaima kasan bashi da
hujjah. Ka biye ma fatawarsa ne bisa son rai. Kuma tabbas Allah zai tambayeku
dakai dashi.
Ta hanyar aikata zina ka fitar da kanka daga layin
muminan kirki awajen Allah. Domin kuwa ita zina saboda girman laifinta awajen
Allah, yana ha'data waje guda ne tare da shirka da kisan kai. Sune laifuka uku
mafiya girma a Musulunci.
Allah yana magana acikin Alqur'ani game da siffar
bayinsa na kwarai, ya ce :
وَالَّذِينَ لَا يَدْعُونَ مَعَ اللَّهِ إِلَٰهًا آخَرَ وَلَا يَقْتُلُونَ النَّفْسَ الَّتِي حَرَّمَ اللَّهُ إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَا يَزْنُونَ ۚ وَمَنْ يَفْعَلْ ذَٰلِكَ يَلْقَ أَثَامًا
Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma
bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma
wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka. (Suratul Furqan 68)
يُضَاعَفْ لَهُ الْعَذَابُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَيَخْلُدْ فِيهِ مُهَانًا
A riɓanya
masa azãba a Rãnar Ƙiyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce. (Suratul Furqan 69)
إِلَّا مَنْ تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ عَمَلًا صَالِحًا فَأُولَٰئِكَ يُبَدِّلُ اللَّهُ سَيِّئَاتِهِمْ حَسَنَاتٍ ۗ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَحِيمًا
Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya
aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu
kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai. (Suratul Furqan 70)
Malamai irin su Ikrimah sun ce acikin Jahannama
akwai wasu ramuka guda biyu masu suna "Gayyu da Atham" acikinsu ake
jefa mazinata da sauran masu biye wa sha'awa anan duniya.
Ibnu Abid dunya ya ruwaito wani hadisi ta hanyar
Haitham bn Malik Atta'eey (Allah ya yarda dashi) ya ce Manzon Allah (sallal
Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya ce : "BAYAN SHIRKA BABU WANI ZUNUBI
MAFI GIRMA AWAJEN ALLAH FIYE DA MANIYYIN DA MUTUM YA SANYA ACIKIN MAHAIFAR DA
BATA HALATTA GARESHI BA".
Don Qarin bayani aduba tafseerin Ibnu Katheer,
Suratul Furqan ayah ta 68-70.
Ga kuma hadisin da Bukhary da Muslim ta Tirmidhiy
suka ruwaito ta hanyar Sahabbai daban daban, wanda Manzon Allah (sallal Lahu
alaihi wa aalihi wa sallam) ya ce "MAZINACI BA ZAIYI ZINA ALHALI YANA
MUMINI BA" (WATO YAYIN DA MAZINACI YAZO ZAI YI ZINA, ANA CIRE MASA IMANI
NE DAGA ZUCIYARSA).
Idan laifin zina ya tabbata akan saurayi musulmi,
ko kuma yayi furuci da kansa cewa yayi zina, to hukuncinsa shine bulala ɗari kamar yadda ayar cikin suratun Nur ta
bayyana.
Don haka nake yi maka nasihar cewa kaji tsoron
Allah ka tuba zuwa gareshi. Shi Allah mai karɓar tuban bayinsa ne. Ka nisanci zina da
duk abin da ya shafeta. Kaje kayi aure ka runtse idanuwanka daga kallon haram
ko aikata haram. Domin akwai ranar da Allah zai tambayi kowacce ga'bar jikinka
akan dukkan aikin da ka aikata da ita.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.