Ya Mutu A Wurin Sata

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ɓarawo ne ya je sata kuma sai suka kama shi suka yi masa duka har ya mutu. To menene hukuncin wannan kisan? Kuma ko za a iya cewa kisan ya zama masa kaffara, ko a ce ya yi shahada?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

    1. Ba zan iya cewa wannan mutuwar shahada ce a gare shi ba, domin ba aikin Allaah ne ya je yi, ko ya mutu yana aikatawa ba. Sai dai ko in ya tuba kafin cikawarsa, ko kuma idan ya cika da Kalmar Shahada. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    « مَنْ قَالَ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ ابْتِغَاءَ وَجْهِ اللَّهِ خُتِمَ لَهُ بِهَا دَخَلَ الْجَنَّةَ »

    Wanda ya faɗi Laa Ilaaha Illal Laah yana mai neman fuskar Allaah, sai kuma aka cika masa (ajalinsa) da ita, to ya shiga Aljannah. (Ahmad: 24028, kuma Al-Albaaniy a cikin Ahkaamul Janaa’iz (shafi: 43) ya ce: Isnadinsa sahihi ne).

    2. Kuma ba zan ce wannan kisan da aka yi masa na zalunci ya zama kaffara mai kankare masa zunubansa ba, domin a yanzu ba zan iya tuna inda wani malami ya ambaci hakan da dalilinsa mai ƙarfi ba. Sai dai kuma tun da dai sata ba kafirci ba ne, ta iya yiwuwa ya haye idan mun je lahira, kamar idan kyawawan ayyukansa sun yi rinjaye a kan munanan a kan sikeli. Allaah Taaala ya ce:

     فَأَمَّا مَن ثَقُلَتۡ مَوَ ٰ⁠زِینُهُۥ،. فَهُوَ فِی عِیشَةࣲ رَّاضِیَةࣲ

    Amma duk wanda ma’aunansa suka yi nauyi. To shi yana cikin rayuwa yardajjiya. (Surah Al-Qaari’ah: 6-7).

    3. Sannan kuma wannan kisa da suka yi masa ba daidai ba ne, tun da dai ba da wani makami ne suka same shi ba, balle har su ce sun kashe shi ne a wurin kare kawunansu daga ta’addancinsa. Don haka akwai diyya da kaffara a kansu, sai dai ko in binciken alƙalin musulunci ya tabbatar cewa ba su da wani laifi.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.