Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Rubuta Novels (Ƙagaggun Labarai)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Malam, don Allah ina da tambaya a kan rubutun labarai (ƙagaggun labarai), watau: Novels. Wasu suna ganin in mutum zai rubuta ne don faɗakarwa, duba da yadda matasanmu yanzu suke son karanta ‘novels’ a yanar-gizo, sai mutum ya yi amfani da wannan damar ya ƙirƙiri wani labari da yake ganin zai ja hankalin matasa su daina wata ɓarna’ ta hanyar nuna illolin da abin zai iya haifarwa ko yake haifarwa, musamman matsalolin da suka shafi 'social media'. Kamar yadda wata baiwar Allah ta yi rubutu a kan matsalar ‘pre-wedding pictures’. Ta fitar da matsalolin da waɗanda suka yi ‘pre-wedding pics’ a cikin labarin, suka fuskanta. Don Allah malam, me ye gaskiyar lamarin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Da farko dai ma'anar ƙagaggun labarai ita ce: Labaru na ƙarya, ba na gaskiya ba. Watau mutum ya zauna ya tsara wata tatsuniya ta ƙarya a kan wani abin da bai taɓa aukuwa ba, kuma ya yaɗa shi a cikin jama'a.

A fili ya ke cewa wannan abin laifi ne, ba daidai ba ne, saboda dalilai kamar haka:

1. Ba zai yiwu a ce wanda ya yi wannan ya kuɓuta daga shiga ƙarƙashin siffar maƙaryata ba. Kowa kuwa ya san cewa ƙarya Haram ce.

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

إِيَّاكُمْ وَالْكَذِبِ ، فَإِنَّ الْكَذِبَ يَهْدِي إِلَى الْفُجُورِ ، وَإِنَّ الْفُجُورَ يَهْدِي إِلَى النَّارِ ، وَلَا يَزَالُ الرَّجُلُ يَكْذِبُ وَيَتَحَرَّى الْكَذِبَ ، حَتَّى يُكْتَبَ عِنْدَ اللهِ كَذَّاباً

 Ku yi nesa da ƙarya, domin ƙarya tana kaiwa ne ga kangare wa Allaah, kuma kangare wa Allaah yana kaiwa ne ga shiga Wuta. Kuma mutum bai gushe yana yin ƙarya kuma yana kirdadon sharara ƙarya ba, har sai an rubuta shi a wurin Allaah a matsayin babban maƙaryaci!

2. Sannan kuma a wurin mutanen kirki mai aikata irin wannan ba mutumin kirki ba ne, shi dai mutumin banza ne kawai. Shi ya sa a wurin malaman Hadisi ba su yarda da riwayarsa. Sai ka ji sun ba shi matsayin MUNKAR , ko da kuwa ba a cikin riwayar Hadisi ne ya yi ƙaryar ba.

3. Sannan kuma ko da ya ce:  ƙurungus! irin na mai tatsuniya, watau ya bayyana cewa: Labarin ƙarya ne a farko ko a ƙarshensa, wannan bai fitar da shi daga cikin ƙungiyar maƙaryata ba.

4. Sannan kuma abu ne sananne a wurin duk masu hankali da basira cewa, irin waɗannan labaran kamar fima-fimai ne, ba su gyara mutane sai dai ma su lalata su kawai, kamar yadda muke ji da gani a kullum.

Domin surar yadda wannan abin ya ke irin a wurin masu yi shi ne:

(1). Wane ko su-wane suna shirya aikata wani sharri.

(2). Bayanin yadda suka shirya aiwatar da wannan sharrin.

(3). Bayanin matakan da suka bi don aiwatar da sharrin.

(4). Suna gab da farawa, ko suna cikin aiwatarwa, ko kuma ma sun gama zartar da sharrin.

(5). Asirinsu ya tonu, an yi rigima ko gwagwarmaya da su, an kama su. An hukunta su.

Shikenan.

5. Yawancin masu kallo ko saurare ko karatun labarin sun fi tasirantuwa da ɓangaren yadda ake shiryawa da aiwatarwa, ko zartar da sharrin, maimakon ɓangaren horo ko mummunan sakamakon da ya auku ga masu aikata sharrin. Wannan kuwa saboda maganar Allaah Ta'aala ce:

إِنَّ النَّفْسَ لَأَمَّارَةٌ بِالسُّوء

 Lallai ne rai mai yawan umurni ne da mummunan abu.

6. Maimakon ƙagaggun labarai, meyasa ba za mu koma ga kyawawan labarai daga cikin Al-Ƙur'aan da Sunnah Sahihiya ba.  Allaah Ta'aala ya ce:

نَحْنُ نَقُصُّ عَلَيْكَ أَحْسَنَ الْقَصَصِ بِمَا أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ هَذَا الْقُرْآن

Mu ne muke labarta maka mafiya kyawun labarai, saboda abin da muka yi maka wahayinsa gareka na wannan Al-Ƙur'aanin.

7. Shiyasa manyan malamai irinsu: Al-Haafiz Ibn Katheer (Rahimahul Laah) ya rubuta littafin Ƙasasul Ambiyaa'i . Watau bayan magabata irinsu Al-Imaam Al-Bukhaariy (Rahimahul Laah) a cikin mashahurin littafinsa: Sahih Al-Bukhaariy ya ware Kitaab Ahaadeethul Ambiyaa'i domin jawo kyawawan labarai masu amfani da amfanarwa ga al'ummar Musulmi. Kuma su ne asali ko tushe ga littafina: Sahihan Labarai Don Tarbiyya.

Allaah Ta'aala ya ƙara mana shiriya, ya tabbatar da mu a kan hanyar mutanen kirki har zuwa ƙarshenmu.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments