𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. A kan hadisin da ya ce:
« مَا مِنْ مُسْلِمٍ يَمُوتُ يَوْمَ الْجُمُعَةِ أَوْ لَيْلَةَ الْجُمُعَةِ إِلاَّ وَقَاهُ اللَّهُ فِتْنَةَ الْقَبْرِ »
An ce wai Al-Imaam At-Tirmiziy ya ce mai rauni ne!
Menene gaskiyar hakan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Ƙwarai da gaske! Ya
tabbata a cikin Sunan At-Tirmiziy (lamba: 1095) da isnadinsa har zuwa ga Annabi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa, shi ya ce:
« مَا مِنْ مُسْلِمٍ يَمُوتُ يَوْمَ الْجُمُعَةِ أَوْ لَيْلَةَ الْجُمُعَةِ إِلاَّ وَقَاهُ اللَّهُ فِتْنَةَ الْقَبْرِ »
Babu musulmin da zai rasu a yinin Jumma’a ko daren
Jumma’a face kuwa Allaah ya tsare shi daga Fitinar Ƙabari.
A ƙarshen hadisin ne kuma sai ya ce:
قَالَ أَبُو عِيسَى هَذَا حَدِيثٌ غَرِيبٌ وَلَيْسَ إِسْنَادُهُ بِمُتَّصِلٍ. رَبِيعَةُ بْنُ سَيْفٍ إِنَّمَا يَرْوِى عَنْ أَبِى عَبْدِ الرَّحْمَنِ الْحُبُلِىِّ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو وَلاَ نَعْرِفُ لِرَبِيعَةَ بْنِ سَيْفٍ سَمَاعًا مِنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو.
Ma’ana:
Abu-Isa (At-Tirmiziy) ya ce: Wannan hadisi ne
‘ghareeb’ (watau mai rauni), isnadinsa ba sadajje ba ne. Rabee’ah Bn Saif yana
riwaya ne kaɗai
daga Abu-Abdirrahman Al-Hubuliy, daga Abdullaah Bn Amr, kuma ba mu san Rabee’ah
ya ji karatu kai-tsaye daga Abdullaah Bn Amr ba.
A ƙarƙashin wannan bayanin, riwayar nan ta zama mai
rauni kenan saboda ba ta da sadajjen isnadi. Domin sanannen abu ne cewa: A ƙa’ida, hadisi ba ya zama saheeh (ingantacce)
ko hasan (kyakkyawa) sai in ya cika waɗansu sharuɗɗan da suka haɗa da samun saduwa ko haɗuwar isnadinsa.
Sai dai kuma malamai sun nuna cewa: Hadisin ya zo
a cikin Al-Musnad na Ahmad ta hanyoyi biyu:
1. Irin hanyar da At-Tirmiziy ya kawo, watau daga:
Rabee’ah Bn Saif daga Abdullaah Bn Amr, kuma da irin lafazinsa, a lamba ta:
6739.
2. Sai kuma ta hanyar Baqiyyah, daga Mu’awiyyah Bn
Sa’eed, daga Abu-Qabeel, daga Abdullaah Bn Amr, a lamba ta: 6805, da wannan
lafazin:
« مَنْ مَاتَ يَوْمَ الْجُمُعَةِ أَوْ لَيْلَةَ الْجُمُعَةِ وُقِىَ فِتْنَةَ الْقَبْرِ »
Wanda ya rasu a yinin Jumma’a ko daren Jumma’a za
a tsare shi daga Fitinar Ƙabari.
Sai kuma ya sake zuwa da shi da irin wannan isnadin
da lafazin a lamba ta: 7246.
A cikin wannan riwayar ta biyu babu matsalar da
At-Tirmiziy ya ambata, musamman ma ta ƙarshe (lamba: 7246) wacce isnadinta cike
ya ke da ‘tahdeeth’ da ‘samaa’i’.
Sannan kuma, hadisin yana da waɗansu shawaahid, kamar yadda
Al-Mubaarakafuuriy ya ambata a wurin sharhinsa ga wannan hadisin a cikin
Tuhfatul Ahwaziy (4/160).
Abin da ya rage sai manyan malaman hadisi su duba
su ga ko waɗannan
shawaahid ɗin
suna da matsayin da za su iya ƙarfafar wanan hadisin na At-Tirmiziy, ko kuwa ba
za su iya ba.
Shi dai Al-Imaam Al-Albaaniy ya tabbatar da cewa
za su iya. Don haka ya hassana hadisin a cikin Al-Mishkaatul Massabeeh: 1367,
kuma ya kafa hujja da shi a cikin Ahkaamul Janaa’iz, shafi: 49, inda a ƙarshe
ya ce:
فَالْحَدِيثُ بِمَجْمُوعِ طُرُقِهِ حَسَنٌ أَوْ صَحِيحٌ
Don haka, Hadisin nan ko dai hasan ne ko kuma
saheeh, lura da tattaruwar hanyoyinsa.
Waɗansu
malaman kuma a bayansa ba su amince da shi ba.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.