Ticker

6/recent/ticker-posts

Nafila A Bayan Jumma’a

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Menene matsayin nafilar da waɗansu suke yi a bayan Jumma’a? Raka’a nawa ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

A cikin hadisi Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« مَنْ كَانَ مِنْكُمْ مُصَلِّيًا بَعْدَ الْجُمُعَةِ فَلْيُصَلِّ أَرْبَعًا »

Cikinku duk wanda zai yi sallah a bayan Jumma’a, to ya yi salah raka’o’i huɗu. (Sahih Muslim: 2075)

Sannan kuma Abdullaah Bn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce:

وَكَانَ لاَ يُصَلِّى بَعْدَ الْجُمُعَةِ حَتَّى يَنْصَرِفَ فَيُصَلِّى رَكْعَتَيْنِ

Kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kasance ba ya yin sallah a bayan Jumma’a har sai ya juya, sai ya yi sallah raka’a biyu. (Sahih Al-Bukhaariy: 937)

Daga waɗannan riwayoyin guda biyu ya bayyana cewa: Ya halatta mutum ya yi nafila raka’a biyu ko huɗu a bayan Jumma’a.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments