𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Wa Rahmatul Laah, A cikin amsar
Fatawa da ta gabata kun faɗi
cewa, liman da mamu duk za su faɗi:
‘SAMI’ALLAAHU LIMAN HAMIDAH’ ne a lokacin ɗagowa daga ruku’u, kuma a lokacin tsayuwa
sai su faɗi: ‘RABBANAA
WA LAKAL HAMDU’. To, shi ne wani ya ce: Mamu ‘RABBANAA LAKAL HAMD’ kaɗai zai ce! Har kuma ya kawo hadisin da
wani sahabi yake faɗin:
‘RABBANAA WA LAKAL HAMDU: HAMDAN KASIRAN ƊAYYIBAN MUBAARAKAN FIH’, a matsayin hujja.
Wane bayani malam zai ƙara a nan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Tun a cikin amsar Tambayar da ta gabata na nuna
cewa, akwai saɓanin
malamai a kan wannan mas’alar, na ce: Amma game da mamu mai Sallah a bayan
liman ne malaman suka sha bamban. Kuma abin da ya fi bayyana a wurinmu daga
cikin maganganunsu shi ne: Shi ma dai yadda limaminsa ya yi haka zai yi, watau
ya faɗi
'SAMI'AL LAAHU LI MAN HAMIDAH' a lokacin ɗagowa, kuma ya faɗi 'RABBANAA WA LAKAL HAMDU' bayan ya gama ɗagowa. Saboda Hadisin Sahih Al-Bukhaariy
wanda a cikinsa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
صَلُّوا كَمَا رَأَيْتُمُونِي أَصَلِّي
Ku yi Sallah kamar yadda kuka ganni ina yin sallar.
(Sahih Al-Bukhaariy: 7246)
Kuma da wanda ya ce:
إِنّمَا جُعِلَ الْإِمَامُ لِيُؤْتَمَّ بِهِ
An sanya Liman ne kaɗai domin a yi koyi da shi. (Sahih
Al-Bukhaariy: 378; Sahih Muslim: 948)
Galibi a irin waɗannan mas’alolin na saɓani maganar da na yarda da ita, ita ce
nakan fi kawo mata dalilai masu tabbatar da ita. Ba safai nakan waiwayi sauran
ra’ayoyin da hujjojinsu ba.
Amma game da hadisin da ɗan’uwa ya kawo a nan, ya zo a cikin
hadisin Rifaa’ah Bn Raafi’ Az-Zuraƙiy
(Radiyal Laahu Anhu) cewa:
كُنَّا يَوْمًا نُصَلِّى وَرَاءَ النَّبِىِّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - فَلَمَّا رَفَعَ رَأْسَهُ مِنَ الرَّكْعَةِ قَالَ :
« سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ » . قَالَ رَجُلٌ وَرَاءَهُ : رَبَّنَا وَلَكَ الْحَمْدُ ، حَمْدًا كَثِيرًا طَيِّبًا مُبَارَكًا فِيهِ ، فَلَمَّا انْصَرَفَ قَالَ :
« مَنِ الْمُتَكَلِّمُ » . قَالَ : أَنَا . قَالَ :
« رَأَيْتُ بِضْعَةً وَثَلاَثِينَ مَلَكًا يَبْتَدِرُونَهَا ، أَيُّهُمْ يَكْتُبُهَا أَوَّلُ »
Watarana muna sallah a bayan Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), to da ya ɗago kansa daga ruku’u ya ce: ‘SAMI’AL LAAHU LIMAN
HAMIDAHU’, sai wani mutum a bayansa ya ce: ‘RABBANAA WA LAKAL HAMDU, HAMDAN
KASIRAN, TAYYIBAN MUBAARAKAN FIH’. Da ya juyo a bayan sallama sai ya ce: ‘Waye
mai maganar nan?’ Mutumin ya ce: ‘Ni ne.’ Ya ce: ‘Na ga mala’iku fiye da
talatin suna tsere da juna: Wanene zai rubuta ta da farko!’ (Sahih Al-Bukhaariy:
799, Sunan An-Nasaa’iy: 1070, Sunan Abi-Daawud: 770)
Amma a cikin wata riwaya kuma cewa ya yi:
صَلَّيْتُ خَلْفَ النَّبِىِّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - فَعَطَسْتُ ، فَقُلْتُ : الْحَمْدُ لِلَّهِ ، حَمْدًا كَثِيرًا ، طَيِّبًا ، مُبَارَكًا فِيهِ ، مُبَارَكًا عَلَيْهِ ، كَمَا يُحِبُّ رَبُّنَا وَيَرْضَى . فَلَمَّا صَلَّى رَسُولُ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيَْ-
Imaam At-Tirmiziy ya hassana shi, dama
kamar haka: in malamai a kan wannan mas'a kan cewaan su da kansu.هِ وَسَلَّمَ - انْصَرَفَ ، فَقَالَ : « مَنِ الْمُتَكَلِّمُ فِى الصَّلاَةِ » . فَلَمْ يُكَلِّمْهُ أَحَدٌ ، ثُمَّ قَالَهَا الثَّانِيَةَ : « مَنِ الْمُتَكَلِّمُ فِى الصَّلاَةِ » . فَقَالَ رِفَاعَةُ بْنُ رَافِعِ بْنِ عَفْرَاءَ : أَنَا يَا رَسُولَ اللَّهِ . قَالَ :
« كَيْفَ قُلْتَ »؟ قَالَ قُلْتُ : الْحَمْدُ لِلَّهِ ، حَمْدًا كَثِيرًا ، طَيِّبًا ، مُبَارَكًا فِيهِ ، مُبَارَكًا عَلَيْهِ ، كَمَا يُحِبُّ رَبُّنَا وَيَرْضَى . فَقَالَ النَّبِىُّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - : « وَالَّذِى نَفْسِى بِيَدِهِ ، لَقَدِ ابْتَدَرَهَا بِضْعَةٌ وَثَلاَثُونَ مَلَكًا ، أَيُّهُمْ يَصْعَدُ بِهَا »
Na yi sallah a bayan Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam), sai na yi atishawa, sai na ce: ‘AL-HAMDU LIL LAAHI, HAMDAN
KASIRAN TAYYIBAN MUBAARAKAN FIH, MUBAARAKAN ALAIHI, KAMAA YUHIBBU RABBUNAA WA
YARDAA.’ To, lokacin da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
ya juyo sai ya ce: ‘Waye mai maganar nan a cikin sallah?’ Babu wanda ya ce
komai. Sai ya ƙara cewa a karo na-biyu: ‘Wanene mai maganar nan a cikin Sallah?’ Sai Rifa’ah Bn Raafi’ Bn Arfraa’ ya ce: ‘Ni ne, ya Manzon Allaah!’ Ya ce: ‘Me ka ce
ma?’ Ya ce: ‘Cewa na yi: ‘AL-HAMDU LIL LAAHI, HAMDAN KASIRAN TAYYIBAN
MUBAARAKAN FIH, MUBAARAKAN ALAIHI, KAMAA YUHIBBU RABBUNAA WA YARDAA’. Sai
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: ‘Na rantse da wanda
raina ke hannunsa! Tabbas! Mala’iku fiye da talatin ne suka yi tsere da juna:
Wanene daga cikinsu zai ɗauke
ta zuwa sama!’ (Sunan An-Nasaa’iy: 939. Kuma At-Tirmiziy ya hassana shi. Haka
ma Al-Albaaniy a cikin Sahih An-Nasaa’iy da Sahih Abi-Daawud da Sahih
At-Tirmiziy).
Daga waɗannan riwayoyin biyu za a iya fahimtar abubuwa
kamar haka:
(i) Rifaa’ah Bn Raafi’ (Radiyal Laahu Anhu)
maruwaicin hadisin, shi ne kuma ya faɗi wannan zikirin da Mala’iku sama da talatin suke
gaggawar rubutawa da ɗaukar
sa zuwa sama.
(ii) Me yiwuwa kuma Rifaa’ah ya faɗi maganar ce sakamakon atishawar da ta
same shi a lokacin ɗagowar
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), ba nufinsa zikirin ɗagowa daga ruku’u ba.
(iii) Maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) bayan an yi sallama daga sallar ita ce ta mayar da abin da Rifaa’ah
ya faɗa ta
zama ɗaya
daga cikin lafuzzan Zikiri a bayan ɗagowa daga ruku’un.
(iv) Kodayake waɗansu malamai ba su yarda da wannan haɗin ba, saboda wai akwai bambanci a cikin
dalilan zuwan hadisan guda biyu da kuma tsarin kalmominsu, amma dai Al-Haafiz
(Rahimahul Laah) ya nuna babu cin-karo a tsakaninsu, inda ya ce:
لَا تَعَارُضَ بَيْنَهُمَا ، بَلْ يُحْمَلُ عَلَى أَنَّ عُطَاسَهُ وَقَعَ عِنْدَ رَفْعِ رَأْسِ رَسُول اللَّهِ - صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
Babu cin-karo da juna a tsakanin hadisan guda
biyu. Ana dai ɗauka
cewa: Atishawarsa ta auku ne lokacin dago kan Manzon Allaah (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). (Fat-hul Baariy: 2/286)
(v) Hadisan ba su nuna cewa mamu ba ya ce SAMI’AL
LAAHU LIMAN HAMIDAHU ba. Abin da ya ke cikinsu kawai shi ne: Rifaa’ah bai
ambaci hakan ba. Wannan kuwa ba dalili ne a kan, ba a faɗin hakan ba.
Yana da kyau ɗan’uwa da ya kafa dalili da hadisin ya
tuna cewa: Su malamai da suka zo kafa hujja a kan cewa mamu ba zai ce ‘SAMI’AL
LAAHU LIMAN HAMIDAHU’ ba, ba da wannan hadisin na Rifaa’ah ne suka kafa hujja
ba. Abin da suka dogara a kansa riwayoyi ne kamar haka:
(i) Riwayar Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) daga
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:
« إِنَّمَا (جُعِلَ)
الإِمَامُ لِيُؤْتَمَّ بِهِ ، فَلاَ تَخْتَلِفُوا عَلَيْهِ ، فَإِذَا كَبَّرَ فَكَبِّرُوا ، وَإِذَا رَكَعَ فَارْكَعُوا ، وَإِذَا قَالَ سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ . فَقُولُوا اللَّهُمَّ رَبَّنَا لَكَ الْحَمْدُ . وَإِذَا سَجَدَ فَاسْجُدُوا ، وَإِذَا صَلَّى جَالِسًا فَصَلُّوا جُلُوسًا أَجْمَعُونَ ».
An sanya liman ne kawai domin a yi koyi da shi,
don haka kar ku saɓa
masa. Idan ya yi kabbara sai ku yi kabbara, idan ya yi ruku’u sai ku yi ruku’u,
idan ya ce: ‘SAMI’AL LAAHU LIMAN HAMIDAH’ sai ku ce: ‘ALLAAHUMMA RABBANAA LAKAL
HAMD’. Idan ya yi sujada sai ku yi sujada, kuma idan ya yi sallah a zaune to
sai ku yi sallah a zaune gaba-ɗayanku.
(Sahih Al-bukhaariy: 722, Sahih Muslim: 957, 962)
(ii) Riwayar Anas (Radiyal Laahu Anhu) a lokacin
da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi sallah a zaune saboda
ciwon da ya ji a bayan ya faɗi daga
kan doki ya gurje sashin jikinsa na dama, sai waɗansu daga cikin Sahabbansa suka yi sallah
a bayansa a tsaye, [sai ya yi musu ishara cewa, ku zazzauna]. Da ya yi sallama
sai ya ce:
« إِنَّمَا جُعِلَ الإِمَامُ لِيُؤْتَمَّ بِهِ ، فَإِذَا صَلَّى قَائِمًا فَصَلُّوا قِيَامًا ، فَإِذَا رَكَعَ فَارْكَعُوا ، وَإِذَا رَفَعَ فَارْفَعُوا ، وَإِذَا قَالَ سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ . فَقُولُوا رَبَّنَا وَلَكَ الْحَمْدُ . وَإِذَا صَلَّى قَائِمًا فَصَلُّوا قِيَامًا ، وَإِذَا صَلَّى جَالِسًا فَصَلُّوا جُلُوسًا أَجْمَعُونَ »
An sanya Liman ne kawai domin a riƙa koyi
da shi: To, idan yayi sallah a tsaye sai ku yi sallah a tsaye, idan ya yi ruku’u sai ku yi ruku’u, idan ya ɗago sai ku ɗago. Idan Liman ya ce: 'SAMI'AL LAAHU LI
MAN HAMIDAH' sai ku ce: 'RABBANAA WA LAKAL HAMDU' Idan ya yi sallah a tsaye sai
ku yi sallah a tsaye, idan kuma ya yi sallah a zaune, to sai ku yi sallah a zaune
gaba-ɗayanku.
(Sahih Al-Bukhaariy: 689; Sahih Muslim: 948)
Sai dai kuma waɗansu malaman irinsu Al-Imaam As-Suyuutiy
(Rahimahul Laah) sun nuna cewa, babu hujja a cikin waɗannan riwayoyin. Ta hanyoyi kusan goma ya
nuna haka a cikin: At-Tashnee’ Fee Mas’alatit Tasmee’ na cikin littafinsa:
Al-Haawiy Lil Fataawiy.
Bayan ya ambaci mabambantan mazhabobi da ra’ayoyin
malamai a kan mas’alar, sai ya shiga kawo hanyoyin da na yi ishara a baya, a
shafi: 1/50 ya ce:
(الْمَسْلَكُ الْأَوَّلُ) : أَنْ لَا حُجَّةَ لِلْخُصُومِ فِي هَذَيْنِ الْحَدِيثَيْنِ ، إِذْ لَيْسَ فِيهِمَا مَا يَدُلُّ عَلَى النَّفْيِ ، بَلْ فِيهِمَا أَنَّ قَوْلَ الْمَأْمُومِ : رَبَّنَا لَكَ الْحَمْدُ يضكُونُ عَقِبَ قَوْلِ الْإِمَامِ : سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ
Hanyar farko: A cikin waɗannan hadisan babu inda aka hana mamu ya
ce: ‘SAMI’AL LAAHU LIMAN HAMIDAHU.’ Abin da ke cikinsu kawai shi ne: Faɗin mamu cewa: ‘RABBANAA LAKAL HAMDU’ yana
biyo bayan faɗin
liman: ‘SAMI’AL LAAHU LIMAN HAMIDAHU’ ne.
وَالْوَاقِعُ فِي التَّصْوِيرِ ذَلِكَ ، لِأَنَّ الْإِمَامَ يَقُولُ التَّسْمِيعَ فِي حَالِ انْتِقَالِهِ ، وَالْمَأْمُومَ يَقُولُ التَّحْمِيدَ فِي حَالِ اعْتِدَالِهِ ، فَقَوْلُهُ يَقَعُ بَعْدَ قَوْلِ الْإِمَامِ كَمَا فِي الْحَدِيثِ
Kuma haka abin yake aukuwa a surar yadda ake yin
sallah, domin Liman yana yin Tasmee’ ne a lokacin ɗagowarsa. Shi kuma mamu yana yin Tahmeed
ne bayan ya daidaita a tsaye. Don haka, maganarsa tana aukuwa ne a bayan
maganar liman, kamar yadda ya zo a cikin hadisin.
وَنَظِيرُ ذَلِكَ قَوْلَهُ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - : (إِذَا قَالَ الْإِمَامُ : وَلَا الضَّآلِّينَ ، فَقُولُوا : آمِين)
. فَإِنَّهُ لَا يَلْزَمُ مِنْهُ أَنَّ الْإِمَامَ لَا يُؤَمِّنَ بَعْدَ قَوْلِهِ (وَلَا الضَّآلِّينَ) ، وَلَيْسَ فِيهِ تَصْرِيحٌ بِأَنَّ الْإِمَامَ يُؤَمِّنُ كَمَا أَنَّهُ لَيْسَ فِي هَذَيْنِ الْحَدِيثَيْنِ تَصْرِيحٌ بِأَنَّ الْإِمَامَ يَقُولُ : رَبَّنَا لَكَ الْحَمْدُ ، لَكِنَّهُمَا مُسْتَفَادَانِ مِنْ أَدِلَّةٍ أُخْرَى صَرِيحَةٍ
Makamancin wannan shi ne maganarsa (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa: ‘Idan Liman ya ce: ‘WALAD DAALLEEN’, sai ku
ce: ‘AMEEN’. Daga wannan bai nuna cewa: Liman ba ya yin Ameen ɗin a bayan faɗin WALAD DAALLEEN ba, kuma a cikinsa babu
magana a fili cewa Liman yana cewa AMEEN. Kamar yadda a cikin waɗannan hadisan guda biyu ma babu bayani a
fili cewa: Liman yana faɗin
‘RABBANAA LAKAL HAMDU’. Sai dai an samo hakan daga waɗansu dalilan ne na daban da suka bayyana
hakan a fili.
مِنْهَا هُنَا. مَا أَخْرَجَهُ الْبُخَارِيّ وَمُسْلِمٌ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ : أَنَّ رَسُولَ اللهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - كَانَ إِذَا قَالَ : (سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ) قاَلَ :
(اللَّهُمَّ رَبَّنَا لَكَ الْحَمْدُ)
Daga cikin irin waɗannan dalilan akwai abin da Al-Bukhaariy
da Muslim suka fitar daga Abu-Hurairah cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ya kasance idan ya ce: ‘SAMI’AL LAAHU LIMAN HAMIDAH’, sai
kuma ya ce: ‘ALLAAHUMMA RABBANAA LAKAL HAMDU’.
وَأَخْرَجَ مُسْلِمٌ عَنْ حُذَيْفَةَ : أَنَّ النَّبِيَّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - قَالَ حِينَ رَفَعَ رَأْسَهُ : (سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ ، رَبَّنَا لَكَ الْحَمْدُ)
Kuma Muslim ya fitar daga Huzaifah cewa: Annabi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa lokacin da ya ɗago kansa cewa: ‘SAMI’AL LAAHU LIMAN
HAMIDAH. RABBANAA LAKAL HAMD’.
وَأَخْرَجَ الْبُخَارِيُّ مِثْلَهُ مِنْ رِوَايَةِ ابْنِ عُمَرَ ، وَمُسْلِمٌ مِثْلَهُ مِنْ رِوَايَةِ عَبْدِ اللهِ بْنِ أَبِي أَوْفَى
Al-Bukhaariy ya fitar da irinsa daga riwayar Ibn
Umar, muslim shi ma ya fitar da irinsa daga riwayar Abdullaah Ibn Abi-Aufaa.
فَثَبَتَ بِهَذِهِ الْأَحَادِيثِ أَنَّ الْإِمَامَ يَجْمَعُ بَيْنَ التَّسْمِيعِ وَالتَّحْمِيدِ عَلَى خِلَافِ ظَاهِرِ هَذَيْنِ الْحَدِيثَيْنِ
Daga waɗannan hadisan ya tabbata kenan cewa: Liman yana haɗawa ne a tsakanin Tasmee’in da Tahmeedin,
saɓanin abin da zahirin waɗannan hadisan guda biyu ya nuna.
فَلَمْ يَصْلُحِ الاسْتِدْلَالُ بِهِمَا عَلَى أَنَّ الْإِمَامَ لَا يَجْمَعُ بَيْنَهُمَا ، وَإِذَا لَمْ يَصْلُحِ الاسْتِدْلَالُ بِهِمَا فِي حَقِّ الْإِمَامِ ، لَمْ يَصْلُحِ الاسْتِدْلَالُ بِهِمَا فِي حَقِّ الْمَأْمُومِ أَيْضًا كَمَا لَا يَخْفَى
Don haka, bai inganta ba kenan a kafa dalili da su
a kan cewa, Liman ba ya haɗawa a
tsakanin zikirorin guda biyu. Idan kuma bai inganta su zama dalili ba a kan haƙƙin
liman, to kuma ba zai inganta su zama dalili ba a kan haƙƙin mamu.
Sai kuma ya cigaba da ambaton sauran hanyoyin har
zuwa na-tara.
Wannan fassarar ita ce manyan malamai muhaƙƙiƙai
suka yarda kuma suka yi bayaninta irin su: Al-Haafiz a cikin Fat-hul Baariy:
2/143, da Al-Khattaabiy a cikin Ma’aalimus Sunan: 1/210 da An-Nawawiy a cikin
Al-Majmuu’: 3/420, kamar yadda As-Shaikh Al-Mujaddid Al-Albaaniy ya ambato daga
gare su a cikin Aslu Sifatis Salaah: 2/677-679.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.