Ina Biyawa Kaina Bukata Dalilin Mijina Baya Gamsar Dani

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum Malam ni na kasance inada aure to amma matsalar danake fuskanta itace mijina baya iya biyamin buqata hakan bayayimin dadi amma nake hurewa to hardai hakurina yagaza idan yabiya bukatarsa ya tashi nikuma sainayi kokarin biyawa kaina bukata to nadauki tsawon lokaci ina'aikata haka 😭 gashi kuma nakasa daina idan nadaina saina kuma cigaba wallahi abin yadameni narasa yandazanyi. Yanzu haka kwatakwata sha'awata ta ɗauke kome mijina zaiyidani banajin komai amatsayina namace inacikin tashin hankali wllh. Ga infection yasani agaba kulum inafama da fitar farin ruwa ga bushewa ahalin yanzu bana fahimtar jindadin mu'amala ta auratayya  Inabukatar shawara dan Allah

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikis Salaam:- Toh Shawara anan shine Ki ji tsoron Allah, Ki Ji Tsoron haɗuwa da Azabar Ubangijin ki, Ki Tuna Cewa akwai Ranar da za a Ƙwantar da ke, daga ke sai Ayyukan ki, ki Sani Cewa Ki Saɓawa Allah na Awa 1 tak Azabar Shekara 1000 ne Allah zai miki, Kiyi Tunanin Cewa Azabar da ke Cikin Qabarin Ki Shin Sha'awar ki na Minti 10 zai iya Ɗaukar sa?  Kiyi Tunanin Cewa Azabar da Allah zai miki ta dalilin wannan jin Sha'awar ki na Minti 10 zai iya Ɗaukar sa? Shakka babu Wannan Abunda kike aikatawa yana daga Cikin Saɓon Allah mafi girma, kiyi tunanin cewa shin idan kina Cikin aikata Hakan sai Allah Ya ɗauki Rayuwar ki, me za ki gayawa Ubangijin ki daga Cikin Qabarin ki har zuwa Ranar Alkiyama?  Shin kina Cikin yin haka Sai ga Yaran ki Ko Mijin ki Shin me za ki ce musu kike yi??

    Ƴar Uwa ki Ji Tsoron Allah Wannan Shine Shawarar, duk wani Abunda za ki yi Matukar ba ki saka tsoron Allah a Cikin Zuciyar ki ba, ba saka Cewa Lallai Abunda kike yin nan Azaba ce Allah yake yiwa duk mai yi ba, ba ki tuna cewa Lallai za ki mutu Allah ya je ya tambaye ki ba, ba ki tuna cewa Lallai idan kin mutu me zaki tarar a Cikin Qabarin ki ba, toh Shakka babu ba za ki taɓa ɗena Abunda kike yi ba,  amma idan kin saka Tsoron Allah a Cikin Ranki, kina tuna makomar ki, dole ne ki koma ga Allah wajen dena wannan Saɓon Allahn, amma idan ba ki tuna komai ke kawai damuwar ki Sha'awar ki ta biya, toh ki sani Cewa Za ki faɗa Cikin Ukubar Allah a Ranar Alkiyama, ke ba za ki so ace a Ranar Alkiyama Hannayen ki ko kuma kin tashi da Ciki ba,  duk mai Aikata irin wannan a Ranar Alkiyama Hannayen sa suna Yin CIKI na Azaba don haka kiyi Gaggawan Tuba zuwa ga Ubangijin ki, ki yawaita Istigifari da Ayyukan Alkhairi Allah zai yafe miki.

    Shawara na Karshe, Infection ɗin da kika ga yake yawan miki kina Fitsari ko zubar Fitsari, ki Sani Cewa Wannan Biyawa Kanki Bukatar Shine ya jawo Miki Wannan abun, kin ga Kenan ke da kanki kin jawo kanki Ciwo, sannan nan gaba bayan Lafiyar ki da hakan zai haifar miki, toh ki sani Cewa Sha'awar na kin ma, nan gaba za ki nemi sa ki rasa.

     Kin ga ke da kanki za ki kashe kanki Matukar kin cigaba da yin hakan, Lafiyar ki zai taɓu yanzu ma kin fara ganin haka, sannan Sha'awar ki ma zai dena za ki dawo tamkar ba ki jin komai game da Sha'awar koda ke zakiyi hakan da kanki ba za ki ji komai ba ki biyawa kanki bukatar babu Abunda za ki ji, kin ga kin gama da kanki Kenan. Duk Abunda aka ce muku Allah ya haramta shi ai Ubangiji yafi mu sanin meyasa yayi hakan, amma sai mu rufe idon mu, mu aikata daga baya abun ya zo ya taɓa Lafiyar mu, mu zo muna zare ido.

    Meyasa a Lokacin da ke ba ki gamsuwa da Mijin ki ai sai kiyi masa bayani Cewa ke fa Ƙwata-ƙwata ba ki jin komai, idan yana da Adalci da tausayi a Kullum ko da Shi ya gama biyan bukatar sa, sai ya jira ki kema sai kin biya naki bukatar haka zaman Aure yake, amma bawai ɓangare ɗaya ya gamsu ɗayan bai gamsu ba kuma ɗayan ya bar shi, akwai cutarwa ga hakan, in ma kin gaya masa ya Ƙi ai sai ki bi Hanyoyin da Addinin ki ya ce a bi, ki nemi Waliyyan ku  ki gaya musu, a kira sa ya gyara in ko bana gyara bane, toh akan ki Saɓawa Allah gara kun Rabu ya sake ki, ki je ki Auri wanda zai iya gamsar da ke Kamar Yadda kike so. Toh amma ba kiyi hakan ba wata kila ke kawai idan ba ki ji kin gamsu ba sai kiyi Abunda kike yi, toh saɓon Allah ne Wannan kuma akwai Azaba mai tsanani ga musu yin haka.

    Sannan Maza kuji tsoron Allah, ba zai yiwu Ace ka Auro Mace ka ajiye ta kai Kullum sai dai bukatar ka ta biya amma kai ba ka san Cewa nata bukatar ya biya ko bai biya ba, kamata yayi idan ka biya Bukatarka ka gama, ka tambaye ta shin ta gamsu?  Idan tace A'a kayi mata Adalci ka ga ka gamsar da ita kamar Yadda itama tayi ma, amma Kuskure ne kai kawai ka son kanka baka son ta, hakan yana yiwa Mata illa sosai zai iya haifarwa Mace ta je tayi Zina, sannan zai haifar ma da irin wannan Kamar Yadda yanzu take yi, don haka ba Adalci bane ace kai ka ji daɗin ka, ka biya Bukatar ka, amma ita ko oho bai kamata ba, ba ka ma damu da cewa ta gamsu ko bata gamsu ba, kai tunda naka bukatar ya biya Shikenan ita ko oho, ba Adalci bane hakan.

    Abunda yakamata shine idan ka gama biyan bukatar ka, itama ka jira ta, ta gamsu Wannan shine Adalci kuma zaka fi karɓuwa a wajen ta. Idan bata gamsu ba ka sake tambayar ta?  Sai tace Eh, Wannan shine zaki samun natsuwa matar ka ta Ƙame kanta, amma idan ka ce A'a toh zata rika Zina da Wannan abu. Allah ya tsare.

    Don Haka ku ji tsoron Allah ku dena yi musu haka. Allah ya Shirya. Ki ji tsoron Allah daga yau ki ɗena Wannan shine Shawarar.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.