Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokacin Sallar Mace A Gida

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuhu. Malam tambayata ita ce: Idan aka kira sallah, shin mu mata wai bai hallata ba mu yi sallah sai liman ya idar za mu yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Da zarar mukutarin lokacin sallah ya shiga, mace za ta iya yin sallarta ba sai ta jira har sai masallaci sun idar sannan ta yi tata ba, saboda sallar mace sallah ce mustaqilla (mai cin gashin kanta) kamar yadda sallar liman da mamu take mustaqilla. Kawai abin da mace ya kamata ta kiyaye shi ne ta tabbatar lokacin sallah ya shiga kafin ta yi tata, ko liman ya idar ko bai idar ba.

Amma idan mace a gida ba ta iya gane cewa lokacin sallah ya shiga, to a nan ya fi kamata ta jira har sai ta ji liman ya idar, sannan ta yi tata.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments