Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'ar Karya Sihiri

TAMBAYA (05)

Assalam malam DANALLAH ataimaka min da addu’ar karya sihiri. Please it’s urgent Allah yasaka da alkhair

AMSA

Waalaikumussalam. Warahmatullahi. Wabarakatuhum.

Ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari (5819) an rawaito cewar Labid Bin al'asam Alyahudi yayi amfanida gashin kan Annabi SAW yayi masa sihiri wanda har Ma'aiki SAW yakanyi kokwanto a cikin gudanar da al'amuransa na yau da kullum. Hakama Muslim ya fitardashi, hadisi mai lambata 2325

Sai Allah SWT ya nunawa Annabi SAW rijiyar da aka binne sihirin a cikin mafarkinsa. Akaje aka tararda ruwan rijiyar ya sauya kala kamar lalle saboda tasiri da dafin sihirin

Silar hakanne Allah SWT ya saukar da "Mu'awwidathayn" wato Surorin neman kariya daga sharrin mutum da aljan (Falaqi Surah ta 113 da Nasi Surah ta 114)

Annabi SAW ya warke sannan kuma ya koyarda sahabbai cewar su dinga karanta wadannan surori domin neman tsari daga sihiri. Wanda ana son mutum ya dinga karantasu da safe, yammaci da kuma lokacin kwanciya bacci

Anfi son a karanta kowacce Surah sau uku-uku a lokacin kwanciya bacci da karin Suratul Ikhlas itama sau 3 sai a tofe ko'ina a jiki (inda ya sawwaqa)

Idan aka karantawa wanda akayiwa sihirin da kyakkyawar niyya ko kuma shi da kansa ya karanta to in sha Allahu za a samu waraka

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato, Usmannoor_Assalafy

https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments