Ticker

6/recent/ticker-posts

Bacci Ya Rinjaye Ni, Na Rasa Sallar Asuba, Ya Zan Rama Ta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh malam tambaya ta anan itace nine banyi sallar asuba ba saboda nayi barci kuma ban farka ba har sai da rana ta fito, yaya zan rama wannan sallar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Na'am ɗan'uwa sallah ibadah ce mai muhimmanci wanda itace na biyu  daga cikin ginshikan musulunci, kuma duk wanda yabar sallah yana mai kore wajabcin ta to yayi riddah ya fita musulunci, Allah ta'ala yana cewa:

وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَارْكَعُوا مَعَ الرَّاكِعِينَ

Ma'ana  "Kuma ku tsayar da sallah kuma ku bãyar da zakkah kuma ku yi rukũ'i tãre da mãsu yin rukũ'i"   (Baqarah)

Sannan kuma lallai sallah tana da lokutan ta keɓantattu wanda duk wanda bai sallaci wannan sallar akan lokacin ta ba, matukar ba yana da wani uzuri na shari'a ba to hakika ya aikata abin da Allah ta'ala baiyi umarni da'a aikata ba, domin kuwa lallai Allah ta'ala yana cewa:

ۚإِنَّ الصَّلَاةَ كَانَتْ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَّوْقُوتًا

Ma'ana  "Lallai ne sallah tã kasance a kan mũminai, farilla mai kayyadaddun lõkuta"  (Nisaa'ey)

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce" An dauke Alqalami akan mutane guda uku:

1. Yaro har sai ya kai shekarun balaga.

2. Mahaukaci har sai ya samu lafiya.

3. Mai barci har sai ya farka.

(Tirmidhiy Abu-Dawud da wasun su)

Ɗan'uwa da wannan hadisin zamu kafa hujja sai muce maka idan barci ya rinjaye ka har ka rasa sallah ba ma asuba kadai ba koma wacce sallah ce, to anan baka da wani abin tuhuma a wajen Allah, amma fa kasani matukar wannan dabi'ar ka ce bakatashi kayi sallah sai kaga dama saboda yawaita barci da kake yi to anan kuwa sai dai muce (Innaa Lillaahi Wa`innaa Ilayhi Raaji'on) domin wallahi fitina ce take tunkarar mai irin wannan dabi'ar wanda kuma idan ta riske shi ya shiga uku, Allah ta'ala ya tsare mu, lallai masu irin wannan halayyar suyi kokari suji tsoron Allah ta'ala tun kafin yayi fushi dasu, (Allah ta'ala ya shiryar damu)

Ɗan'uwa ana rama sallah ne a lokacin da mutum yasan ya rasa ta, ta sanadiyyar mantuwa ko kuma barci, wato idan mutum ya manta baiyi sallah ba ko kuma yayi barci baiyi sallah ba, to wannan sallar ana rama ta ne domin kuwa ya tabbata acikin sahih muslim hadisi mai lamba 680 hadisin Sa'eed ɗan Musayyib ya tabbatar da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya rama wata asuba da shi da sahabban sa alhali sun rasa wannan sallar a sanadiyyar barci da sukayi, duba cikin MUWADDA MAALIK acikin Kitabus-Salat shafi na 27 babi na 6 hadisi na 25. Lallai duk wanda yayi barci baiyi sallah ba ko kuma ya manta ta to zai rama ta ne a lokacin daya tashi daga barci ko kuma ya tuna cewa baiyi ba,  domin kuwa hadisi ya tabbata daga Abi-Qatadah ya ce na ambaci barci cewa (ya rinjaye ni banyi sallah ba) sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce "Lallai babu asara ga wanda yayi barci (baiyi sallah ba) kaɗai asara tana tabbata ne ga wanda (yabar sallah) alhali yana a farke, idan ɗayanku ya manta baiyi sallah ba ko kuma yayi barci to ya sallaci wannan sallar a lokacin da ya tuna ta"   (Tirmidhiy ne ya ruwaito hadisi mai lamba 149)...

Imam Tirmidhiy rahimahullah ya ce  "Hakika an samu saɓanin malamai akan mutum wanda yayi barci alhali baiyi sallah ba ko kuma ya manta ta baiyi ba, to idan ya farka daga barcin sa, ko kuma ya tuna ta alhali ba lokacin sallah bane (yana nufin ya farka ko kuma ya tuna a lokacin da manzon Allah yayi hani da ayi sallah a wannan lokacin) kamar lokacin da rana take fitowa ko kuma take faduwa, Imam Tirmidhiy ya ce wasu daga sashin malamai sukace  "kawai ya sallaci wannan sallar a lokacin da ya farka daga barci, ko kuma ya tuna koda kuwa ace a lokacin ne rana take faduwa ko kuma take fitowa, wannan shine abin da waɗannan malamai guda huɗu suke akai shine qaulin Imam Ahmad da Is'haaq da Shafi'ey da Imam Maalik. wasu kuma sukace  "Matukar ya tuna ta ne ko kuma ya farka a lokacin da rana take kokarin fitowar ko kuma take kokarin faduwa to ba zaiyi wannan sallar a wannan lokacin ba, dole sai dai ya jira bayan ta fito ta daukaka ko kuma ta kammala faduwa"  Amma dai zancen su Imam Maalik shi muke akai in shaa Allah.

Don haka ɗan'uwa a lokacin dakatashi ko kuma katuna cewa baka sallaci wata sallah ba to a lokacin zaka sallace ta in shaa Allah, a duba FIQHUL-MUYASSIR shafi na 61 Allah yasa mudace.

WALLAHU A'ALAM

Hussaini Haruna Ibn Taimiyyah Abu-Nabeelah Kuriga

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅��𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments