Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sallar Qasaru

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh Malam nice nayi tafiya hutu wani garin amma xan dade shin malam xan riqa yin qasaru neh ko cikakkiyar sallah xan nayi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh 'yar uwa dukkanin wanda ya nufaci zaiyi tafiya bai rigaya ya kuduce ga iya kwanakin da zaiyi ba acan bayan zuwan sa, to zaici gaba da yin kasaru tsawon dadewar da yayi yana zama acan komin dadewar sa kuwa, Al-Imamu Ibnul-Munzir Allah ya masa rahama ya ce

"أجمع أهل العلم أن للمسافر أن يقصر ما لم يجمع إقامة, وإن أتي عليه سنوان"

Ma'ana "Masana (malamai) kansu ya hadu cewa lallai matafiyi zaita yin kasaru madamar bai zama dan gari ba, koda kuwa ace shekaru zasu riske shi ne a wajen" (Fiqhul-Muyassar Na Sa'ad Yusuf Abu-Aziz shafi na 134)

Don haka zaki cigaba da kasaru in shaa Allah gwagwadon kwanakin da kikayi wa kanki fatan zakiyi, koda kuwa kwana nawa ne zakiyi, amma idan kwanakin ki suka kare kuma baki dawo ba to zaki cika sallah in shaa Allah, amma idan baki kayyade kwana nawa zakiyi ba to zaki cigaba da yin kasaru tsawon zamanki a wajen madamar ba kin koma can da zama bane, amma dai kiji a ranki cewa baki saba wa Allah ba ki samu yikini cewa kina akan dai dai kina akan koyi da shiriyar Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, amma idan kokonto ya shigo acikin zuciyar ki to zaki cigaba da cika sallar ki in shaa Allah domin ba'a gabatar da ibadah da shakka anaso a samu yakini ne acikin bauta wa Allah tsarkakakken sarki, Allah ne mafi sani ku duba (Al-mughniy na Ibn Qudamah juz'i na 2 shafi na 134-145 haka cikin Majmoo'ul-Fataawa na BinBaz wato Fatawas-Salah shafi na 458)

WALLAHU A'ALAM

Ustaz Hussaini Haruna Kuriga

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments