Ticker

6/recent/ticker-posts

A Ina Mutum Zai Sanya Hannunsa Bayan Ya Ɗago Daga Ruku'u?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam don Allah tambaya ta anan itace, a ina mutum zai sanya hannun sa bayan ya ɗago daga ruku'u acikin sallah, shin zai sanya su akan kirji ne ko kuma zai barsu a kasa ne?  Allah ya bada ikon amsawa

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Na'am 'yar uwa abin da ya tabbata a Sunnah shine Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance idan ya ɗago daga ruku'u yana sanya hannuwan sa ne akan 'kirjin sa kamar yanda yake ɗora hannun daaman sa akan hagun sa akan  'kirjin sa a lõkacin da yake tsaye, to haka bayan ya   ɗago daga ruku'u yake ɗora hannun daman sa akan hagun sa akan kirjin sa, kuma lallai sallar mutum zatafi kamala ne idan yayi koyi da sallar Annabi , amma wanda ya kasance shi idan ya ɗago daga ruku'u yana sauke hannun sa ne a   'kasa to sallar shi tayi in shaa Allah sai dai bata cika cikakkiya ba, wanda ya ɗora hannun daman sa akan hagun sa akan 'kirjin sa to tabbas shi zaifi samun lada akan wancan, don haka muyi koyi da Annabi domin mu samu babban rabo, Allah yasa mudace,  Duba acikin littafin Sheikh Abdul'ziz Binbaz Rahimahullah mai suna ثلث رساءل في الصلاة  acikin littafin tambayoyi ne guda uku akan sallah, to a karkashin tambaya ta uku mai taken  أين يضع المصلي يديه بعد الرفع من الركوع juz'i na 1/20 a farko farkon shafin malam yayi cikakken bayani  kuma wannan siffar sallar ya shafi maza da mata, Allah yasa mudace.

WALLAHU A'ALAM

Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments