Hukuncin Amarya Da Ango Da Basa Sallah A Daren Amarci

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuh malam Tambaya nake da ita, shin ya halatta amarya taqiyin sallah a ranar da aka daura mata aure saboda yawan aikace-aikace da rashin lokaci, ko kuma a daren amarci sai nakiyin sallar asuba, shin hakan ya halatta?  Malamai inaso aja ma amare kunne akan hakan domin gaskiya mata da yawa basayin sallah a daren amarci saboda wani dalili na daban, Allah ya saka maku da Alkhairi.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumussalam warahmatullah wabarakatuh.

    Magana ta gaskiya itace wajibi ne a gareku Amarya da Ango su sallaci sallolin su na farillah da Allah ya wajabta ma musulmai yin waɗannan salloli.

    An tambayi commitee na malamai masu bada fatawa na kasar saudiyya cewa "Yaya hukucin yin sallah ga mace a daren amarci?

    Sai suka Amsa da cewa " Ya wajaba a gareta ta sallaci sallolin ta na farillah saboda babu wani sassauci akan barinta wai saboda daren amarci, sai dai idan da wani dalili da zai hanata sallah kamar tana a halin haila (jinin dabi'a) ko kuma jinin haihuwa"

    Domin neman karin bayani duba acikin littafin (LAJNATUD-DAA'IMAH 7/343)

    Wajibi ne Amarya da Ango ku kasance kun sallaci sallolin ku a ranar da aka daura maku aure, kuma ku nisanci saɓon Allah maɗaukakin sarki, ku kiyaye daga dukkan wani aiki da zai kai ku zuwa ga saɓa ma Allah, lallai babu wani dalili na daban wanda shari'a batayi magana akansa ba da zai hana mace yin sallah, matukar ba waɗannan da aka lissafa ba, kai kuwa Ango dolene baka da wani dalili Don haka dukkan wanda ya nisanci sallah to sheɗan yayi galaba akansa, irin waɗannan ma'auratan sai ayi masu nasiha, musamman iyayenmu sai suyi kokarin kwaɗaitar dasu dangane da gyara tsakanin bawa da mahaliccin sa.

    'Yar uwata kiji tsoron Allah maɗaukakin sarki ki sallaci sallolin ki, kaima Ango kaji tsoron Allah maɗaukakin sarki domin kuwa Allah yayi tanadi na azaba ga wanda yabar sallah da gangan, Allah maɗaukakin sarki ya shiryar damu, Allah yasa mudace

    Hussaini Haruna Ibn Taimiyyah Kuriga

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.