𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam dan Allah ina so a min
bayani ne a kan raka'atainil fajir. Da wani lokaci ake yin ta. Ana ba da sallar
Asuba ce ko yaya? Ina son ƙarin
bayani sosai malam. Mu wuni lafiya, na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam. Raka'atal Fajri sallah ce mai
raka'o'i guda biyu da ake yi bayan Alfijir ya keto, wato yayin da lokacin
sallar Asubahi ya shiga.
Raka'atal Fajri Sunnah ce ba farilla ba. Annabi ﷺ ya faɗi falalarta a hadisin Nana A'isha Allah ya
ƙara mata yarda, wanda
Imamu Muslim ya ruwaito, a hadisi mai lamba 725, inda Annabi ﷺ yake cewa:
ركعتا الفجر خير من الدنيا وما فيها.
MA'ANA:
Raka'o'i biyu na sallar Alfijir sun fi duniya da
abin da ke cikinta.
Sannan kuma ba a yin Raka'atal Fajri sai bayan
ketowar Alfijir, kafin a yi sallar Asubahi, kuma sallah ce da ake taƙaita karatu a cikinta, wato Annabi ﷺ bai yin dogon karatu a cikinta, yana taƙaitawa ne. Haka kuma idan mutum ya saba
yin Raka'atal Fajri kullum, sai wata rana barci ya rinjeye shi ba laifi ya rama
ta bayan ya idar da sallar Asubahi ko da gari ya yi haske, Saboda an yi hakan a
gaban Manzon Allah ﷺ bai
hana ba.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.