1) Kurin ɗiya na ubansu ne, ba
su ba,
Ka zama gamji ina ba dai sara ba.
2) Mafara a bincinka
ina wai tamka tai?
Ni ban ga wanda yaz
zam tamka tai ba.
3) Ci da shammu duk
Allah yats tsara,
Ya rataya wa giwa ba dai tsako ba.
4) Baba abinka duk ka
ce na iyalinka,
Wurin kula da su, ba ka yo ƙwauro ba.
5) Idan ya tashi
kyauta tamkar iska ne,
Zama ka ce bai san
zafin samu ba.
6) Ya tsare haƙƙi na kulluhin, duka
iyalinsa,
Tamkar ka ce da shi,
wani jigo babba.
7) Ya kula da
mas'uliyyar, duka 'ya'ya nai
Ta ba su illimi da ɗai bai sarayar ba.
8) Ina gwanin wani,
ni ko in ce ga nawa,
Shi at turke gare mu, ja gaba dai baba.
9) Ina tuna baiwa
iri-iri da yay yi a kaina,
Na kyautuna da ba zan iya ƙirga ba.
10) Magana ta Ɗaha Musɗafa yag gasganta,
Na wanda duk yake saki, ba zai taɓe ba.
11) Baba yana saki ga
dukkanin iyalinsa,
Don haka ne da ɗai, ba zai rasa samu ba.
12) Baba tun gaban ya
zam police, ɗan sanda,
Ya yi zama malamin aji, teacher babba.
13) Daga nan ya zo ya
samu promotion nic ce ma,
Muna gida kawai muka
ji albishiri babba.
14) Ya fito a
matsayin ASPin 'yansanda,
Ya zama S O a zamanin Haji Yari baba.
15) Idan kana so ka
ga Gwamna, sai da sanin sa,
Yaz zama gimshiƙi guda mai tunkuɗe gaba.
16) Shi kaɗai tilo yake ƙwallin ƙwal-ƙwal-ƙwal,
Ubangiji ya lulluɓe sa, bai bar shi da
ragga ba.
17) Ubangiji ina daɗa roƙo wannan bawanka,
Ka kankare saga'ir da kaba'ir duka Rabba.
18) Idan aka tambaye
ka mine ne jigon waƙata,
Yabo da jinjina ne niy yo, ku ji don baba.
19) Samir Aminu shi
ne marubucin da ya tsara ta,
Rana ta 6 ga watan 6 2023 ba raibi ba.
20) Yabon bajimi dole
ne, ga wanda ya san kunya,
Allah shi ne karimu zul arshin nan babba.
Name: Samir Aminu Musa
Email: samiraminumusa95@gmail.com
Phone Number: 08109474995
Maa shaa Allah, Allah yaqara basira
ReplyDelete