This article is published in Taguwa Journal of Humanities, Vol. 2 No. 1, 2009, Faculty of Humanities, Umaru Musa Yar’adua University, Katsina, page 141-165.
Ƙaura da Shigowar Fulani Ƙasar Hausa da Tasirin Al’adunsu a Kan
Wanzanci
English Rendition as “Migration and Settlement of Fulani Communities in
Hausa Land and the Influence of their Culture on Hausa Barbers Tradition”
Bashir Aliyu Safana Sallau
Department of Nigerian Languages
Umaru Musa Yar’adua University
Katsina – Nigeria
ABSTRACT
Since the 1960s reseachers have devoted their time in collecting relevant data in respect of migration and settlement of various communities in West African sub-region and the socio-economic and political consequences that resulted in the new settler communities. At present scholars have devoted serious interest on conducting reseaches on Hausa culture which has now been considered as an academic discipline in our universities. This reseach investigate Hausa culture. Hence, this article is to examines migration and settlement of Fulani communities in Hausaland and their attendant influence on the Hausa culture and tradition of Hausa Barbing Tradition (Wanzanci). For long the salient norms and values of our culture have been influenced in one way or the other by foreign cultures, but little has been done in highlighting this developments.The article highlights the impact of the migrant Fulani on barbing tradition in Hausaland.
1. 0 Gabatarwa
Tun cikin shekarun 1960 zuwa wannan lokaci masana da
manazarta da ɗalibai masu binciken tarihi suke ta kai-kawon nazari kan ƙaura da
shigowar baƙi da kuma sakamakon da wannan ƙaura ta haifar ga al’ummomi daban-daban
da ke a faɗin Afrika ta Yamma.
Dangane
da haka ne wannan takarda ta yi ƙoƙarin kawo bayanai akan ƙaura da Fulani suka yi
daga ƙasashensu na asali suka shigo ƙasar Hausa. An kuma kawo dalilansu na zaɓar
ƙasar a matsayin wurin da suka ga ya dace su zauna ko dai don cirani ko kuwa
don su yi zama na dindindin. Haka kuma an duba ire-iren abubuwan da wannan ƙaura
ta haifar a tsakaninsu da Hausawa dangane da yadda ake aiwatar da sana’ar
wanzanci. A taƙaice an duba irin tasirin da al’adun Fulani suka yi a kan
al’adun wanzancin Hausawa ta fuskar yadda ake gudanar da ayyukan wanzanci.
1. 1
Farfajiyar Ƙasar Hausa Jiya da Yau
Yana da matuƙar mahimmanci kafin mu faɗa cikin kogin
wannan nazari mu ɗan yi waiwaye domin sanin wurin da ƙasar Hausa take a jiya da
kuma a yau. Ƙasar Hausa ta asali tana a Afrika ta Yamma ne, a farfajiyar da ke
tsakanin hamadar Sahara da dazuzzukan da suka doshi gaɓar tekun Atlantika daga
kudu. Kuma ana kiran ƙasar da sunan Sudan ta Yamma, watau tsakanin Tafkin Cadi
da gwiwar Kogin Kwara a can Yamma (Alhassan, 1981:1).
A wata faɗar kuma an bayyana cewa Ƙasar Hausa tana shimfiɗe
ne a can Arewacin Nijeriya da kuma kudancin Jamhuriyar Nijar a cikin Afrika ta
Yamma. Daga Gabas ta yi iyaka da ƙasashen Borno. Daga Yamma ta yi iyaka da ƙasashen
Dahomey a gaɓar Kogin Kwara. Daga Arewa ta yi iyaka da ƙasar Adar a cikin
Jamhuriyar Nijar. Daga wajen Kudu kuma ta yi iyaka da ƙabilun Gwari da kuma ƙabilun
kudancin Zariya da na Kudancin Bauci (
Ibrahim, 1982:1).
A wannan zamani a iya cewa Ƙasar Hausa yanki ne wanda ya
mamaye dukkan Jihar Katsina da Jihar Kano da Arewacin Jihar Kaduna da wasu ɓangarori
na Jihohin Bauci da Gwambe da Neja da kuma kudancin Jamhuriyar Nijar. Idan aka
tayar da saiti daga Arewa zuwa Kudu ƙasar Hausa ta fara daga Azbin har ya zuwa
kusurwar Arewa maso gabas da tsaunukan Jos. Daga nan sai ta shararo ta yi Yamma
har zuwa wurin da Kogin Kaduna ya yi wani babban doro. Daga nan kuma sai ta
malala ta yi arewa maso yamma ta yi mahaɗa da ƙaton rafi na kogin Kabi. Daga
wannan wuri sai ta karkata ta nufi arewa maso gabas har Azbin (Birnin-Tudu, 2002:11-12).
Ƙasar Hausa wadda tana shimfiɗe a shiyyar Sudan ta
Tsakiya, a tsari na gargajiya a iya cewa ta haɗa da ƙasashen sarakunan Katsina
da Kano da Daura da Zazzau ( idan aka ɗebe kudancin Zazzau) da Kabin Argungu da
Gwandu da Gumel da Haɗejiya da Ƙwanni da Maraɗi da Tassawa.
Idan muka juya kan su wane ne Hausawa za a ga cewa masana
da manazarta daban-daban sun kawo ra’ayoyinsu kan waɗanda suke ganin cewa su ne
Hausawa. A ra’ayin wani masani ya bayyana cewa Hausawa su ne mutanen da ke
zaune a ƙasar Hausa tun tuni, kuma suna magana da harshen Hausa a matsayin
harshen uwa ( Ibrahim, 1982:1)
Wani masanin kuma na ganin cewa, Hausawa sun haɗa da mutanen nan waɗanda saboda
ƙaura da magabatansu suka yi daga ƙasar Hausa zuwa wasu sassa da ke maƙwabtaka
ta kusa ko ta nesa da ƙasar Hausa, ko da kuwa ba sa magana da harshen Hausa ko
yin al’adun Hausawa sun ɗauka su Hausawa ne. Misali, Abakwariga da ke zaune a
Jihar Taraba ta Nijeriya da kuma wasu da ke ikirarin cewa su Hausawa ne waɗanda
ke zaune a ƙasashen Cote de Ɓoire da Burkina Faso da Mali ( Adamu, 1983:3).
Akwai kuma waɗanda saboda da ƙaura da magabatansu suka yi
zuwa ƙasar Hausa sun manta da harshensu da adabinsu da al’adunsu na asali sun ɗauki
na Hausawa. A taƙaice sun koma Hausawa a harshe da adabi da al’ada. Misalin
ire-iren waɗannan mutane sun haɗa da Barebari da Kanbarin Barebari da Barebarin
Katsina da Buzaye da wasu Fulani (Sallau, 2000:71).
Wani masanin kuma ya bayyana cewa Hausawa dai su ne
mutane waɗanda harshensu shi ne Hausa sannan dukkan al’adunsu da ta’addunsu na
Hausa. Haka kuma addinin Musulunci ya yi cikakken tasiri a kansu ( Magaji, 1986:3).
1. 2 Yanaye – Yanayen Ƙasar Hausa
Mafi yawancin sassan ƙasar Hausa yana shimfiɗe ne kuma
yana da yawan sarari, amma duk da haka akwai tsaunuka da tuddai a wasu wurare
kamar Dutsin Dala da na Goron – Dutse a Kano da Dutsin Dutsin-ma a jihar
Katsina da Dutsin Kwatarkwashi a jihar Zamafara da Duwatsun Kufena a Zariya da
da sauransu.
Akwai ‘yan dazuzzuka waɗanda suka haɗa da dajin Rugu
wanda ya ratsa jihohin Katsina da Zamfara da dajin Falgore wanda ya ratsa jihar
Kano da wani ɓangare na lardin Zazzau a jihar Kaduna. Yanayin dajin da ke ƙasar
Hausa iri biyu ne, da wanda ake kira “Sahel”, watau irin dajin da ake samu a
arewa, da kuma dajin “Saɓanna”wanda ake samu a kudancin ƙasar. Akwai ƙarancin itatuwa a dajin
“Sahel” kuma mafi yawancinsu gajeru ne. A lokacin rani da yawa daga cikin
ganyayen da ke wannan daji kan kakkaɓe, idan kuma damina ta kusa zuwa sai su
fara tohuwa. Ciyawar da ake samu a wannan daji dabbobi kan cinye rabi su
tattake rabin, amma da an yi ruwan tohon geza duk sai ta tsiro a ko’ina. Wuraren
da wannan daji ya mamaye sun haɗa da dukkan kudancin Jamhuriyar Nijar da
arewacin ƙasar Hausa a sassan jihohin Katsina da Kano da Jigawa da Zamfara da
Sakkwato da Kabi. Daga dajin “Sahel” idan aka yi kudu kaɗan sai dajin “Saɓanna”. A wannan irin daji itatuwa sun fi tsawo da kusanci
da juna, haka kuma ana samun ganyaye da ciyayi da suke shekara cikin ɗanyantakarsu
watau kore. Ana samun yanayin irin wannan daji a kudancin jihar Katsina da
Lardin Zazzau a jihar Kaduna da Ladin Kabi da Yawuri a jihar Kabi da Kwantagora
a jihar Neja.
Duk faɗin ƙasar Hausa manyan koguna biyu ne suka ratsa ta
cikinta da kogin Rima da kogin Haɗejiya. Kogin Rima shi ne ya taso daga ƙasar
Zamfara ya malala ya yi arewa zuwa cikin Jamhuriyar Nijar, daga nan sai ya
karkata kudu ya bi ta yammacin Sakkwato ya je ya faɗa cikin kogin Kwara wanda
shi ke iyaka da ƙasar Hausa. Kogin Haɗejiya kuwa ya fara daga ƙasar Kano ya
gangara ya yi gabas, ya bi ta Jama’are a jihar Bauchi, ya bi ta Gashuwa da
Gaidam a jihar Yobe ya faɗa tabkin Cadi (Alhassan;1981:3).
Ta fuskar yanayin shekara ƙasar Hausa na da yanayi iri
biyu, lokacin damina da lokacin rani. Ana samun ruwan sama a lokacin damina
wanda ke farawa daga watan Mayu zuwa watan Satumba, kuma ruwan da ake samuba
mai yawa ne ƙwarai ba, amma duk da haka yana da albarka da biyan buƙatun manoma.
Shi kuma lokacin rani yana farawa daga watan Oktoba zuwa watan Afrilu, ya kuma
rabu biyu watau lokacin ɗari da lokacin zafi ko bazara (Adamu, 1997:13-14).
2. 1
Ma’anar Ƙaura da Ire-Iren ta
Masana da manazarta da ɗalibai daban-daban sun kawo
ra’ayoyinsu kan ma’anar kalmar ƙaura. Wani daga cikinsu ya bayyana cewa ”ƙaura
na nufin tashin mutane daga ƙauyuka ko garuruwa zuwa manyan birane, wasu na
wani ɗan lokaci (cirani), wasu kuma sun koma don su yi zama na dindindin a
wannan sabon wuri” (Osaghae, 1994:20).
Wani masanin kuma na ganin ƙaura a matsayin “ tashi daga
wata gundumar mulki zuwa wata, wadda sakamakon wannan ƙaura ke samar da wurin
zama na dindindin”(Prothero, 1981:51).
A wata fassarar kuwa ana ganin ƙaura a matsayin “mutum ko
ƙungiyar mutane masu yawa su canja wurin zamansu su koma wani wuri na daban
wanda za su yi zama na dindindin, amma ba irin canjin wurin da makiyaya ko ‘yan
ƙodago ko ‘yan cirani da makamantansu ke yi ba waɗanda ba sa yin zama na
dindindin a sabon wurin da suka koma” (Bello, 1999:1).
Ko-da-yake ƙoƙarin da waɗannan masana da manazarta da ɗalibai
da aka kawo ra’ayoyinsu kan ma’anar ƙaura, sun ɗan sha bamban kan yadda
kowanensu ke ganinta, sun gamu kan manufa ɗaya wadda ta bayyana cewa ƙaura dai
na nufin tashi daga wani wurin zama zuwa wani.
A wannan zamani an kasa ƙaura zuwa iri biyu, akwai wadda
ake yi daga wata ƙasa zuwa wata, sai kuma wadda ake yi a cikin ƙasa ɗaya. Ƙaura
daga wata ƙasa zuwa wata na da matuƙar wuya saboda dalilan nisan wuri, kuma mai
yin irin wannan ƙaura ka iya fuskantar matsaloli waɗanda suka haɗa da na
bambancin harshe da yanayin sabon wurin da za a koma. Akwai kuma bambancin
al’adu da hanyoyin samun kuɗi da halin zamantakewa. A wani lokaci kuma ana iya
fuskantar matsalar rashin karɓa mai kyau daga al’ummomin da aka yi ƙaura zuwa ƙasashensu.
Amma ita ƙaura ta cikin gida tana da matuƙar sauƙi don kuwa ba a fuskantar
matsalar nisan wuri, kuma matsalar baƙin al’adu da harshe da halin zamantakewa
da hanyoyin neman kuɗi za a same su da sauƙi a wuraren da aka koma. Wannan kuwa
ya samu ne saboda a mafi yawancin lokaci akan tarar da ‘yan uwa da abokan
arziki waɗanda suka daɗe a waɗannan wurare, kuma su ne kan karɓi sababbin zuwa,
su zama jagora a gare su wajen tafiyar da harkokinsu har su koya (Bello, 1999:9).
2. 2 Dalilan Shigowar Fulani Ƙasar Hausa
Akwai dalilai da dama waɗanda suka sa Fulani yin ƙaura
daga ƙasashensu na asali suka shigo ƙasar Hausa. Daga cikinsu akwai wadatattun
wuraren kiwo da na ba dabbobi ruwa a ko’ina cikin ƙasar Hausa. Haka kuma
kasancewar al’ummar Hausawa mutane ne masu son zaman lafiya kuma ƙasar Hausa na
da fuskar jawo baƙi saboda wadatacciyar albarkar ƙasa sun ƙara taimakawa wajen
shigowar Fulani wannan ƙasa. Wasu Fulanin kuma sun shigo ne domin yaɗa addinin
Muslunci. Bugu da ƙari kuma kasancewar al’ummar Hausawa na da ɗabi’ar zama lafiya
da kowa baƙo da ɗan gida ya ƙara taimakawa wajen shigowa da zaman wasu
al’ummomin Fulani a sassa daban-daban na ƙasar Hausa.
2. 3 Al’ummar Fulani da Rabe-Rabensu
Mazaunin Fulani na farko a Afrika ta Yamma na a yankin
Senegal, amma a yanzu ana samunsu a Chadi da Kamaru da Gambiya da Sudan da
Habasha (Abubakar, 1977:27). A wannan zamani yawan al’ummar Fulani ya fi
Miliyan shida kuma fiye da rabinsu na zaune a Arewacin Nijeriya (Johnston, 1967:20).
A lokaci mai tsawo da ya gabata al’ummar Fulani ta kasu zuwa kashi uku. Akwai
Fulani Mbororore’en1 da Fulɓe Na’i2 da Fulɓe Shi’e3.
Da farko waɗannan rabe-raben Fulani duk suna haɗe waje ɗaya a ƙarƙashin
Mbororore’en, amma saboda wasu dalilai aka samu waɗannan rabe-rabe (Abubakar, 1977:27).
Daga cikin dalilan da suka kawo rabe-raben, sun haɗa da a lokacin da suke yawon
neman wuraren kiwo, wasu kan fuskanci matsalolin da kansa dabbobinsu raguwa ko
su ƙare musamman ta hanyar cutuka ko wani bala’i. Haka kuma akwai waɗanda idan
aka samu wurin kiwo mai kyau sai wasu
su yanke hukuncin zama a wannan wuri. Ga waɗanda suka
fuskanci matsalar raguwar dabbobinsu, sai su riƙa kula da waɗanda suka ragu, kuma
sai suka riƙa haɗawa da yin wasu aikace-aikace kamar noma da kasuwanci. Wannan
dalili ne ya haifar da samuwar kashi na biyu na Fulani watau Fulɓe Na’i. Idan
yawansu ya ƙaru sai su koma ma rayuwarsu ta yawon neman wuraren kiwo masu kyau
kamar danginsu Mbororore’n. Amma ga waɗanda dabbobinsu suka ƙare duka sai su
samu wuri mai nagartattar ƙasa su riƙa yin noma da wasu sana’o’i su daina
yawace-yawacen da suka gada. Wannan shi ya haifar da samuwar kashi na uku na
Fulani watau Fulɓe Shi’e (Abubakar, 1977:28).
Bayan raguwa ko ƙarewar dabbobi ga Fulanin da suka daina
yawon neman wuraren kiwo, cuɗanya tsakaninsu da al’ummomin wuraren da suke kiwo
ya ƙara taimakawa matuƙa wajen samuwar Fulanin da kan zauna su daina
yawace-yawace ko dai na wani ɗan lokaci ko su yi zama na dindindin a waɗannan
wurare. A sakamakon shigowar addinin Musulunci a Afrika ta Yamma a cikin ƙarni
na goma sha ɗaya al’ummar Fulani ne suka fara karɓarsa (Abubakar, 1977:28). Wannan
dalili ne ya sa suka zama na gaba-gaba wajen yaɗa shi a duk faɗin Afrika ta
Yamma. Saboda kasancewar addinin Musulunci ya shafi dukkan rayuwar wanda ya karɓe
shi, wannan ya taimaka ƙwarai wajen canja rayuwar wasu Fulani waɗanda wannan
al’amari ya sanya su mayar da hankalinsu wajen koyo da koyarwa da yin
aikace-aikacen addini fiye da kiwon dabbobi da suke yi kafin su karɓi addinin. Daga
nan sai suka riƙa yawo daga wurin wannan malami zuwa wurin wancan don neman ilimin
addinin Musulunci, wannan ya sa wasunsu suka zama mashahuran malamai. Samuwar
addinin Musulunci a wajen Fulani ya ƙara taimakawa matuƙa wajen zaman wasunsu
wuri ɗaya tare da iyalansu. Wannan ne ya sa wasu suka zama alƙalai, wasu
mashawarta ga sarakunan wuraren da suke zaune, wasu kuma sai suka zama mabiya
addinin kawai ta hanyar tafiyar da harkokin rayuwarsu kamar yadda dokokin
shari’ar addinin Musulunci suka tsara. Su kuwa Mbororo’en a wannan lokaci
addinin Musulunci bai yi wani tasiri na a-zo-a-gani ba cikin rayuwarsu, don
kuwa sun fi mayar da hankalinsu kan kiwon dabbobinsu fiye da yin aikace-aikacen
addinin Musulunci (Abubakar, 1977:28).
Wannan zama da Fulani suka yi cikin al’ummomi daban-daban
da suka tarar da kuma cuɗan-in- cuɗe-ka da suke yi da juna ya ƙara danƙon
zumunci tsakaninsu. Domin kuwa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci sai da Fulani da waɗannan
al’ummomi suka fara yin musayar al’adu da kuma auratayya4. Wannan ya
ƙara taimakawa matuƙa wajen zaunar da wasu Fulani wuri ɗaya suka daina
yawace-yawace.
2. 4 Shigowar Fulani Ƙasar Hausa da Wuraren da Suka Fara
Zama
Dangane da shigowar Fulani ƙasar Hausa a haƙiƙa yana da
matuƙar wuya a ce ga takamaiman lokacin da suka fara shigowa wannan ƙasa. Amma
duk da haka manazarta ƙaura da shigowar baƙi ƙasashe sun yi kintacen cewa wata ƙungiyar
Fulani maƙaurata sun shigo ƙasar Hausa a farkon ƙarni na goma sha huɗu
(Abubakar, 1977:29). Wannan kuwa ya faru ne sakamakon ƙaura da suka yi daga
yankin Senegal zuwa gabas domin neman wuraren kiwo masu kyau. A farkon ƙarni na
goma sha shida akwai al’ummomin Fulani da daman gaske a ko’ina cikin ƙasar
Hausa. Daga ƙasar Hausa ne wasu Fulani suka yi kudu-maso-gabas har suka kai
gewayen kogin Gongola a cikin ƙarni na goma sha bakwai.
A bayanan da aka samu daga Katsina an bayyana cewa kafin
kafuwar mulkin Muhammadu Korau a Katsina cikin shekarun 1450 wasu Fulani da ake
kira Sissilɓe (Sulluɓawa)5 sun baro Futa-Toro da niyyar zuwa Masar
amma sai suka tsaya a Katsina (Nadama, 1977:170). An kuma bayyana cewa a ƙarshen
ƙarni na goma sha takwas waɗannan Fulani sun zauna da gindinsu a garuruwan
Kanwa da Ƙusa da Zandam da Bugaje da Shinkafi waɗanda dukkansu suna kusa da
Birnin Katsina (Usman, 1972:191-192).
Bayan wannan ƙungiya an sami wasu ƙungiyoyin Fulani waɗanda
suka shigo ƙasar Katsina daga Borno, sun kuwa haɗa da Yerimawa da Gallawa
(Gallanko’en) da Daɓawa da kuma Dallazawa. Dukkan waɗannan al’ummomi na Fulani
sun sauka a garuruwan da ke iyakar ƙasar Katsina ta gabas. Yerimawa sun mamaye ƙasar
Yamel, wasu daga cikinsu kuma suka yi kudu ta gabas har Ɗanbatta ta ƙasar Kano.
Su kuma Gallawa sun zauna a arewacin Yamel suka kafa garuruwan Sirika da Gallu,
wannan ne ma ya sa ake kiransu da sunan Sirikawa. Daɓawa kuwa sun zauna ne akan
iyakar da a yanzu ta raba Nijeriya da Jamhuriyar Nijar a ƙauyen Kantche. Daga
nan ne kuma wasu suka matsa gaba suka kafa ƙauyen Daɓawa wanda ke kusa da garin
Kaita, wasu kuma zuwa Kanembakashe duk a ƙasar Katsina. Su kuma Dallazawa sun
zauna a arewacin wuraren da Yerimawa suka zauna suka kafa ƙauyen Dallaje. A nan
ne Abdulmumini mahaifin Ummarun Dallaje wanda ya zama Sarkin Katsina na farko
bayan jihadi ya zauna6. Ana sa ran cewa Yerimawa sun shigo ƙasar
Katsina a cikin ƙarni na goma sha bakwai, su kuma Dallazawa a cikin kashin
farko na ƙarni na goma sha takwas (Usman, 1972:190-191).
Wasu Fulanin kuma da suka shigo ƙasar Katsina sun haɗa da
Yerobawa waɗanda daga cikinsu ne ake sa ran Malam Na’Alhaji7ya fito,
wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka aiwatar da jihadi a ƙasar Katsina. Sun
shigo wannan ƙasa a cikin ƙarni na goma sha takwas, sun sauka a Kwomi wurin da
aka riƙe Malam Na’Alhaji bayan rasuwar mahaifinsa a Makka.
Al’ummar Fulani sun fara shigowa ƙasar Kano a lokacin
mulkin Sarkin Kano Yakubu (1452-1463), kuma sun fara zama a Ɗanbatta da Rano da
Sumaila da Kazaure da dai sauran wurare da dama a cikin Kano da kewayenta. Akwai
kuma wasu Fulani da suka shigo ƙasar Kano don yin yaƙin jihadi a farkon ƙarni
na goma sha tara. Waɗannan Fulani ne suka kafa unguwanni Yola da Danbazau da
Galadanci da Daneji duk a cikin Birnin Kano (Baƙo, 1990:73).
Torankawa Fulani zuri’ar da Shehu Usman Ɗanfodiyo ya fito
daga cikinta sun sauka a Ƙwanni arewacin ƙasar Zamfara a ƙarƙashin shugabansu
Malam Musa Jokollo a cikin shekarun 1450. An bayyana cewa Torankawa sun shigo
cikin ƙasar Gobir tun lokaci mai tsawo da ya wuce. Daga baya ne wani malami
daga cikinsu mai suna Muhammadu ɗan Sa’idu ya fita shi da magoya bayansa daga ƙasar
Gobir suka zauna a Maratta cikin ƙasar Galmi.
An kuma sami zuri’ar wani Bafulatani mai suna Ali waɗanda
suka zauna a Guluba ta ƙasar Zamfara, ana yi masu laƙabi da sunan Alibawa a ƙasar
Zamfara daga sunansa. An bayyana cewa sun shigo ƙasar Zamfara ta yankin Zurmi
tun shekaru ɗari uku kafin jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo. An ce wasunsu sun
shigo ne daga Dosso suka zauna Zurmi, wasu kuma sun zo Zurmi ne a ƙarƙashin
shugabansu mai suna Isau daga Babbar-Ruga ta ƙasar Katsina (Nadama, 1977:171, 176).
Mafi yawa daga cikin Fulani Alibawa manoma ne don kuwa sun bar yawace-yawacen
neman wuraren kiwon, wannan kuwa ya faru ne sakamakon ƙarewar dabbobinsu. Zamansu
a Zurmi cikin Zamfarawa Hausawa ya sa suka manta da harshensu da al’adunsu na
Fulani suka koma Hausawa (Nadama, 1977:176).
Bayan Alibawa akwai kuma Alawa waɗanda su makiyaya ne, sun
shigo ƙasar Zamfara daga yamma. Saboda yawan dabbobinsu sun sauka a gabacin ƙasar
a gefen dajin Rugu. Daga Zamfara ne wasunsu suka yi gabas zuwa Kazaure ta ƙasar
Kano. Alawa sun zauna a Kamani da Magare da Aya duk a kan iyakar ƙasar Zamfara
da dajin Rugu.
Akwai wasu al’ummomin Fulani da aka tabbatar da zamansu a
ƙasar Zamfara tun cikin ƙarni na goma sha takwas. Daga cikinsu akwai Jallawa waɗanda
a yanzu suke zaune a Kurya Madaro da Rawayya kuma suna ikirarin sun zo daga
Mali ne. Akwai kuma Ƙasarawa da Sulluɓawa waɗanda suka shigo ƙasar Zamfara daga
ƙasar Katsina a farkon ƙarni na goma sha takwas. A yanzu Ƙasarawa suna zaune kusa
da Dutsin Masari, su kuma Sulluɓawa suna zaune a garuruwan Sado da Morai
(Nadama, 1977:176-181).
A sakamakon ƙaura da shigowar Fulani ƙasar Hausa an sami
wata al’umma wadda a yau ake kira Hausa/Fulani. Wannan kuwa ya faru ne
sakamakon cuɗanya da auratayya wadda ake yi tsakanin waɗannan al’ummomi fiye da
dukkan wasu ƙabilu da suke cikin Nijeriya da kuma na maƙwabtanta. Haka kuma
rawar da masu jihadi suka taka wadda ta haifar da Daular Usmaniyya ta ƙara
taimakawa wajen samuwar wannan al’umma ta Hausa/Fulani. Wannan cuɗanya ta
taimaka ƙwarai wajen mayar da wasu Fulani su koma Hausawa a harshe da adabi da
al’ada. A yanzu a iya cewa mafi yawancin gidajen sarautu da suke a ƙasar Hausa
masu mulkinsu asalinsu Fulani ne zuri’ar waɗanda suka amso tutar jihadi daga
wurin Shehu Usman Ɗanfodiyo. Amma daga cikin ire-irensu kaɗan ne kawai suke iya
magana da harshen Fulatanci. Bayan su, akwai wasu Fulani masu yawan gaske waɗanda
suke zaune a sassa daban-daban na ƙasar Hausa tun lokaci mai tsawo da ya wuce. Su
ma sakamakon cuɗanya da Hausawa sun koma Hausawa a harshe da adabi da al’ada. A
yanzu ire-iren waɗannan Fulani ana kiransu da sunan Fulanin gida ko Fulanin
zaure, amma daga cikinsu ana samun waɗanda suke iya magana da harshen Fulatanci
da kuma na Hausa a lokaci ɗaya.
Bayan waɗannan akwai wasu Fulanin waɗanda duk da cuɗanya da auratayya da take tsakaninsu da Hausawa ba su bar harshensu da adabinsu da al’adunsu ba. Ire-iren waɗannan Fulani suna zaune ne a wuraren da yake kusa da makiyayar dabbobi da wuraren ban ruwa a sassa daban-daban na ƙasar Hausa. Waɗannan Fulani a yanzu suna tafiyar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum a ƙarƙashin shugabanninsu waɗanda ake kira “Arɗo”. Shi Arɗo ne yake wakiltarsu a duk wasu al’amura tsakaninsu da sarakunan ƙasar Hausa. Akwai ire-iren waɗannan Fulani da yawa a sassa daban-daban na ƙasar Hausa, kuma su ne suke samar da mafi yawan shanun da ake kiyayawa a duk faɗin ƙasar Hausa. Bayan shanu suna kiwon tumaki da awaki da kaji da zabbi. Haka kuma matansu ne suke tallar nonon shanu da man shanu da ake haɗawa ana dama hura don sha ko don yin magani da dai sauransu. Bayan harshensu na Fulatanci suna magana da harshen Hausa kamar yadda suke yi da wannan harshe nasu, kuma al’adunsu sun shiga cikin na Hausawa kamar yadda al’adun Hausawa suka shiga cikin nasu. Haka kuma akwai Hausawa waɗanda sakamakon cuɗanya da Fulani suke magana da harshen Fulatanci kamar yadda suke yi da harshensu na Hausa.
3. 1 Tasirin Al’adun Fulani a Kan Wanzancin Hausawa
A lokacin da Fulani suka shigo ƙasar
Hausa sun riƙa gudanar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali da
lumana. Wannan ne ya ba su damar aiwatar da al’adunsu cikin Hausawa ba tare da
fuskantar wasu matsaloli ba. Haka su ma Hausawa da aka tarar a ƙasarsu
suna tafiyar da nasu al’adun a kan idanun Fulani. A lokacin da suke yin wasu
al’adu kamar bukin aure ko haihuwa da dai sauransu sukan gayyaci juna. Watau a
lokacin da Fulani suke yi sukan gayyaci Hausawa, haka idan Hausawa na yi sukan
gayyaci Fulanin. Wannan dangantaka ta taimaka ƙwarai wajen musayar
al’adu da fahimtar juna a tsakanin waɗannan al’ummomi. A sakamakon haka ne aka riƙa
samun nason al’adun Fulani cikin al’adun wanzancin Hausawa. Wannan al’amari ya
yi babban tasiri kan yadda Hausawa suke tafiyar da al’adun wanzanci dangane da
yadda ake gudanar da aski da gyaran fuska da cire belun-wuya da tsayar da gemu
da kaciya da tsagar kwalliya da dai sauran ayyukan wanzanci.
Yanzu za a bi diddigin ire-iren waɗannan ayyuka na wanzanci don gano nason da al’adun Fulani suka yi a kansu.
3. 1. 1 Aski da Gyaran Fuska
Ta fuskar aski da gyaran fuska al’adun Fulani sun
yi naso a kan wanzanci musamman ire-iren askin da ake wa matasan Fulani da ma
wasu Hausawa waɗanda
ke yin hulɗoɗi da Fulani wajen kiwon shanu. Akwai
nau’o’in aski iri daban-daban da ake yi wa matasan Fulani, Hausawa na kiransu
da suna ciko-a-gaba da ciko-a-baya da kuma ciko-a-gaba-da-baya. Su kuma
dattawan Fulani askin ƙwaryar molo ake yi masu, a wurin gyaran fuska ne
aka samu nason al’adunsu a kan wanzanci. Dattawan Fulani na yin irin gyaran
fuska wanda Hausawa ke kira ƙahon barewa. Haka kuma ana yi wa matan Fulani
gyaran fuska, jarirai da ƙananan yara ana yi masu zanko.
a) Gyaran Fuska Ƙahon Barewa
Wannan nau’i na gyaran fuska dattawan Fulani ne ake yi wa irinsa. Ana yin irin wannan gyaran fuska don a aske gashin da ke a wurin fuska da haɓa a lokacin da suma ba ta yi yawan da za a sake ta ba. A wannan lokaci ne sai wanda ke da buƙatar, ya je wurin wanzami don a yi masaA irin wannan gyaran fuska ana gyara gashin da ke wurin goshi a kuma aske dukkan saje tun daga wurin da ya haɗu da sumar kai har zuwa wurin gemu. Ba a aske gemu sai dai a kwakwafe shi ya yi siriri da tsawo. A lokacin da aka zo yin irin wannan gyaran fuska ana gyara sumar da ke wurin goshi a kwakkwafe ta har a taɓo wadda ke a gefen goshin. Ana ɗan shiga ciki yadda wurin zai yi kyau sosai.
b) Gyaran Fukar da Ake yi wa Matan Fulani
A lokacin da aka yi wa mata kitso suna aske gashin
da bai shiga cikin kitso ba na goshi da na ƙeya. Wasu da kansu suke
aske wannan gashi, wasu kuma ‘yan uwansu mata ne ke yi masu irin wannan aski. Akwai
kuma wasu matan musamman waɗanda
ke cikin ƙauyuka, wanzamai ne ke yi masu irin wannan aski. Har yanzu akwai matan
Fulani waɗanda
ake yi wa irin wannan gyaran fuska. Wanzaman da ke yin ayyukan wanzanci a gidajen
waɗannan mata ne ke yi masu
irin wannan gyaran fuska. A lokacin da aka yi sabon kitso wadda aka yi wa
kitson ce ke zuwa wurin wanzami a gidansa don ya yi mata gyaran fuska. Wasu
kuma suna kiran wanzamin ne ya tarar da su a gidajen aurensu don ya yi masu
gyaran fuska. A wasu lokuta kuma akan yi gamon-katar a lokacin da aka yi mata
kitso, sai wanzamin ya zo gidan don yi wa yaran gidan aski ko wasu daga cikin
ayyukan wanzanci. Ana yi wa ‘yan matan Fulani manya da ƙanana gyaran fuska a
lokacin da suka yi sabon kitso. A wannan zamani yin gyaran fuska ga matan
Fulani ya yi sauƙi musamman ga ‘yan mata da waɗanda aka yi wa aure, amma duk da haka ana
yi wa tsofaffi.
c) Tukkaye Uku Waɗanda Ake yi wa ‘Ya’Yan Fulani
A lokacin da jariri namiji ya kai kimanin wata biyu zuwa uku da haihuwa ana yi masa tukkaye uku a bisa kansa. Ana yin ɗaya a goshi ɗaya tsakiyar kai ɗayan kuma a ƙeya. Waɗannan tukkaye ba za a aske su ba, sai a ranar da za a yi wa wannan yaro kaciya, wasu ma kan bar irin waɗannan tukkaye har sai sun girma sosai sun isa aure. Idan suka yi tsawo, sai a riƙa yi masu kitso. Akwai Hausawa waɗanda ke kwaikwayon yi wa ‘ya’yansu ire- iren waɗannan tukkaye.
d) Askin Ɗaurin Guga
Kamar tukkayen da aka yi bayaninsu a sama, wasu jariran kuma maimakon a yi masu irinsa, sai a yi masu askin ɗaurin guga. Ana yin askin ɗaurin guga ne ta hanyar barin sumar tsakiyar kai da kuma wata ta ratsa daga gefen kai zuwa ɗaya gefen kan. Ana yin irin wannan aski kamar yadda ake ɗaura iccen gugar ƙwarya, kuma ana yi wa yara maza da mata irinsa. Ga ‘yan mata ba a aske shi daga nan ne za a fara yi masu kitso a lokacin da gashin ya fara taruwa sosai. Su kuma samari ba a aske shi, sai a lokacin da za a yi masu kaciya, a lokacin da sumar ta yi tsawo sosai, sai a yi masu kotso. Wasu kuma ba a aske masu shi a wannan lokaci, sai lokacin da za a yi masu aure. Shi ma irin wannan aski akwai wasu Hausawa waɗanda suke kwaikwayon yi wa ‘ya’yansu irin sa.
3. 1. 2 Al’adar Tsayar da Gemu
A al’adar Fulani ana tsayar da gemu a lokacin da
mutum ɗansa
ko ɗiyarsa ta yi aure har aka
sami haihu. Idan kuma ba a haifa ɗa ko ɗiya ba da aka yi wa aure ya haihu ba, sai
ya tsayar da gemu a lokacin da ɗa ko ɗiyar tsaransa ya haihu. Ana tsayar da gemu
a lokacin wani buki na aure ko haihuwa. A mafi yawancin lokaci ana tattara
tsararrakin juna a haɗa su
wuri ɗaya
don a sanya masu gemu tare. Ana kuma la’akari da waɗanda aka yi wa kaciya a rana ɗaya, sai kuma a sake haɗa su don sanya masu gemu a rana ɗaya. Tun kafin zuwan ranar ake sanar da
‘yan uwa da abokan arziki da kuma wanzamin gidan wanda shi ne zai sanya wa
wannan mutum ko mutane gemu.
A ranar da za a sanya gemu bayan dukkan ‘yan uwa
da abokan arziki waɗanda
aka gayyata sun taru, sai a kawo ƙwaryar madara a samo ganyen kalgo a naɗa gammo da shi a saka cikin wannan ƙwaryar
madara. Daga nan sai wanda za a sanya wa gemu ya fito ya zauna a gaban dattawa.
A al’adar Fulani an fi son wanzamin da zai sanya wa wani gemu, ya kasance wanda
dukkan mahaifansa watau uwa da uba suna da rai. Idan kuwa wanzamin da yake yin
wanzanci a wannan gida ya rasa ɗaya
daga cikin mahaifansa, sai a samu wani daga cikin dangin wanda za a sanya wa
gemu kuma wanda dukkan mahaifansa ke da rai ya fara sanya wa wannan mutum gemu.
Yadda ake yi shi ne wannan wanda aka wakilta don ya fara sanya gemu zai shafa
ruwan madara na cikin ƙwarya da sabulu, daga nan sai ya riƙa
shafa bayan askar a wurin gashin haɓar wanda za a sanya wa gemu. Daga nan sai ya mayar
wa wanzamin da askarsa don ya ci gaba da yin aski da gyaran fuska don a fito da
gemu daga nan ya tsaya ke nan ba a ƙara aske shi. Idan za a sanya wa Fulani
gemu ana aske saje da gashin baki da hana-ƙarya, shi kuma gemun ana
kwakkwafe sosai ba a barinsa da faɗi sai
dai siriri mai tsawo.
Bayan an gama sanya wa wannan mutum gemu idan
akwai wani tsaransa wanda ya isa sanya gemu amma sai ya ƙi sanyawa, a al’dar
Fulani sai a samu wani abokin wasansa ko wani dattijo ya mame shi ya ɗauko wannan gammo na ganyen kalgo wanda ke
cikin madarar da aka yi amfani da ita wajen sa gemu ya shafa masa wannan ganye
a wurin gemunsa. Da zarar an shafa masa wannan ganye daga nan ya zama dole gare
shi ya zauna a sanya masa gemu ko ya shirya ko bai shirya ba. Wannan dalili ne
ya sa waɗanda
suka san cewa sun isa sanya gemu amma saboda wasu dalilai nasu ba su sanya ba, ko
an gayyace su zuwa wurin sanya gemu ba sa zuwa don tsoron kar a sanya masu gemu
ba tare da sun shirya ba.
A lokacin da ake sanya gemu ‘yan uwa da abokan
arziki za su riƙa bayar da kari. Daga cikin abubuwan da ake
bayarwa akwai kuɗi da
dabbobi. Bayan an gama sanya gemun, sai a miƙa wa dattawa ƙwaryar
madarar da aka yi amfani da ita wajen sanya gemu. Kowannensu zai sha wannan
madara ya kuma shafa wa gemunsa gammon ganyen kalgon da ke cikin madarar. Daga
nan sai su yi masa huɗuba
dangane da abubuwan da suka dace ya riƙa yi da waɗanda ba su dace ya riƙa yi ba. Bayan nan kuma
sai dattawan su karkasa kuɗin da
aka samu na kari zuwa kashi uku. Kashi na farko a raba wa wanzamin da ya sa
gemun da maroƙa, kashi na biyu a ba malamai waɗanda za su yi addu’a, kashi na uku kuma
ana sayen goro don a rarraba wa mutanen da suka tattaru a wurin sa gemun. Sauran
abubuwan da aka samu kamar dabbobi ana bar wa wanda aka sanya wa gemu. Daga nan
sai malamai su yi jagorancin addu’ar fatan Allah Ya sa albarka ga wannan wanda
ya sa gemu kuma Allah Ya tsare shi daga aikata wasu ayyuka na rashin daidai waɗanda bai kamata a ce mai gemu ya yi su ba.
Ana kuma ƙarawa da yin addu’o’in roƙon Allah Ya biya wa dukkan mutanen da suka haɗu a wannan wuri buƙatunsu na alheri. Ana
kuma roƙon Allah Ya ba da damina mai albarka da dai addu’o’in neman biyan buƙatu na
duniya da lahira.
A wannan zamani akwai Hausawa a sassa daban-daban na ƙasar Hausa waɗanda suke yin koyi da irin wannan al’ada ta sanya gemu irin na Fulani.
3. 1. 3 Askin Jarirai na Ranar Suna
Wani ɓangare
na wanzanci wanda al’adun Fulani suka yi naso a cikinsa shi ne askin jarirai na
ranar suna. A al’adar Fulani ba a fito da abin da aka haifa a ranar suna don yi
masa aski, wai don tsoron kada mayu su cinye shi. Wannan dalili ya sa Fulani ke
kiran wanzami kafin ranar suna ko bayan suna don ya yi aski ba tare wasu mutane
sun ga wannan jariri ba. A wannan zamani saboda ƙarin wayewa da ake samu
ta addini da ta ilimin zamani an samu sauƙin irin wannan al’ada. A yanzu wasu Fulani
yi wa jariran da aka haifa masu aski a ranar suna, kuma sai da maraice sosai a
lokacin da dukkan ‘yan uwa da abokan arziki suka tattaru. A wannan lokaci ne
wanzami zai fara yin aski don waɗanda
suka taru a wurin bukin suna su riƙa bayar da kuɗin aski.
3. 1. 4 Zanko
Wani nau’in aski irin na Fulani wanda ya yi naso
cikin al’adun wanzancin Hausawa shi ne zanko. Ana yin zanko ta hanyar aske
gashin kai na ɓangaren
hagu da dama a bar gashin tsakiyar kai kamar layi tun daga goshi har zuwa ga ƙeya. Ana
yin zanko ga yaro namiji ban da mace a aski na biyu bayan askin suna watau a
lokacin askin yada wanka. A duk lokacin da za a yi wa wannan yaro aski ba a
aske wannan zanko, sai dai a gyara shi. Wannan ne ya sa a wasu lokuta idan
gashin ya taru sosai sai a riƙa yi wa yaron kitso wurin wannan gashi na zanko. A
al’ada wannan aski na Fulani ne amma daga baya Hausawa sun riƙa
kwaikwayonsa har ya kai matakin zama askin gado ga wasu Hausawa (Sallau, 2000:32).
3. 1. 5 Nason Al’adun Fulani Dangane da Kaciya
A wurin yin kaciya ma al’adun Fulani sun
yi naso dangane yadda ake yin ta da kuma wasu al’adu waɗanda suka jiɓance ta. Za a iya ganin haka ta yin
la’akari da ranakun da Fulani suka keɓe don yi wa ‘ya’yansu kaciya. Waɗannan ranaku sun haɗa da Juma’a da Lahadi da Talata da Alhamis.
Amma a yanzu saboda wayewar da addinin Musuluci da ilimi zamani suka kawo ana
yi wa ‘ya’yan Fulani kaciya a kowace rana. Wannan ya nuna ke nan wasu daga
cikin al’ummar Fulani sun daina yin irin wannan camfi.
A al’adar Fulani ba a yi wa yaro kaciya sai
shekarunsa na haihuwa sun kai tara zuwa goma sha biyu. Su ma kamar Hausawa ba
sa yi wa ‘ya’yansu masu shekara takwas da haihuwa kaciya. A ranar da aka yi wa
yaro kaciya da an gama, sai a daka garin gero a dama da nonon shanu a ba yaron
da aka yi wa kaciyar ya sha. Haka kuma ana ba dukkan mutanen da suka zo wurin
da aka yi kaciyar wannan gari su sha. Shi ma wanzamin da yaransa ana ba su
wannan gari su sha. Dalilin shan garin shi ne don a sanyaya zuciyar wannan yaro
da aka yi wa kaciya.
3. 1. 6 Tsaga
Tsaga musamman ta gado da ta kwalliya na daga cikin
al’adun Fulani waɗanda
suka yi naso cikin wanzancin Hausawa. Ba kamar Hausawa ba waɗanda a mafi yawancin lokaci ‘yan mata ne
kawai ake yi wa tsagar kwalliya, su Fulani ana yi wa ‘yan mata da samari, kuma
idan za a yi tsagar ba a yin buki kamar yadda ake yi a lokacin da za a yi wa
‘yan matan Hausawa. Akwai ire-iren tsagar gado da ta kwalliya na Fulani da dama
waɗanda har a wannan zamani
ana yi wa ‘yan mata da samarin Fulani ire-irensu, kuma samari da ‘yan matan
Hausawa na kwaikwayon yin su. Ire-iren waɗannan tsaga sun haɗa da tsagar gado ta kalangu da fetali da
kuma tsagar kwalliya ta ‘yar goshi da kibau da ‘yar baka.
i)
Tsagar Gado
A lokacin da Fulani Dallazawa masu jihadi suka ci
Katsina da yaƙi suka kafa mulkin Fulani a wannan masarauta, wasu
Hausawan ƙasar Katsina sun riƙa kwaikwayon al’adunsu musamman waɗanda suka shafi tsaga. Asalin tsagar gado
ta Katsinawa ita ce bille ko tsagar Katsinanci (Sallau, 2000:62, 78). Su kuma
Fulani Dallazawa tsagarsu ta gado ita ce kalangu (Sallau, 2000:90). A saboda
kusanci da waɗannan
Fulani, sai wasu Katsinawa waɗanda
asalinsu Hausawa ne saboda da kusanci da waɗannan Fulani suka daina yi wa ‘ya’yansu
tsagar gado ta billen Katsinanci, sai suka maye gurbinta da tsagar kalangu irin
ta Fulani Dallazawa. Wannan dalili ne ya sa a yanzu a ƙasar Katsina akwai
Katsinawa waɗanda
Hausawa gaba da baya da ke yi wa ‘ya’yansu maza da mata tsagar kalangu a
matsayin tsagar gado.
Irin wannan
al’amari ya faru ga wasu Hausawan a ƙasar Katsina a lokacin mulkin Fulani Sulluɓawa waɗanda su tsagarsu ta gado ita ce bille a
hannun hagu (Magaji, 2002:23). A nan ma an samu wasu Hausawa waɗanda suka maye gurbin tsagarsu ta gado ta
billen Katsinanci zuwa tsagar fetalin hannun hagu irin na Fulani Sulluɓawa. Haka kuma tsagar gadon mahauta ita ce
tsagar fetali a hannun dama (Sallau, 2000:77). Su ma a wannan zamani, sai suka
bar yin irin wannan tsaga a hannun dama suka mayar da ita a hannun hagu irinta
Fulani Sulluɓawa.
Dukkan waɗannan nau’o’in tsagar gado na Fulani har a wannan
zamani akwai wasu daga cikin mutanen ƙasar Katsina da ke yi wa ‘ya’yansu
ire-irensu a matsayin tsagarsu ta gado.
ii) Tsagar ‘Yar Goshi Irin ta Fulani
Irin wannan tsaga ana yin ta a goshi, amma ita ko
kusa ba ta yi kamanni da irin tsagar ‘yar goshi wadda ake yi wa Hausawa ba. Siffar
wannan tsaga ta yi kamanni da kofin cin gasar ƙwallon ƙafa da
makamantansa waɗanda
ake sanyawa don cin wata gasa.
iii)
Tsagar Kalangu Irin ta Fulani
Ita
ma tsagar kalangu irin ta Fulani tana da bambanci da irin wadda ake yi Hausawa.
Tsagar kalangu irin ta Fulani iri biyu ce akwai wadda ake yi ƙanana
kuma sirara, sannan kuma akwai wadda ake yi da girma sosai wadda ta fi irin
wadda ake yi wa ‘yan matan Hausawa girma. ’Yan mata da samarin Fulani ba a yi
masu kalangu biyu-biyu kamar yadda ake yi wa ‘yan matan Hausawa su ɗaya-ɗaya ake yi masu.
iv)
Tsagar Kibau Irin ta Fulani
Irin wannan tsaga Fulani kawai ake yi wa irinta. Ana
yin irin wannan tsaga kamar siffar kibiya wanda a saboda haka ne aka sanya mata
wannan suna. Ana yin ta ne a fuska bisa kundukuki daidai ƙarƙashin idanu wurin da ake
yi wa ‘yan matan Hausawa tsagar kwaluluwa. Ita ma irin wannan tsaga ana yi wa
‘yan mata da samari irinta, kuma a dalilin cuɗanya tsakanin Fulani da Hausawa ya sa ‘yan
matan Hausawa kwaikwayon yin irin wannan tsaga.
ɓ) Tsagar ‘Yar Baka Irin ta Fulani
Wata tsagar kwalliya wadda ake yi wa ‘yan mata da samarin Fulani wadda kuma ta yi naso cikin al’adun wanzanci ita ce tsagar ‘yar baka. Irin wannan tsaga ba ta yi kamanni da irin wadda ake yi wa ‘yan matan Hausawa ba wadda ake yin ta caɓa-caɓa a wurin kumatu. Irin wannan tsaga ana yin layukan tsaga uku-uku ne a kowane kumci kuma kowace ana yin ‘ya’yan tsaga uku-uku ne, amma da na sama da na ƙasa ana yin su a gicciye ne ta tsakiyar ce ake yi a tsaye. Ana yin layukan wannan tsaga da ɗan tsawo kuma dukkansu suna ƙarewa a wutsiyar baki. Bayan an yi waɗannan layuka na tsaga ana haɗe su da ƙananan ‘ya’yan tsaga waɗanda su ma ana tsara su uku-uku ana kuma barin ɗan fili a tsakani. Ita ma irin wannan tsaga ‘yan matan Hausawa na kwaikwayon yin su.
Dukkan waɗannan nau’o’i na tsaga waɗanda aka yi bayani a kan su wanzaman Hausawa ne ke yi wa ‘yan mata da samarin Fulani ire-irensu. Wannan dalili ne ya ƙara jawo hankalin ‘yan matan Hausawa kwaikwayon yin ire-irensu.
3. 1. 7 Goyon Ciki
Wani fanni na al’adun Fulani wanda ya yi naso
cikin al’adun wanzancin Hausawa shi ne goyon ciki. A al’adar Fulani idan mace
ta samu cikin fari ba za ta haihu a ɗakinta ba. A lokacin da cikin ya kai wata shida ko
bakwai, sai a mayar da ita gidan mahaifanta don ta haihu a ɗakin mahaifiyarta. A lokacin da ta haihu
haƙƙin mutanen gidan da take aure ne su turo wanzamin gidansu don ya yi wa
wannan abin da aka haifa dukkan ayyukan wanzanci. Kamar al’adar Hausawa su ma
Fulani namiji ne ke da haƙƙin kiran wanzami ba mace ba. Wannan ne ya sa
wanzamai zuwa gidajen da ba su ke yin wanzanci ba yin ayyukan wanzanci, don
kuwa matar da ta haihu a wannan gida tana aure ne a gidan da suke yin ayyukan
wanzanci (Sallau;2000: 9).
3.1.8
Nason Al’adun Fulani Kan Ire-Iren Ladar Aikin Wanzanci
A lokacin
da aka yi wani aikin wanzanci ga al’ummar Fulani wanda aka yi wa ko iyalansa
suna bakin ƙoƙarinsu wajen kyautata wa wanzamin da ya yi wannan aiki. Misali, idan aka yi
kaciya bayan kuɗi suna
kuma ba da zakara ko kaza ko zabo da kuma damen dawa. Haka kuma idan aka yi
suna a gidajensu idan wanzami ya zo kafin ya yi askin jariri na suna ana ba shi
abinci mai kyau wanda ya haɗa da
danbu da madara a kuma zuba man shanu a ciki. Ana kuma damo hura da nonon shanu
mai kyau a kawo wa wanzamin ya sha. Bayan kuɗin aski da ƙwaryar aski suna kuma ba
wanzamin kan dawo da nono don ya kai wa iyalinsa da ke gida su dama su sha.
A lokacin ɗaurin auren budurwa wanda Fulani ke kira da sunan
walima ana yanka sa ko saniya wanda ake rarraba naman dabbar da aka yanka
kashi-kashi don ba kowa nasa rabon. Daga cikin waɗannan kashe-kashe akwai kushekara da
‘yayanta waɗanda
su ne kason wanzamin da ke yin aikace-aikacen wanzanci a wannan gida. Bayan
kushekara kuma ana ba shi goro a lokacin da za a ɗaura aure. Dalilin da ya sa ake ba wanzami
waɗannan abubuwa shi ne, wai
don shi ne ya yi wa wannan budurwa da za a yi wa aure gyara a farjinta a
lokacin tana jaririya. A saboda haka waɗannan abubuwa suna daga cikin ladar aikin da ya yi.
4. 0 Kammalawa
Kamar yadda aka gani wannan takarda ta yi bayanai
akan ƙaura da shigowar Fulani ƙasar Hausa da kuma irin nason da al’adunsu suka yi
kan wanzancin Hausawa. An fara kawo bayani kan ma’anar ƙaura da ire-irenta da
kuma dalilan da suka sanya Fulani zaɓar ƙasar Hausa a matsayin wurin da suka ga ya dace su
zauna ko don cirani ko kuma don zama na dindindin. Haka kuma an duba ƙaurar
da Fulani suka yi daga ƙasarsu ta asali zuwa ƙasar Hausa. Daga na kuma
sai aka duba fannonin rayuwa na Fulani waɗanda suka yi naso cikin wanzancin Hausawa waɗanda suka shafi aski da gyaran fuska da
tsayar da gemu da askin jarirai na ranar suna da zanko da kaciya da tsagar
kwalliya da goyon-ciki da kuma ire-iren ladar aikin da Fulani ke biyan wanzamin
da ya yi aikace-aikacen wanzanci a gidajensu.
Idan muka dubi waɗannan ayyuka na wanzanci da kuma yadda ake
yin su ga al’ummar Fulani a wannan zamani, za mu ga cewa sun yi naso na a gani
a faɗa kan yadda ake gudanar
da sana’ar wanzanci. Za a iya gani haka ta yadda wasu Hausawa ke kwaikwayon yin
wasu daga cikin waɗannan
al’adu. Misali, idan muka dubi gyaran fuska ƙahon-barewa wanda aski ne
da ake yi wa dattawan Fulani, a yanzu akwai dattawan Hausawa da dama musamman
waɗanda ke zaune a karkara
da suka mayar da yin irin wannan gyaran fuska a matsayin irin askin da suka ga
ya dace a riƙa yi masu. Haka kuma matasan Hausawa waɗanda ke yin hulɗoɗi da Fulani na yin ire-iren askin da ake yi wa
matasan Fulani. Wannan naso bai tsaya a nan ba don kuwa har a wannan zamani
akwai Hausawa waɗanda
saboda hulɗa da
Fulani ba a yi wa jariran da aka haifa masu askin ranar suna cikin mutane, sai
dai a yi kafin ranar suna ko kuwa bayanta. Akwai kuma Hausawa waɗanda ke yi wa ‘ya’yansu zanko wanda a
wannan lokaci wasu ma sun mayar da shi kamar askin gado da ake yi wa dukkan
‘ya’yan da aka haifa masu.
Al’adun tsayar da gemu na daga cikin al’adun
Fulani waɗanda
suka yi naso cikin al’adun wanzanci. A wannan zamani akwai Hausawa waɗanda ke sanya gemu irin na Fulani, watau a
kwakkwafe shi ya yi siriri da kuma tsawo. Haka kuma akwai waɗanda ke bin al’adun Fulani dangane da
yadda ake sanya gemu.
Ta fuskar tsaga ma an samu irin wannan naso na
al’adun Fulani kan wanzancin Hausawa don ‘yan matan Hausawa waɗanda ke yin hulɗoɗi da ‘yan matan Fulani ko waɗanda samarin Fulani ke nema da aure na yin
ire-iren tsagar kwalliyar da ake yi wa ‘yan matan Fulani don su burge waɗannan samari nasu. Haka kuma a wasu lokuta
akwai samarin Hausawa waɗanda
ke yin hulɗoɗi da samarin Fulani ko kuma suna son ‘yan
matan Fulani, a soboda waɗannan
dalilai suna sanyawa a yi masu ire-iren tsagar kwalliya ta Fulani don su burge
waɗannan ‘yan mata nasu.
Ana kuma samun nason al’adun Fulani ta fuskar
ire-iren ladar aikin da ake biyan wanzamin da ya yi ayyukan wanzanci. A wannan
fuska akwai waɗanda
ke ba wanzami kaza da makamantanta idan an yi kaciya da dai sauran ladar aiki
irin wadda Fulani ke biyan wanzamin da ya yi aikace-aikacen wanzanci.
ƘARIN BAYANI
1.
Mbororo’en
su ne waɗanda Hausawa suke kira Fulanin Bararoji waɗanda ke yawace-yawacen
neman wuraren kiwon dabbobinsu. Watau ba zaune suke a wuri ɗaya ba kuma ba sa
yin wata sana’a sai kiwon dabbobinsu kawai.
2.
Filɓe Na’i kuma su ne waɗanda Hausawa suke kira da sunan ‘Yan Korgo.
Suna zama a wuri na wani ɗan
lokaci wanda daga nan ne suke tafiya yawon kiwo. Bayan wani lokaci kuma sai su
dawo wannan wuri. Abin nufi a nan shi ne suna zama rabi da rabi a tsakanin
wurin da suke zaune da wurin da suke yin kiwon dabbobinsu. Idan suka samu wurin
da ya fi wannan wurin kiwo, sai su tashi daga nan su koma wannan sabon wuri.
3.
Fulɓe Shi’e su ne waɗanda Hausawa suke kira da sunan Fulanin
Gida ko Fulanin Zaure. Wannan kuwa ya faru ne a saboda ƙarewar shanunsu sai suka
koma cikin garuruwa suka zauna ko don yin aikace-aikacen addinin Musulunci ko
don zama a fadojin sarakunan ƙasar Hausa inda wasunsu suka riƙa yin
ayyukan alƙalanci ko zama mashawartan waɗannan
sarakuna. A yanzu ire-iren waɗannan
Fulani sun koma Hausawa a harshe da adabi da al’ada kuma daga cikin ire-irensu
ne aka samu waɗanda
suka taimaka wa Shehu Usman Ɗanfodiyo wajen gudanar da jihadin da ya yi
sanadiyyar kafuwar Daular Usmaniyya daga shekarar 1804 – 1809. A dalilin wannan
jihadi ne a yanzu mafi yawa daga cikin gidajen sarauta na ƙasar Hausa zuri’ar
ire-iren waɗannan
Fulani ne suke tafiyar da mulkinsu. A yanzu sun bar yawace-yawacen neman
wuraren kiwon, a maimakon haka sun koma yin noma da kasuwanci da sana’ar
Malanta ko neman ilimin addinin Musulunci da na zamani da dai sauran ayyukan
neman kuɗi.
4. Duk
da musayar al’adu da auratayya da ake yi a tsakanin Fulani da al’ummomi daban-daban a ƙasashen Afrika da dama, ba
a samu irin wannan dangantaka ba a tsakanin Fulani Bararoji da ire-iren waɗannan al’ummomi, don kuwa ba sa aurar da
‘ya’yansu ga kowa sai ga ‘yan uwansu Bararoji. Hasali ma dai sun ɗauka Fulanin Gida na ɓata al’adunsu waɗanda suka gada. Wannan al’amari yana
faruwa har a wannan zamani.
5. Daga
cikin zuri’ar Fulani Sulluɓawa ne
aka sami Sarki Dikko wanda shi ne Sarkin Katsina na farko daga cikin zuri’ar
Fulani Sulluɓawa
wanda ya hau bisa karagar mulkin ƙasar Katsina a cikin shekara ta 1906.
6. Bayan
tuɓe Sarkin Katsina
Abubakar a shekarar 1905 da kuma naɗa ɗan
uwansa Malam Yero a cikin wannan shekara shi ma aka tuɓe shi a farkon shekarar 1906, mulkin
Fulani Dallazawa ya zo ƙarshe a ƙasar Katsina cikin shekarar 1906. A yanzu
zuri’arsu ne ke hakimci a ƙasar Safana da laƙabin Yariman Katsina Hakimin
Safana da kuma a Zakka da laƙabin Gatarin Katsina Hakimin Zakka dukkansu a
cikin Ƙaramar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.
7. A yanzu
zuri’ar waɗannan Fulani ana kiransu da sunan ‘Yanɗakawa, kuma daga cikinsu ne
ake naɗa ‘Yanɗakan Katsina Hakimin Dutsin-ma, wanda yana ɗaya daga cikin Hakiman
Karaga huɗu masu zaɓar Sarkin Katsina. Sauran su ne Ƙauran Katsina Hakimin Rimi
da Galdiman Katsina Hakimin Malumfashi da Durɓin Katsina wadda a da can
sarautar Mani ce, amma a yanzu sai aka mayar da sunan sarautar ga Hakimin Jiƙamshi.
MANAZARTA
Abubakar, S. (1977). The Lamive of
Fombina, Zaria, A. B. U. Press.
Adamu, M. T. (1997). Asalin Hausawa da Harshensu, Kano, Ɗan
Sarkin Kura Publishers Ltd.
Adeleye, R. A. (1971). Power
And Diplomacy in Northern Nigeria, 1804 –1906, Sokoto Caliphate And Its
Enermies, London, Longman.
Adeleye, R. A. (1975). ”Hausaland
And Borno, 1600 – 1800”, a Cikin, Ade Ajayi, J. F. da Crowder, M. History of West Africa, Vol. I, London.
Baƙo, A. (1990);”A
Socio-Economic History of Sabon-Garin Kano 1913 -1989”, Kundin Digiri na Uku
(PhD), Kano. Sashen Koyar da Tarihi, Jami’ar Bayero.
Bello, U. M. (1999), ”An
Immigrant Community:The Nupe in Sokoto, M. A. Sokoto. Sashen Koyar da Tarihi, Jami’ar
Usman Ɗanfodiyo.
Hammani, M. D. (1975);”Adar, The
Tuareg And Sokoto:Relations of Sokoto With The Hausawa And Touareg During The
19th Century”, Sokoto Seminar Paper.
Hogben. J. S. (1967). An Introduction to The History of The
Islamic States of Northern Northern Nigeria, Ibadan, Oɗford University Press.
Ibrahim, M. S. (1982);”Dangantakar
Al’ada da Addini:Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya, Kundin
Digiri na Biyu, Kano. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Johnston, H. A. S. (1967). The Fulani Empire of Sokoto, London, Oɗford University Press.
Laɓers, J. (1997). ”Katsina And The Wider
World:Adɓentures
in The Historiography of Birnin And Ƙasar Katsina”. A Cikin Tsiga I. A. da
Adamu, A. U. Islam And The History of
Learning in Katsina. Ibadan, Spectrum Books Limited.
Magaji, A. (2002);”Wasu
Al’adun Hausawa Yanaye-Yanayensu a Ƙasar Katsina, Kundin Digiri na Uku, Kano. Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Nadama, G. (1977);”The Rise
And Collapse of a Hausa State:A social And Economic History of Zamfara”, Kundin
Digiri na Uku, Zariya, Sashen Koyar da Tarihi, Jami’ar Ahmadu Bello.
Na’iya, M. (1997). ”A Discourse
in The Intellectual Legacies of Some Pre-Jihadic Muslim Scholars in Katsina”. A
Cikin “Tsiga, I. A. da Adamu, A, U. Islam
And The History of Learning in Katsina. Ibadan, Spectrum Books Limited.
Osaghae, E. E. (1994). Trends to Migrant Political Organisations in
Nigeria: The Igbo in Kano, Ibadan, IFRA.
Prothero, R. M. (1981). Typology of African Population Mobility,
London.
Sallau, B. A. S. (2000);”Wanzanci:Matsayinsa
na Al’ada da Sana’a a Ƙasar Hausa”, Kundin Digiri na Biyu, Kano. Sashen
Koyar da Harsunan Nijeria, Jami’ar Bayero.
Usman, Y. B. (1972). Some
Aspects of The Eɗternal
Relations of Katsina Before 1804, Saɓanna
Vol. I. No. 2.
Usman, A. F. (2000). Yorubas in Gusau:A Preliminary Surɓey, Ɗegel, Journal of The Faculty of Arts And Islamic Studies, Sokoto. Usman Ɗanfodio University.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.