Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Waƙar Noma
Ta Makaɗa Idi Loga
Tarihin
Makaɗa Idi Loga
An
haifi Idirisu kimanin shekaru sittin da biyar (65) da suka wuce, wato wajajern
shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da hamsin da bakwai (1957)
a wani gari da ake kira Dodon sahu daga
baya suka tashi suka koma garin malamai a can ne ya girma daga nan sai
suka koma garin Kwakwara da ke cikin
yankin Gangara ta gundumar Sabonbirni a ƙarƙashin ƙaramar hukumar mulkin Sabon Birnin jihar Sakkwato,
nisan kilomita uku daga Gangara, kuma har yanzu a nan yake zaune. Garin
Kwakwara ya yi iyaka da garin Tulu-Rudu daga Kudu, yayin da kuma garin ya yi
iyaka da Satiru daga Gabas.
Idirisu
ya gadi kiɗi daga kakansu
Amadu Maiwasa har zuwa ga babanshi wanda makaɗin noma ne, Idi Loga ya gadi kiɗin noma daga babansa kafin daga
bisani ya faɗaɗa sana’arsa ta kiɗin noma zuwa ga na Sarakuna da masu hannu da shuni. Idi yana da
kimanin waƙoƙi fiye da ɗari biyu da hamsin (250) waɗanda ya yi a ciki da wajen Nijeriya.
Ya sami laƙabinsa ne na
Loga saboda irin rawarsa wadda yake yi a lokacin waƙarsa. Idi loga yana da matan aure
ukku (3) su ne; Sahiya da Sa’a da kuma Talatu, yana da ‘ya’ya goma sha tara a halin yanzu, tara maza
ne, sauran kuma mata ne. mazan kuma sun haɗa da Ibrahim, da Basiru, da Isiya, da Yakubu, da Muhmmadu Yazid, da Ashiru, sai
tagwayensa Hassan da Hussaini suna nan ƙanana.
Yaransa
da suke yawon kiɗi da
su kusan duk danginsa ne na jini waziri Hamza ƙanensa ne wanda ke bi masa, akwai yayansa wanda yake bi
ma uwa ɗaya uba ɗaya mai suna Isihu, sai Sale shi ma
yayansa ne, amma ɗan wa
da ɗan ƙane suke da shi, akwai kuma wani ƙanensa Sule, da wani ƙanen nasa da ake ce ma Buzu Ɗanƙargi, amma sunansa zananne shi ne Isiya. Sai wani
abubakar ɗan Kaura
wanda abokin Hamza ne. maroƙinsa
wato Maba sunansa Sada, wanda ake kira Ɗanmaliki
shi ma mutumen Kwakwara ne. kayan kiɗinsa
shi ne kuru wanda ake kiɗin
noma da shi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.