Ticker

6/recent/ticker-posts

Isaka

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Isaka

 Ga waƙar :Ya Allah sarki

:To Bisimillah Allah sarki,

: Tabaraka Sarkin baiwa,

: Gode ta jallah Allah sarki,

: Jallah maƙagi kai yaywa.

  Jagora: Ko da malam za ya karatu, x2

‘Y/Amshi: Ce Bisimillah ce yah hwara.

 

  Jagora: Koy Bisimillah ya ce Allah, x2

‘Y/Amshi: Za ya ga aiki nai ya yi kyawo,

: Ya sama gyara.

 

  Jagora: Kutau ja turaye,

‘Y/Amshi: Ni zan ɗauko waƙa.

 

  Jagora: Zan shirya waƙa dalla-dalla,

‘Y/Amshi: Ku saurari shi an naku.

 

  Jagora: Zaku ji waƙar, x2

‘Y/Amshi: Gyaran gona Idi loga in ya hwara.

 

  Jagora: Yara ku tashi, x3

  ‘Y/Amshi: Ku sa mi loga,

: Tunda na zaki ya kai geji.

 

  Jagora: Na riƙa waƙar,

‘Y/Amshi: Gyarau gona,

: Raggo na cizon yatsa,

: Wai shi har rai nai ya ɓaci.

 

  Jagora: Ya tahi dajin wajen aiki,

‘Y/Amshi: In yay aiki nai mai waƙa.

 

  Jagora: Giwa kalaceuki ita ce,

‘Y/Amshi: Kalacin Kura ta ci nama,

: Ku ce ma maza su yi aikin gona,

: Idi roƙo nak kama.

 

  Jagora: Wayona ban san gona ba,

‘Y/Amshi: Na san ƙauye na san birni,

: Kuma waƙa ce tak kaini.

  Jagora: Idi ko da bani da gona,

‘Y/Amshi: Bazan iya dukawa gona ba,

: Sai nai waƙa ko ni ɗai ne.

 

  Jagora: Yara Allah yay yoni,

‘Y/Amshi: Amma dai ba don noma ba,

: Nasan waƙa don ta sanni.

 

  Jagora: Ku makaɗa,

‘Y/Amshi: Ga idi roge mai turaye nan,

: Fal jangam sun dare.

 

  Jagora: Kun san Idi gun zuba waƙa, x2

‘Y/Amshi: Rana kin ba kowa aiki.

 

  Jagora: Ko da zaki yazan gawa,

‘Y/Amshi: Ɗan kura bai hwara kirari,

: In dai zaki hay ya haihwa,

: Ko a gida,

: Kuma ko da daji,

: Ko bisa hanya in an gammu.

 

  Jagora: Idi ko ba kayan waƙa,

‘Y/Amshi: In wani hay ya san me wasa,

: Zai ce mune jigoginta,

: Makaɗa ku rage mana wargi.

 

  Jagora: Jirgi ba a haɗa shi da mota,

‘Y/Amshi: Ko da kusa tai tahhwaɗi,

: Idi ba’a haɗani da bami,

: Ko wace hanya sai na bas shi,

: Bami ko da ya iya waƙa,

: Ba zai iya loga ta hili ba.

  Jagora: Kamar maza tana ga mazuru,

‘Y/Amshi: Ko ba hwaɗa da wawan kallo,

: Indai Ɗangwamma ya wulga,

: Ko ba waƙa sai ya yi shawa,

: Balle waƙa ce tsintsinta,

: Yara harshen har ya saba,

: Irin yada nace ta zam waƙa.

 

  Jagora: Yaro masana ka bugun hurmi,

‘Y/Amshi: Shanun huɗa ɗan Mamman.

 

  Jagora: Kobi yaro,

‘Y/Amshi: Ummaru sauda,

: Na ƙwarai,

: Mai geron bayi.

 

  Jagora: Dakan dawa ɗau gyara,

‘Y/Amshi: Su guda garkan Mamman,

: Isaka ka koma gona.

 

  Jagora: Ni Idi in ɗauko gurmi,

‘Y/Amshi: Na riƙa aiki,

: Sai ta hwaɗi,

: Na riƙa waƙa sai ta tashi.

 

 Jagora: Sai aje kallonmu da ni da Isaka,

‘Y/Amshi: Indai gadon noma yay yi,

: Ni nai gadon wajen waƙa,

: Yara tahiya sai doki,

: Jaki na kallon hanya.

 

  Jagora: Maganan ciki sai turu,

‘Y/Amshi: Shi wani aiki sai ɗan gado,

: Noma sabo nai ne,

: Ni waƙa sabo na ce,

: In dai ga Idi loga.

 Jagora: Isaka yana yi mai aikin,

 ‘Y/Amshi: Gona cin waken kusu,

 

Jagora: In ko waƙar nomace,

‘Y/Amshi: Haka sai ni Idi loga,

: Mai turaye ɗan Garba,

: Dogon mai doron waƙa.

 

Jagora: Wani ya san Idi loga,

‘Y/Amshi: Wani bai gane Idi ba,

: Sai jin sunan hanya.

 

Jagora: Wani ya zagan na rama,

‘Y/Amshi: Ga wani ya ɓatan na kyale.

 

  Jagora: Wani ɓatan[1] don gaɗo,

‘Y/Amshi: Ga wani ya ɓatan ɗan waƙa.

 

  Jagora: Idi na tahi yawan waƙa,

‘Y/Amshi: Makaɗa na min wani dubi.

 

  Jagora: Wai ni sun duban dan yaro,

‘Y/Amshi: Har wani ya zunɗan dan jummai,

: Ya ce waƙa ta zama banza,

: Ku ji yaro yayo waƙa,

: Wanga da ka ce mai ɗan yaro,

: Ko ka mance baiwar Allah?

 

  Jagora: Lura da gero ya yi idanu,

‘Y/Amshi: Ɗan masara na kayan gemu.

 

  Jagora: Kasan Allah shi ka sadauki,

‘Y/Amshi: Shi zai gyara mai kaya nai.

  Jagora: In dai waƙar nomace,

: Dan bari bar ceman ɗan yaro,

‘Y/Amshi: Na kai meli[2],

: Babban jirgi,

: In dai harshen waƙoƙi ne.

 

  Jagora: Allah yay maka baiwa

‘Y/Amshi: Ni kuma loga nai mai waƙa.

 

  Jagora: Sai ƙato ya je gona,

‘Y/Amshi: Ya hunce zai riƙa aiki.

 

  Jagora: Ya tuna waƙa nan Isika,

‘Y/Amshi: In ya yi waƙar,

: Kan da ya noma,

: Zai ya ga gonan har an nome.

 

 Jagora: Sai matata ta zuba tsaba,

: Ta tuna waƙar nan ta Isaka,

‘Y/Amshi: In tai waƙar,

: Kan da ta surhwa,

: Zata ga tsabar ta zan surhe[3].

 

 Jagora: Don tsananin baiwar ga Isaka,

‘Y/Amshi: Cikin wata biyu yassa gero,

: Sai Allah ya hiddo shi,

: Ya nome ya maimaice,

: Ikon Allah ya kai geron.

: Gero ya isa girbi,

: Sai yaɗ ɗau kwashe yag girbe,

: Kowace kuyya ya yo jene,

: Kowane jene in an yanke,

: Jaki bai ɗauko geron.

 

  Jagora: Hamza watan huɗu,

: Ya kwan goma,

‘Y/Amshi: Legas yay shikkam[4]

: Masara tai,

: Masara na nan lil-lil- lif,

: Kamar lokacin malka[5] ya kama,

: Masara na nan ta kosa,

: T a kuma bushe,

: Har an kalle,

: Ko wane tushe ya ya yo leda.

 

  Jagora: Na tambayi yaran loga,

: Ledodi nawa ne sun ƙirga,

‘Y/Amshi: Ni leda miliyan ni ƙirga,

: An buga shago duk an sanya

: An buga tuta wajen shago,

: Ga yara nai nan sun zauna,

: Kusa ga shago sai sun bashi,

: Tun da abun jinƙai[6] ya samu.

 

 Jagora: Kwaren ga na bakin gulbi,

‘Y/Amshi: Hamza roƙon mu na sabon birni,

: Babu manomi mai gasa tai,

: Sai an koma wajen tsara,

: Inda zuma mai saƙar gini,

: Ko jiya Idi yay kallo nai,

: Ko wace saƙa ta zam dawa.

 

  Jagora: Yara ku rage min guru x2

‘Y/Amshi: Ga Idi mai sabon launi.

  Jagora: Ga Idi zai buɗe rikoda x2

‘Y/Amshi: Za ku yi saurare don Allah.

 

 Jagora: Tsohuwa na kofar ɗaki,

: In yarinya in ta wulga,

: In dai taso ta yi shari,

‘Y/Amshi: Sussakai ya tashi,

: Kaji ta yi kiran yarinya,

: Wance taho duba min ƙeya,

: Ni keya[7] tasha min kai,

: Sun san ba keyace ba,

: Ke dai cuta kik ƙulla.

 

 Jagora: Tsohuwa bari kulle shari,

‘Y/Amshi: Inji na Mamman Idi loga,

: In ko kin ce zaki yi sharri,

: Gobe ga Allah sai kin ƙone,

: Duk wanda ka kullin sheri,

: Baya darajja ko wajjen wa.

 

  Jagora: Yara ku ɓaci uwah hankaka,

‘Y/Amshi: Don ta ce ɗan wani na ta,

 

  Jagora: Ko da kun ɓatan duka ɗai ne,

‘Y/Amshi: Yara duk ka bai ji mai ciwo.

 

  Jagora: In kan tai magana,

‘Y/Amshi: Ku bugeta,

: Kuce mata loga ya aiko ku.

 

  Jagora: Mai tare tiwha don hwaɗin kai,

‘Y/Amshi: Uwar su wane,

: Mugunyar tsohuwa,

: Ƙasa mai kircin gado.

 

  Jagora: Madara mai dogon kwabro,

‘Y/Amshi: Ni se na batat ta kyale.

 

  Jagora: Da dariya nika ɓacin ‘yar ƙasa,

‘Y/Amshi: In waste mat kayanta.

 

  Jagora: Harafi maza kama ba ƙauye,

‘Y/Amshi: Kuji tace nai mai sheri,

: In tace nai mata sheri,

: In zana mata sunanta,

: Kuji sunan nan ya bita,

: Sannan ku sawo mani reza,

: In aske mat tsoron kai.

 

  Jagora: Kakata mai kircin gado,

‘Y/Amshi: Ga madara mai dogon kwabro,

: Ga balbela mai kyau banza,

: Idi maison ya ci wargi.

 

 Jagora: Shegun tsohin nan ka baci,

‘Y/Amshi: Watsawa nan nika noma.

 

 Jagora: Da mu gyara,

‘Y/Amshi: Gara mu ɓata,

: Kowag gyara,

: Ya ci uwar shi.

 

 Jagora: Tshohuwa bari turin Idi,

‘Y/Amshi: Don Idi bai ɗau wargi ba,

: Kadda ki nuna mai ɗanyen[8] kai,

: Ɗanyen kai ni Idi ba,

: Ko ni ma kaina ɗanye ne.

 

  Jagora: Mamuda faɗa mata  ba ni da kyawo,

‘Y/Amshi: Kada ta faɗamin don Allah.

 

  Jagora: In ko tace sai ta jani,

‘Y/Amshi: Sai ƙasƙanci ya sha man ka,

: Don sai nay talla ‘yar iska,

: Gari – gari,

: Zan zan karsheta.

 

  Jagora: Idi ba a gwada mini kauɗi,

‘Y/Amshi:Komi ƙato ya kai ƙato.

 

 Jagora: Dutsi ba a tare shi da ƙarhi,

‘Y/Amshi: Komi ƙato ya kai ƙato.

 

  Jagora: Ba’a hwaɗama biri ya yi ɓanna,

‘Y/Amshi: Inji ruwayan Idi loga.

 

  Jagora: Baki gwada mini hanya – hanya[9],

‘Y/Amshi: Kisan ko wayo na hiki.

 

  Jagora: Sai kin zambo ki koma gyara.

‘Y/Amshi: Idi na kallon ki,

: In dai baki san Idi ba,

: Yanzu ko sai kin sanshi,

: Sauro mai ramar gayya,

: Idi loga goyan Jumma,

: San keke mijin ‘yar tanko,

: Wa iya gane ma sawunka.

 

  Jagora: Kin ga na Ummaru yaron Jumma,

‘Y/Amshi: Idi loga runbun twasshi,

: Ko wah wahda sai ya tara.

 

 Jagora: Ga wata tai wawta kan Idi,

: Na rantse sai ta hwaɗa,

‘Y/Amshi: Ta hau bori don loga,

: Ku hwaɗa mata dai ta yi niya,

: Don sai ta hau tsallen kayanta.

 

  Jagora: Ba’a hawa bori don loga,

‘Y/Amshi: Ƙirgin giwa,

: Bai agalemi[10],

: Komi malam,

: Yak kai malam,

: Fatar zomo bata ceroki,

: Ko an turda ta bar aiki.

 

 Jagora: Ko kin hwa bori kan loga,

: Idi bejeta wurin ki,

‘Y/Amshi: In dai bori sayu[11]ne,

: To kuma sayun nai,

: Sayun kalgo ko dorowa,

: Ko kuma sayun dogon yaro,

: Ubangiji Allah ka tsare,

: Dauda dan ƙaunar Annabi,

: Mutuwar[12] Ubangiji Allah.[1]  Zagi.

[2]  Babban jirgin ruwa mai ɗaukar manyan kaya.

[3]  Tsabar/hatsin da aka surfe.

[4]  Shuka.

[5]  Lkacin mamakon ruwa kamar wajajen watan ogas.

[6]  Taimaka wa jama’a.

[7]  Kwarkwata.

[8]  Rashin kirki ko rashin tunani ko cin mutuncin na gaba.

[9]  Dubara iri-iri.

[10]  Buzu wanda ake yi da ƙirgin/fatar rago. Malaman azure suka fi amfani da shi.

[11]  Sanyu ko sayyu na icce.

[12]  Idan mutum ya mutu wanda ba a tunanin cewa wani ya yi masa sihiri ko sammu ko sa makami ya kasha shi, sai a ce mutuwar Allah ce ya yi.

Post a Comment

0 Comments