Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
(Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Tatsuniyar Wata Kyakkyawar Yarinya Mai Masoya Da Yawa
Gatanan - gatananku
A
wani gari an yi wata yarinya kyakkyawa wadda ta shahara a kan kyawo, tun kafin
ta girma duk wanda ya gane ta sai ya yi maganarta saboda kyawo. Saboda haka ne
ma sai iyayenta suka yanke shawarar kai wannan yarinya riƙo
a wani gari mai nisan gaske, wanda yake da wani daji mai hatsarin gaske a
tsakaninsa da garinsu, akwai dabbobin daji kowaÉ—anne iri da kuma iskoki. Lokacin da ta girma sai masoya suka taso mata
daga ko’ina a cikin yankin, samari da dama sun shiga neman aurenta amma sun kauce,
sun kauce ne ba don komai ba, sai don Æ™a’idar da ta sa, Æ™a’idar
ita ce duk wanda zai aure ta sai ya raka ta ganin gida!
Ba raka ta ganin gidan ne matsala
ba, sai dai irin haÉ—arin da ke cikin dajin, akwai sheÉ—anun aljanu da kuma miyagun dabbobi irinsu kuraye da damisa da zakuna, su
kuma macizai ba maganarsu ake yi ba. Ita kuma wannan yarinyar ta ce “dole sai an
ratsa wannan dajin an raka ni na gano gida”, gashi kuma lokacin babu abin hawa
sai dai a tafi a ƙasa. Manema aurenta duk suka kauce don tsoron aljanu da
sauran tashin hankalin barazanar dabbobi irinsu zaki da kura da damisa da
sauran irinsu.
Sai
wasu samari su uku suka ce “mun yarda zamu rake ki komai rimtsi”, yarinya ta yi
murnar jin haka, sai aka sa ranar tafiya, an ba su shawara aka ce kowanensu ya
shirya, don su yi tanadin laƙunna irinsu; dagumma da layu da
addu’o’i. Da lokacin tafiya ya yi sai samarin suka shirya suka yi bankwana da
danginsu suka tasam ma gidansu budurwar saboda a can ne za a tashi. Ko da suka
isa yarinyar ta kimtsa, babu wani É“ata lokaci sai suka fita. Sun kama hanyar
suna ihu, suna kirari, suna bugun ciyayi da ‘yan Æ™ananan itace, sun wuni
sun kwana suna tafiya a cikin dajin, sai ga wasu zakuna guda uku sun taso masu
don su sami abin kalaci! Nan take sai wannan yarinya ta É—ora hannu a ka ta
fara kuka, sai samarin suka ce “me ya sa kike kuka?” Sai ta ce; “abin da zai
halaka mu na gani” sai suka ce ai kuwa babu abin da zai taÉ“a ki muddin muna
nan raye, sai suka fara karafkiya[1] da
zakunan uku,
Suna ta É—auki ba daÉ—i, sai wani irin
rugugin zakuna kake ji suna wata ƙara suna gunza! Su
kuma samarin sai kibau ke tashi tsutsul! Tsutsul! Tsutsul! Suna cikin haka sai
kuma yarinyar ta sake É“arkewa da kuka! Sai
guda ya sake tambayarta cewa “me aka yi har kike kuka?” Sai ta ce “Ni wallahi Æ™isa
nike ji kamar in mutu!” da ya ji bayaninta sai ya tambayi dangin cewa “ko kuna
iyawa da zakunan nan uku ku biyu don in je neman ruwan?” Sai suka “eh”, nan
take ya tafi wajen neman ruwa, ya bar su suna ta faÉ—a da zakunan, sai
rugugin zakunan kawai kake ji “Gurrrrrr!, Guuuuur!! Gurrrrrrrr!!!.”
Duk
faÉ—in dajin nan ya
yawace shi bai sami ruwa ba, sai can ya hangi wata tsohuwar rijiya, inda yake
tunanin ya sami ruwan don ya kai mata, ta sha don rayuwarta ta dawo. Da isarsa
wajen rijiyar sai ya ga har ta fara yana-yana, ya leƙa
bai hangi ruwa ba, sai ya samu wani dutsi ya jefa, sai ya ji dutsin ya faÉ—a kandam! Sai kuma
ya ji an ce “wane ka samu?” Sai wani ya ce “shi kenan na samu kuma na haÉ—e!” ashe aljannun
ruwa ne suke jiran rabonsu ya faÉ—o! Sai ya ce “kai!kai!kai!” “dutsi kenan
ina ga ni mutum?” Sai kuma ya tuna da irin halin da yarinyar nan take a ciki na
tsananin ƙisa, ai kuwa sai ya raba ƙafafuwansa ya shiga
rijiya! Yana riƙe da ɗan ƙoƙonsa. Ya yi ta yin ƙasa
har ya kai inda ruwan, ya É—ebo ya yo sama, ai kuwa sai aljanun ruwan nan suka ce “da
wa aka haÉ—a mu ba da kai ba?”
Shi kuma sai sama yake yi, daga mai katse masa layu, sai mai katse masa warki,
har dai ya fito wajen rijiyar da ɗan ruwansa kacal-kacal a cikin ƙoƙo.
Su kuma waÉ—ancan samarin biyu da suka rage da zakuna uku suna ta
artabu[2] da
su, sai ta sake fashewa da kuka, sai gudan ya tambaye ta “mene ne?” sai ta ce “wallahi
É—ari (sanyi) nike ji kamar in mutu!”
Sai ya
ce wa gudan “kana iyawa da zakunan don in je in nemo mata wuta don kar ta mutu?”
Ya ce “ina iyawa”, shi kuma ya tafi ya bar shi suna ta karafkiya da zakukin nan
guda uku. Ya faÉ—a cikin daji bai
san inda zai nufa ba don ya samo wuta! Duk inda ya nufa sai ya ga babu wuta,
sai can ya hangi hayaƙi yana tashi, da ya matsa sai ya ga wuta, to ashe
aljanu ne su goma suke gashin mutum tara da suka kamo! Yana ji sai É—aya daga cikinsu ya
ce “ina jin warin mutum”, sai wani aljanin ya ce masa “bayan waÉ—annan guda tara da
muke kawa?” Sai ya ce “shi wannan mai rai ne”, sai wancan ya ce “to Allah ya kawo
shege don mu cika goma, kowa ya É—auki guda mu huta da rabo”. Shi dai yana É“oye yana jin su,
har ya ji kamar ya koma, sai kuma ya tuna halin da yarinya take ciki, sai kuwa
ya fara jan ciki har ya matse wutar, sai kuwa ya yi wuf! Ya É—auki bakin wuta ya
juyo da gudu. Da ganin haka, sai aljanun nan suka biyo shi aguje, sai sun yi
kamar su kama shi, ya bauÉ—e masu, a sake
notawa da gudu, har ya tsare masu fintinkau, suka koma.
Lokacin da ya isa wajen yayinya ya
tarar mai É—ibar ruwa ya kawo ruwa, shi kuma wancan
É—ayan ya kashe zaki guda sauran
biyun sun ranta cikin na kare. Ita kuma yarinya har ta galabaita saboda matsalolin da
suka addabe ta! Su ukun suka tayar da ita suka bata ruwa ta sha, suka haÉ—a mata gwami ta ji É—umi duk dai
rayuwarta ta dawo daidai. Ta dubi waÉ—annan samari nata ta ga irin wahalar da
kowa ya sha don ceto rayuwarta, sai ta tambayi kanta cewa
“shin daga cikinsu wa zan
aura?”
Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.
Tambayoyi
1.
Saboda me mutane suke
son yarinya kyakkyawa?
2.
WaÉ—anne matsaloli ne masoyan yarinyar
nan suka shiga a kan hanyarsu ta rakiyarta ganin gida.
3.
WaÉ—anne irin darusa ne aka koya daga
wannan tatsuniyar?
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.