Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Tatsuniyar Tallar San Birai
Gatanan – gatananku
Wasu birai ne suke da wani ƙaton
sa, kuma suke son su sayar da shi, suna zagaye
tunga-tunga suna tallarsu ga kowa da kowa. Duk inda suka je sai su ce “kuna sayen sa?” Idan an ce “eh”, sai a tambaye su nawa san yake? Sai su ce ai san baya da tsada, “kullun
mu zo mu ba mutum kashi bakin sanmu”, sai mutanen su ce “kai don Allah ku tai
ku ba mutane wuri, saboda sa kullum sai a ba mutum kashi?” Sai su wuce.
Bayan sun ga cewa mutane sun ƙi sayen sansu, sai
su wuce wata tungar, suna ta yin haka har suka isa wata tungar, a can suka iske wata tsohuwa, wadda ta kira su ta tambaye su “nawa ne kuɗin sansu?” Sai suka ce; “sanmu ba tsada, kullum sai mu zo mu ba mutum kashi mu tafiyarmu”. Ita kuma tsohuwa babu wani abun da take tinƙaho da shi sai
surukanta guda uku, masu auren ‘ya’yanta uku, babbar ‘yar Zaki yake aurenta, ta
biyu kuwa damishi, ta ukun ce karen gida ke aure. Sai kuwa ta ce wa birai “to na saye ku shigo ku ɗaure man shi nan”, “na saye ku rinƙa zuwa kuna ba ni kashin kullum”.
Safiya na yi kuwa sai birai suka shiga daji suka yo damen buloli, babban ya ɗauko ya shigo gaba, da zuwa kofar gidan tsohuwa bai tsaya ba sai kofar ɗaki, ya aje damen buloli tim! ya ce “assalamu alaikun tsohuwa gamu mun zo”. Tsohuwa kuwa ta fito ta miƙa bayanta suka yi ta bugu har suka gama, suka ce “to tsohuwa mun tafi sai gobe in mun dawo”. Tsohuwa ta koma ɗaka tana darzar kuka. Gobe ma suka sake zuwa da damen tsuma babban ya aje tim!
Ya ce “tsohuwa fito gamu mun zo”, sai ta fito ta kuma
sake miƙa masu bayanta suka yi ta zane ta har ta yi taushi, sannan suka
tafiyarsu suka ce “sai gobe in mun dawo”.
Wanshekare sai ga zaki ya zo wajen
ganin surukarsa wato tsohuwa, sai ya iske ta a kwance tana nishi! Sai ya ce “tsohuwa lafiya kike ƙunnai[1]?”
Sai tsohuwa ta ce, “wai wasu birai ne suke zuwa kullum suna ba ni kashi don na sayi sansu!” Sai zaki ya ce “ko yau suna zuwa?” Sai ta ce
ai kullum sai sun zo, sai zaki ya ce; “yi shurun ki, wannan matsala tamu ce”, “ke
baruwanki, ƙyale ni da su”.
Can sai ga sallama ta babban birin
nan, sai zaki ya tambayi tsohuwa “Wancan mai sallama da tsauri har cikin kai
wane ne?” sai tsohuwa ta ce “Birai ne, wannan muryar
babbansu ce”, sai zaki ya ce wa tsohuwa, “tsohuwa ba wata ƙofa a ɗakinki?” Ta ce “a’a”. Sai kuwa ya banki bangon Gabas na ɗakinta, kun san zaki da ƙarfi, sai ya buge
bangon, ya yi ƙofa ya bi ya hurce ya tafiyarsa!
Tsohuwa ta fito suka ba ta kashi suka gama suka ce “sai gobe in mun dawo”.
Gobe kuma sai ga Damishi ya zo wajen ganin surukarsa wato tsohuwa, sai ya iske ta a kwance tana nishi! Sai ya ce “tsohuwa lafiya kike ƙunnai?” Sai tsohuwa ta ce, “wai wasu birai ne suke zuwa kullum suna ba ni kashi a kan sansu!” Sai Damishi ya ce “ko yau suna zuwa?” Sai ta ce “ai kullum sai sun zo”, sai Damishi ya ce; “yi shirunki, wannan matsala tamu ce”, “ke baruwanki, ƙyale ni da su mu za a yi wa shegantaka?” Can sai ga sallama ta babban birin nan, sai Damishi ya tambayi tsohuwa “Wancan mai sallama da tsauri har cikin kai wane ne?” sai tsohuwa ta ce “Birai ne kuma waccan muryar babbansu ce”, sai ya ce “waccan hanya tsohuwa wa ya yi ta?” tsohuwa ta ce “zaki ya yi ta”. Sai ya ce “ai ni ma ita zani biya”, ya bi ta nan ya sulale!.
Tsohuwa ta fito suka ba ta kashi suka gama suka ce “sai gobe in mun dawo”.
Kafin lokacin zuwan birai kuma sai
ga karen gida ya zo wajen ganin surukarsa wato tsohuwa, sai ya iske ta a kwance
tana ƙunnai! Sai ya ce “tsohuwa lafiya kike ƙunnai?” Sai tsohuwa ta
ce, “ba lafiya uwaka! Ɗan neman mutumin banza”, Sai kare ya sake cewa “tsohuwa ki yi haƙuri ki gaya man yadda
aka yi?” ita tsohuwa tana ganin cewa zaki ya kasa, damishi ya kasa to balle kare. Ya dai cigaba da rarrashin surukar tasa har
ta gaya masa, Sai ta ce; “wai wasu birai ne suke zuwa kullum suna ba ni kashi a kan sansu!” Sai Kare ya ce “ko yau suna zuwa?” Sai ta ce “ai kullum sai sun zo”, sai
karen ya ce; “kwantar da hankalinki, wannan matsala tamu ce, ke baruwanki, ƙyale ni da su, mu za a
yi wa shegantaka?” “Idan sun zo ko sun yi sallama kar ki amsa, kyale su”. Can sai ga sallama ta babban birin nan, sai Kare ya tambayi tsohuwa “Wancan
mai sallama da tsauri har cikin kai wane ne?”
Sai tsohuwa ta ce “Birai
ɗin ne, sai ya ce kar ki amsa kyale su”, da birai suka ji sun yi sallama ba a amsa ba, sai suka ce “ko tsohuwa ta mutu?” Sai wasu daga cikinsu suka ce “ai ko ta mutu sai mun buga”, suka ce ma
babban “kai dai shiga ka fito mana da ita” Shi kuma kare da ma ya laɓe bakin ƙofa, babban birin nan
ya miƙo kansa sai kare ya cafke wuyansa a daidai maƙogwaronsa, sai suka yi
gumu[2] a
cikin ɗakin tsohuwa, sai kokawa suke yi kowa na ƙara, su ko birai suna ta kirari (sun ɗauka tsohuwa ce aka kamo), suna cewa “yawwa babba jawo ta, jawo mana mu
buga”, shi kuwa ta ƙwatar ransa yake yi. Ai da suka dunkule da wata kokawar sai waje gaban sauran biran,
Lokacin har babba ya yi taushi, amma kare bai sake shi ba, sai da rai ya yi halinsa (ya mutu). Da ganin haka ai sai sauran kowa ya ranta a cikin na kare! Sai tsohuwa ta ce “ashe kare ya fi zaki da damisa zuciya”. Tun daga nan tsohuwa ta sami lafiya, ba wanda ya sake zuwa balle ya ba ta kashi, ta ɗauki kare da mutunci fiye da sauran.
Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.
Tambayoyi
1.
Daga wannan tatsuniyar
nawa ne kuɗin san birai?
2.
Daga cikin surukan
tsohuwa wane ya fi ƙarfi? Wane daga ciki ya taimaki tsohuwa?
3.
Waɗanne irin darusa ne aka koya daga
wannan tatsuniyar?
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.