Ticker

6/recent/ticker-posts

MAI BUNU A GINDI

1. Mai bunu ɗaure ƙugu,

Ba ya kai ɗaukin waninsa.


2. Duk mai matsala gidansa,

To ya fara kula da kansa.


3. Shsshigi ne cusa kai ne,

Ya zaƙewa maƙociyarsa.


4. Cewa zai gyara nata,

Bayan ya kasa nasa.


5. Mai ‘ya’yayensa titi,

Gyara nasu wajibinsa.


6. Ai halin zakara daban ne,

Tsabarsa ya ba waninsa.


7. Wai shi domin ya birge,

Sai ya sa tsakuwa gabansa.


8. Wane domin dai a tafa,

Zai kunna wuta gidansa.


9. Don ya birgi ‘yan tamore,

Zai fatattaki ‘yan uwansa.


10. Zai ƙulla faɗa da yaki,

Don a ce mas ba kamarsa.


11. E, don su yaba su tafa,

Ko su ce masa ba kamarsa.


12. Bai sani ba ya cuci nasa,

Shi ya karya maƙotacinsa.


13. Da tunani yai ya duba,

Sai ya kau da wutar gabansa.By:

Murtala Uba Mohammed

11/08/2023

6:09 ny

Post a Comment

0 Comments