Ticker

6/recent/ticker-posts

Rubutattun Waƙoƙi

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Rubutattun Waƙoƙi

Waɗannan waƙoƙi mabarata suna amfani da su wajen yin bara duk da yake mawallafan waƙoƙin ba domin a yi bara da su suka wallafa su ba. Tun a can baya an ambaci cewa daga cikin mabarata masu amfani da rubutattar waƙa wajen bara akwai Gardawa, wato masu neman ilmin addini waɗanda suka zarce matakin Almajirai da kuma naƙasassu, wato masu wata naƙasa ga wata gaɓar jikinsu. Rubutattun waƙoƙin da mabaratan ke bara da su kashi biyu; na Larabci da na Hausa. Su waƙoƙin Larabci mafi yawa Gardawa ne da wasu naƙasassu da suka sami damar yin karatun addini suke amfani da su. Waƙoƙin Larabci mafi yawa sukan kasance waƙar Ishriniya ce ko ta Alburda. Su ma waɗanda ba su yi karatu ba sukan je a karantar da su wasu baitoci na iri waɗannan waƙoƙin su hardace su sami abin zuwa bara da shi. Bayan waƙoƙin Larabci akwai kuma rubutattu na Hausa waɗanda wasu malamai suka wallafa domin begen Annabi ko domin wa’azi ko ilmantarwa su je suna amfani da su wajen bara. Misali, kamar waƙar Imfiraji da wasu waƙoƙin malaman jihadi da kuma duk wasu waƙoƙi da wani malami ya wallafa ta wannan fuskar. Ko a yau aka sami wata sabuwa waƙar ta addini da wani malami ya wallafa za ka sami mabarata sun are ta suna amfani da ita wajen bara (Duk da yake mabaratan kan yi amfani da wasu waƙoƙin Larabci wajen bara kamar yadda aka ambata can baya, to amma waƙoƙin Hausa ne kawai za a kawo misalansu). Ga misalin wasu baitoci daga cikin iri waɗannan waƙoƙin rubutattu da mabarata ke amafani da su. Sunan waƙar “Lauwali”:

Post a Comment

0 Comments