Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Rasuwar Amali Sububu
Amali ya rasu ranar wata Alhamis 3/11/1995, ya rasu ne a lokacin da yake da shekaru sittin da ɗaya a Duniya a sakamakon wani haɗarin mota da ya samu bayan ya dawo daga wurin yawon kiɗinsa, sun fito ne daga wani ƙauye da ake kira Gangara wani ƙauye na cikin yankin Isa ta cikin jihar Sakkwato. An ce sun shigo motar haya ne har da wata ‘yarsa wadda take aure a can ta biyo su ne domin ganin gida, a lokacin ne har ya karɓi ɗanta wato jikansa ya riƙe. An ce a cikin wata mota a-kori-kura ne, lokacin da haɗarin zai faru sai ɗai ta ji ya ce riƙa ɗanki-riƙa ɗanki, tana riƙawa kuwa sai ya diro daga cikin motar ya faɗo! Allahu akbar! A sakamakon wannan ne ya cika. Ina roƙon Allah ya gafarta masa kurakuransa, amin.
Daga cikin yaran Amali Abu Amali (ƙanensa) shi ne ya jagoranci tawagar
kiɗan bayan rasuwarsa, wanda shi ma bai
yi doguwar gora ba, ya rasu a ranar Alhamis 15 ga watan Rajab 1440 A.H. wanda
ya yi daidai da watan Janairu 2019. Tun wancan lokacin har yanzu babu wani
wanda ya sake jagorantar tawagar waƙar, amma dai ba a ɗebe tsammanin nan gaba a sami wani daga cikinsu ya ɗauka ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.