Ticker

6/recent/ticker-posts

Soma Wakar Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Soma Waƙar Amali  Sububu

A wata hira da gidan Rediyon Rima Sakkwato ya yi da shi Amali ya faɗi da bakinsa cewa ya fara waƙarsa ne tun yana ƙarami[1], tun lokacin bai da wani abin kiɗa sai dai  kiɗa tandu[2] ko takalmi ko dai wani abu da ke samar da amo, kamar jerkokin ɗibar ruwa da sauransu. Sai daga bisani ne Amali ya fara yin amfani da duman tsaye wajen aiwatar da waƙoƙinsa.

Da farko-farkon waƙoƙin Amali yana yin su ne saboda sha’awarsa kurum ba sai an kira shi ba, Musamman idan ya ga wani ko wata ya ko ta shahara sai kawai ya yi masa waƙa ko ya ba shi kuɗi ko kuma bai ba shi ba, ko ya ba shi hatsi ko kuma bai ba shi ba, sai ya waƙe shi ya tafiyarsa ana murna ana ganin hikimomin[3] da ya saka a cikin waƙar. Amma daga baya sai in mutum ya nuna yana son ya yi masa waƙa ko kuma ya isa a yi mai waƙa ne yake yi masa waƙar, kamar dai yadda yake cewa a cikin waƙarsa ta Arzika kulkin horon jema:

    Jagora : Dauri[4] ina yaro,

: Ban san kan kiɗi ba,

: In ka ban kuɗɗi in kiɗa ma,

: Kuma ko ba kuɗɗi in kiɗa ma,

: In kab ban gero in kiɗa ma,

: Kuma ko ba gero in kiɗa,

: Yanzu da nir rege,

: Na bambanta roƙo,

   ‘Y/Amshi : Amali ya rege,

: Banza ba ta sha nai.

 

  Jagora : Amali na gane,

: Banza ba ta sha na,

   ‘Y/Amshi : Amali ya rege,

: Banza ba ta sha nai,

: Tahi gona,

: Bai san gargare ba,

: Jan zaki rana mi takai ma?

(Amali  Sububu: Arzika Kulkin Horon Jema.

Amali Sububu ya kasance makaɗi wanda yake sha’awa yin kiɗin shi kansa, a waɗannan ɗiyan waƙar ya nuna cewa a wancan lokacin bai san kan kiɗi ba, amma daga baya da ya sai wanda ya neme shi da ya yi masa waƙa yake yi masa waƙar don wata kankanbar banza bata sa ya yi wa mutum waƙa.

Haka kuma a lokacin da Amali ya fara bunƙasa sai mutane Musamman manoma suka soma raja’a wajen waƙoƙinsa, ana samun manoman da suka shahara cikin noma waɗanda Amali bai yi ma waƙa ba saboda ba su neme shi ba. Wannan bai ya rasa nasaba da irin bunƙasar da Amalin ya yi, da kuma irin yadda mutane ke son waƙoƙinsa, saboda haka idan mutum bai kafu sosai ba ba zai iya gayyato shi ba don ya yi masa waƙa. Dubi yadda ya faɗa a wata waƙarsa:

 

 Jagora : Amali kiɗinmu sai mai iyawa,

   : Kiɗinmu sai mai na kai nai,

   : Kiɗinmu sai mai riƙonmu,

: Ba ni matce ma ƙato yanai man

: ƙarya.

   ‘Y/Amshi    :  Ba ni matce ma ƙato yanai man

: ƙarya,

   : Na taho in buga mai ƙwarya,

   : Zubairu manyan manoman gero.

 

    Jagora    : Ba ni matce ma ƙato yana

: ɗangwanno[5],

     ‘Y/Amshi    : Ba ni matce ma ƙato yanai man  

: ƙarya,

   : Na taho in buga mai ƙwarya,

   : Zubairu manyan manoman gero.

    (Amali: Zubairu Mailalle)

 

A ɗan waƙar na farko Amali ya nuna cewa sai fa wanda ya kafu ke iya ɗaukar kiɗinsa ba kowa ba, ya ce baya matse ma wanda bai da komai sai ƙarya. Ƙarya a nan tana nufin rashin biyan waƙa ko da kuɗu ko kuma da hatsi. A ɗan waƙar na gaba Amali ya fito da nau’o’in mutanen da ya kamata su amfana da kiɗansa, kamar wanda ya tara gero ko kuɗi wato ya sami arziki gwargwado, irin waɗannan su ne suka dace su nemi kiɗin Amali ba ‘yan Allah ya ba ku mu samu ba. 

Wani lokacin kuma Amali yana shaƙuwa da wani manomi har ya zauna masa ga zuciya sai ya kai masa kiɗi su yi zumunci don hankalisa ya kwanta, kamar yadda yake faɗi a wani ɗan waƙar:

 

    Jagora : Gajere abun da yawa,

   : Inda baƙon Habibu,

   : Ina gida wani bin,

: Hankalina ka tashi,

   : Ga ni can wani bin,

: Zuciyata ta yo nan,

   : In biyo hanya,

: In taho in da Mamman,

: Ko da niz zaka.

    ‘Y/Amshi : Sai hankali na ya kwanta,

   : Ka yi sunan noma,

   : Mu gaisai da aiki,

   : Mai gidan Nasara,

: Ɗan da yat tara damma.

    (Amali  Sububu: Maigidan Nasara)

 

Amali mutum ne mai haƙuri da kuma ƙoƙari wajen kiɗi domin yana fita ya bar gida har ya yi kwanaki bai gida domin yawon kiɗinsa. Dubi yadda yake faɗi a cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsa:

 

   Jagora : Na biyo cikin Ɓula,

: Hak Kuka tara,

   : Girnashe ni biyo,

: Nik kwan niw wuce,

   : Na biyo Tsabre,

: Na kwan na wuce,

   : Tsabren Citumu,

: Na kwan na wuce,

   : Tsabren ɓauna,

: Na kwan na wuce,

   : Tsabren sarki,

: Na kwan na wuce,

   : Na biyo Shalla,

: Na kwan na wuce,

   : Sai na lwaye[6],

   ‘Y/Amshi : Na kwan Dukkuma.

 

   Jagora : Sai na kwan nan,

: San nan zan wucewa.

   ‘Y/Amshi : Ko can an ce,

: Komi yi sukai.

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

     (Amali  Sububu: Isah Maikware)

 

A wani ɗan waƙar kuma ya ambaci wani gari inda bai samu zuwa ba sai daga baya, dubi yadda yake cewa:

 

  Jagora: Har yar yau ban zo gidan Hanya : ba, 

   ‘Y/Amshi: Don jikan Kohwa can za ni in

 : kwana, 

 

  Jagora : Dare da rana yana gona,

   : Hussani zarton hwashin kuyye.

  ‘Y/Amshi : Dare da rana yana gona,

   : Hussani zarton hwashin kuyye.

(Amali  Sububu: Hussaini zarton hwashin kuyya)

 

Haka kuma Amali ya ambaci wani garin da ya je wurin kiɗinsa yana cewa:

 

 Jagora : Ni mai lalle can za ni in kwan,

  ‘Y/Amshi: Tun da Zubairu an ce yana nema : na.

  Jagora : Ni Mailalle can za ni in kwana,

   ‘Y/Amshi    : Tun da Zubairu an ce yana nema : na.

  Jagora: Tun da Zubairu an ce yana nema : na.

‘Y/Amshi : Tun da Zubairu an ce yana nema  : na.

   : Na taho in buga mai ƙwarya,

   : Zubairu manyan manoman gero.

        (Amali  Sububu: Zubairu Mailalle)

 

A wani ɗan waƙar kuma ya kawo wata tafiya ga alama mai nisa da ya yi:

 

 Jagora : Mun kwana munka yo sallah,

: Munka dawo,

  : Amali na yi hul-tanki[7],

: Tun da sahe,

  : Ni dai ina ta ɗora giya,

: Babu dama,

  : Mun zo Arewa mun yi kwana,

  : Munka kwan nan.

   ‘Y/Amshi : Jijjihi[8]yakai daji,

: Baya wargi,

  : Kodayaushe shi dai bai,

: San sake ba,

: In yi mai kiɗin aiki,

: Garba Dauran.

(Amali  Sububu: Garba Dauran)

 

Waɗannan garuruwa da Amali ya kawo duk ya je ne ba don komai ba sai don yawon kiɗansa na noma, wannan yana nuna cewa idan Amali ya fita gidansa yana iya shafe kwanaki kafin ya dawo gida saboda wannan sana’a tasa.

 

Ba a gida kawai ya tsaya ba har wajen jiha yakan fita Musamman idan an yi la’akari da labaran da yakan bijiro da su a cikin waƙoƙinsa. Kamar yadda ya ce a waƙa ta gaba:

Jagora : Na leƙa ƙasat Kwantagora,

  : Can ma na ga manyan manoma.

  ‘Y/Amshi : Amma ba su aikin mutanen Hausa[9].

 

 Jagora : Na leƙa ta sashen Ilori,

  : Can ma na ga manyan manoma.

  ‘Y/Amshi : Amma basu aikin manoman Hausa.

 

  Jagora : Na leƙa ta sashen Ibadun,

  : Can ma na ga manyan manoman gero.

  ‘Y/Amshi : Amma ba su aikin mutanen Hausa.

 

 Jagora : Na leƙa ta sashen Ilori,

  : Can ma na ga manyan manoma.

  ‘Y/Amshi : Amma basu aikin manoman Hausa.

 

 Jagora : Na yi Kano da waƙa da yara,

  : Can ma na ga manyan mutanena.

  ‘Y/Amshi : Amma ba su aikin mutanen Hausa.

 

Jagora : Birnin Bauchi na kwana roƙo,

  : Can ma na ga manyan manoma.

‘Y/Amshi : Amma ba su aikin mutanen Hausa.

 

     Jagora : Na Gwambe na kwana wasa,

  : Can ma na ga manyan manoma.

‘Y/Amshi : Amma ba su aikin manoman Hausa.

 

     Jagora : Na je Borno na kwana wasa,

  : Can ma na ga manyan mazaizai[10].

‘Y/Amshi : Amma ba su aikin mutanen Hausa.

 

Jagora  : Na Koma ta sashen Arewa,

  : Can ma na ga manyan manoma.

‘Y/Amshi : Amma ba su aikin manoman Hausa.

(Amali  Sububu: Zubairu Mailalle)

 

Su kuma waɗannan garuruwan da mawaƙin ya ambato a cikin waƙarsa duk a wajen jihar haihuwarsa ce, yana nufin duk ya tafi wurin yawon kiɗinsa. Amma dai wannan waƙarsa ta bayyanar da haka, muna kuma iya kafa hujjarmu da ita.

Haka kuma Amali yakan sami labarin noman manomi da ƙwazonsa har ya kai masa ƙiɗansa, dubi yadda yake cewa:

   Jagora   : Ba tun yau ba nij ji labarin,

   : Ka tara hatci.

   ‘Y/Amshi   : Ka tsere ma shakitinbau[11].

   : Riƙa da gaskiya,

   : Noma ba kashi yakai ba,

   : Yari ɗan Bagge,

   : Noma ba ya sa ka rama.

  (Amali  Sububu: Yari ɗan Bagge)

 

Idan Amali ya sami labarin cewa mutum ya girma ga aikin noma to yakan kai masa kiɗi don ya kwarzanta shi a kan wannan sana’ar tasa. Kamar yadda yake cewa ya daɗe da jin labarin tara hatsin Yari Ɗan Bagge. Wannan labarin da ya ji shi ya sa ya yi masa waƙarsa.



[1]  Hirar da Ibrahim Ahmad Isa ya yi da Amali a shirinsu na “Daga bakin mai ita” a Rima Rediyo Sakkwato a  shekarar 1994 mako biyu zuwa uku gabanin rasuwarsa.

[2]  Tandu wani mazubi ne da ake zuba man shanu, wanda iyayen amarya kan tanada dona a kai gidan ango.

[3]  Waɗansu kalamai masu daɗin ji ko na ban mamaki

[4]  Lokaci mai tsawo da ya shuɗe

[5]  Sata Musamman ta hatsi/Ƙwalto/ kala.

[6]  Sakankancewa

[7]  Cika tankin wani abin hawa mai inji da mai kamar mashin ko mota.

[8]  Sammako/ Fita tun da sassafe.

[9]  Ƙasar Sakkwato.

[10]  Mazaje/manoma/gwaraza.

[11] Raggo: wanda ba ya iya aikin noma.

Post a Comment

0 Comments