Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Mamman Mai Walkin Zomo

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Na Mamman Mai Walkin Zomo

 

  G/Waƙa: Barkan ku dai da aiki.

: Na Mamman maiwalkin[1]zomo.

 

 Jagora : Barkan ku dai da aiki.

‘Y/ Amshi: Barkan ku dai da aiki.

: Na mamman mai walkin zomo.

 

Jagora: Kai bar kan ku da aiki addai dai,

: Ko na waje damman,

: Gero nai kuma gaya,

: Da tsabar kuɗɗi nai.

‘Y/ Amshi: Ko danyi sun batai banga.

Jagora: Babu abunda ya,

: Sha kanki da Turanci,

: Babu ruwanki da na tsohuwa,

: Babu ruwanki da ɗan kowa,

: Babu ruwanki,

: Da mashal- mashal,

: Babu ruwanki da hwadanci.

‘Y/ Amshi: Kai tahi ka dara huska tai cif cif,

: Idan ta ka kware  ka hi muje ta ga,

: Allah as sarki.

 

  Jagora: Kai wanga ka zan aiki gona ,

: Don Allah kabar wasan kwana,

: A yi kwance a samu sai mata.

‘Y/ Amshi: Ko su ba’a basu gabanza ba,

: Da sun ɗaga  cinya sun ‘yamma,

: Shi ya yi ma aiki nai dai dai,

: Namman mai walkin zomo .

 

Jagora: Ba wani dare da ka sara ma zomo.

‘Y/ Amshi: Ba wani dare da ka sara ma gona.

: Ya yadda ya lalace.

 

Jagora: Kowa da abiun da ka sha mai kai,

: Kowa da abun da ka ja mai girma,

: Dan  mai ko ya ci ruwa.

‘Y/ Amshi: A’ a da yadda ga doki sai gero,

: Ka haɗa ta da nono ko tonka,

: Sannun kuka shirya wa dai dai ,

: Shi ya yiwa aiki nai dai dai ,

: Namman mai walkin zomo.

 

 Jagora: Arne  yai mana doki nai yab bai.

‘Y/ Amshi: Bai ci amanar kawu[2] ba .

 

 Jagora: Da ba ya riƙa gadon tsohonai.

‘Y/ Amshi: Arne bai saki gadon tsoho ba .

 

Jagora: Haba ya riƙe gadon tsohonai.

 ‘Y/ Amshi: Arne bai saki gadon tsoho ba,

: Yana gaba ga karni baya.

  Jagora: Ham .

 ‘Y/ Amshi: Shi ya yi ma aiki nai dai dai,

 

 Jagora: Da sana’ar mota ganganci.

‘Y/ Amshi: Ai in an riƙe riba sai buzu,

: Ko shi ra kumma nai yah hau ,

: Shi ya yi ma aiki nai dai dai,

: Na Mamman mai walkin zomo.



[1]  Warki, fatar wata dabba da aka jeme ake ɗaurawa a rufe al’aura.

[2]  Kayan kiɗan noma ko kiɗan noman kansa.


Post a Comment

0 Comments