Ticker

6/recent/ticker-posts

Muhammadu Zaɓaɓɓe

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Muhammadu Zaɓaɓɓe

Allahu na yi roƙonka ka ban iko sarki,

Ka sa ni in yi begen Muhammadu zaɓaɓɓe.

Sarkinmu na da kyauta ba za ta iyaka ba,

Ya baka babu sarkin da zai amshe ma ba.

Ni zullumin da nake na amsa kiran sarki,

Zuwa garin da ba dangi ba ka da alfarma.

Matambaya su iske ka su ce barka bawa,

Zaman da kai yi can duniya wane aiki kay yo.

In sun ishe Musulmi ne, su ce barka bawa,

Taso mu kama hannunka mu kai ka ga zaɓaɓɓe.

In sun ishe ɓatacce ne su ja shi yana kuka,

Macijiya kunamu to kun ji maƙwabta nai.

Post a Comment

0 Comments