Ticker

6/recent/ticker-posts

Jirgi Ɗan Amina

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Jirgi Ɗan Amina

Jirgi Ɗan Amina alƙawalin duniya

Allah ya yi duniya ya yo lahira,

Ita waccan ta lahira can muka dogara,

Bismillahi Rabbana kai muka roƙo,

Na roƙe ka don kana da abin roƙo,

Waƙe za ni yi ka ban ikon yi nai,

Kar mu mace muna cikin aikata ɓarna,

Kowa yam mace yana aikata ɓarna,

Shi ka ganin duhu gun kabari nai,

Jahillai ka tambaya wai a gaya masu,

Wane aiki akai a samu ganin Annabi,

Shi aikin ganin Muhammadu da yawa ya ke,

A yi sallah biyar-biyar kowace safiya,

A yi azumi a fidda zakka a tsaya kurum,

Sai mu ga ya Rasulu mai ceto lahira,

Allah sa mu gan shi ba da hisabi ba,

Jirgi Ɗan Amina Muhammadu sallallah.

Muhammadu kowag gane ka na da rabon gobe,

Allah sa mu gan shi ba da hisabi ba.

Post a Comment

0 Comments