𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum! Malam, barka da
yini. Ya gida, ya ayyuka, ya ibada? Allah Ubangiji Ya ƙara ɗaukaka.
Malam, ina da tambaya ne: Mene ne hukuncin mutumin da ya yi addu'a da harshen Hausa a cikin sallarsa?
HUKUNCIN YIN ADDU'A DA HARSHEN HAUSA A CIKIN SALLAH
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi
wa barakatuh.
Malamai masana fiƙihu sun yi saɓani
a kan hukuncin yin addu'a da harshen da ba Larabci ba a cikin sallah. Akwai
manyan fahimta guda uku a kan wannan mas'ala:
1. Fahimta ta farko:
Wasu malamai sun tafi a kan cewa ya halatta ga wanda bai iya Larabci ba ya yi
addu'a da harshensa a cikin sallah. Amma wanda yake iya Larabci sosai, bai
kamata ya yi addu'a da wani harshe ba. A wasu bayanan wannan fahimta, idan ya
yi hakan alhali yana iya Larabci, sallarsa tana iya ɓaci.
2. Fahimta ta biyu:
Wasu malamai sun tafi a kan cewa ya halatta ga wanda yake iya Larabci da wanda
ba ya iya Larabci su yi addu'a da harshensu a cikin sallah.
3. Fahimta ta uku:
Wasu malamai kuma sun tafi a kan cewa bai halatta mutum ya yi addu'a da wani
harshe da ba Larabci ba a cikin sallah, ko da kuwa yana iya Larabci ko ba ya
iya ba.
(Dubi: Al-Mawsu'ah Al-Fiqhiyyah
Al-Kuwaitiyyah, 11/172–173).
Ra'ayin
Da Ya Fi Ƙarfi
Ra'ayin da ya fi zama kusa da daidai
shi ne na farko, wato wanda bai iya Larabci ba, ko kuma bai iya kyautata furta
addu'ar da Larabci ba, yana da damar yin addu'a da harshensa a cikin sallah,
musamman a wuraren da ake halatta yin addu'a, kamar sujjada.
Dalili kuwa shi ne, Allah Maɗaukakin
Sarki Ya san dukkan harsuna, kuma Ya san abin da zuciyar mutum take nufi, ko da
kuwa bai iya bayyana buƙatarsa da Larabci ba.
Sheikhul Islam Ibn Taymiyyah (RA) ya
bayyana cewa:
“Addu'a ta halatta a yi ta da
Larabci ko da wani harshe daban. Allah Maɗaukakin Sarki Ya san nufin mai
roƙonsa da abin da yake nema, ko da harshensa bai iya bayyana hakan ba. Lallai
Allah Ya san abin da sautuka suke ƙunshe da shi, duk da bambancin harsuna da
buƙatu.”
(Dubi: Majmu'ul Fatawa,
22/489).
Haka kuma, Allah Maɗaukakin Sarki Ya
ce:
لَا
يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا
“Allah ba Ya ɗora wa rai wani abu
face gwargwadon ikonta.” (Suratul Baƙara: 286).
Shin
Wanda Ya Iya Larabci Zai Iya Yin Addu'a Da Hausa?
A nan ne saɓanin malamai yake. Wasu
sun hana hakan, wasu kuma sun halatta. Saboda haka, wanda yake iya Larabci ya
fi dacewa ya yi addu'o'in da aka ruwaito daga Annabi ﷺ
da Larabci, musamman addu'o'in da ake yi a cikin sallah.
Amma ya kamata a bambanta tsakanin
addu'a da karatun da yake wajibi a cikin sallah. Misali, Fatiha da sauran
karatun Alƙur'ani ba a maye gurbinsu da fassara ko wani harshe ba. Wannan
hukuncin da muka tattauna yana magana ne a kan addu'a, ba karatun Alƙur'ani ba.
Kammalawa
Saboda haka, wanda bai iya Larabci
ba, ko bai iya kyautata furta addu'ar da Larabci ba, yana da damar yin addu'a
da Hausa a cikin wuraren addu'a na sallah, kamar sujjada. Amma wanda yake iya
Larabci, ya fi dacewa ya yi amfani da addu'o'in da aka ruwaito daga Annabi ﷺ, tare da kiyaye bambancin da malamai suka
yi a kan wannan mas'ala.
Allah ne mafi sani.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alƙur'ani da
Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.