Ticker

6/recent/ticker-posts

Landiya

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Landiya

Landi landi landiya

Ɗan yaro bai sha ba ne

Ni han na sha na rage

Na aza bisa ragaya,

Ɗanƙane yas shanye mani,

Ɗanƙane mai kurtun ciki,

Ciki kamar ƙundun duwa,

Ɓera ya sato dame,

Ƙoƙi tana mai sussuka,

Biri da kalangu na kiɗi,

Kwarkwata da kujera na kitso,

A taru a bamu na Annabi.


Post a Comment

0 Comments