Ticker

6/recent/ticker-posts

Garba Abin Azawa Ga Gona

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Garba Abin Azawa Ga Gona

A Gidan Rijiya Garba yake Shi ne sarkin fawa garin ne, amma kuma manomi ne sosai yana noma yana samun abin aiki sosai. Amali ya yi masa waƙar noma don ya ƙara sa masa ƙaimi.

 

    G/Waƙa : Abin azawa ga gona,

: Ɗan Barmo.

  : Yi gabcen Jigawa.

 

     Jagora: Garba abin kwahewa[1],

: Ga gonaa sai sahe,

  : Yi gabce ka samo.

‘Y/Amshi: Abin azawa ga gona,

: Ɗan Barmo.

  : Yi gabcen Jigawa.

       

Jagora:  Za ni ga Garba mai kai ni wajje,

‘Y/Amshi: Yau  Za ni ga Garba mai kai ni wajje.

 

     Jagora:  Za ni ga Garba in sha gaba ɗai.

‘Y/Amshi: Yau  Za ni ga Garba in sha gaba ɗai.

  : Abin azawa ga gona Ɗan Barmo.

  : Yi gabcen Jigawa.

 

Jagora: Na gode ma ran ‘Yam magaji x2

 ‘Y/Amshi: Ba canjin sule tab biɗa ba.

  : Abin azawa ga gona Ɗan Barmo.

  : Yi gabcen Jigawa.

 

Jagora: Don Allah ka cetan ga gulbi Garba.

  : Don Allah ka hisshe ni wajje.

‘Y/Amshi: Abin azawa ga gona Ɗan Barmo.

  : Yi gabcen Jigawa.

 

Jagora  :  Za ni ga Garba mai kai ni wajje[2],

‘Y/Amshi:  Za ni ga Garba in sha gaba-ɗai.

: Abin azawa ga gona,

: Ɗan Barmo.

  : Yi gabcen Jigawa.

 

Jagora  : Garba abin kwahewa ga gona,

: Sai sahe,

  : Yi gabcen jigawa.

‘Y/Amshi: Abin azawa ga gona,

: Ɗan Barmo.

  : Yi gabcen Jigawa.x2[1]  Aza abu ya zauna daram.

[2]  Ƙarshen gona/biya masa buƙata. 

Post a Comment

0 Comments