Ticker

6/recent/ticker-posts

Zubairun Mailalle

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Zubairun Mailalle

Zubairu na garin Mailalle manomi ne sosai, garin Mailalle yana can yamma ga Sabonbirni ta jihar Sakkwato. Amali ya yi masa waƙa shi ma saboda shahararsa ga noma.

 

G/Waƙa : Na taho in buga[1] mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

 

     Jagora: Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

‘Y/Amshi: Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

 

     Jagora: Ni mai lalle can za ni in kwan,

‘Y/Amshi: Tun da Zubairu an ce yana nema na.

 

     Jagora: Ni Mailalle can za ni in kwana,

‘Y/Amshi: Tun da Zubairu an ce yana nema na.

 

     Jagora: Tun da Zubairu an ce yana nema na.

‘Y/Amshi: Tun da Zubairu an ce yana nema na.

  : Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

 

     Jagora: In mutum ya ji kainai,

  : Lalle in mutum ya ji kainai,

  : Yat tara geron dakawa,

  : Gami da kuɗɗin kashewa,

  : Yat tara mata na wari[2],

  : Yanzu kiɗinmu shi za shi ƙauna,

  : In dai ba kare za shi wa wanka ba.

‘Y/Amshi: In dai ba kare za shi wa wanka ba.

  : Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

 

Jagora: Jatau in mutum ya ji kai nai[3],

  : Yat tara geron dakawa,

: Yat tara kuɗɗin kashewa,

  : Yas sami mata na wari,

  : Yanzu kiɗinmu shi za shi ƙauna,

  : In dai ba kare za a wa wanka ba.

‘Y/Amshi: In dai ba kare za ya wa wanka ba[4].

: Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

     Jagora: Na leƙa ƙasat Kwantagora,

  : Can ma na ga manyan manoma.

‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen farko.

 

     Jagora: Na leƙa ta sashen Ilori,

  : Can ma na ga manyan manoma,

‘Y/Amshi: Amma ba su aikin manoman farko.

 

     Jagora: Na leƙa ƙasat Kwantagora,

  : Can ma na ga manyan manoma.

‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen farko.

 

     Jagora: Jatau in mutum ya ji kai nai,

  : Yat tara geron dakawa,

: Yas sami kuɗɗin kashewa,

  : Yat tara mata na wari,

  : Yanzu kiɗinmu shi za shi ƙauna,

  : In dai ba kare za a wa wanka ba.

‘Y/Amshi: In dai ba kare za ya wa wanka ba.

: Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

 

Jagora: Na leƙa ƙasat Kwantagora,

  : Can ma na ga manyan manoma.

‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen Hausa[5].

 

     Jagora: Na leƙa ta sashen Ilori,

  : Can ma na ga manyan manoma.

‘Y/Amshi: Amma basu aikin manoman Hausa.

 

Jagora: Na leƙa ta sashen Ibadun,

  : Can ma na ga manyan manoman gero.

‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen Hausa.

 

     Jagora: Na leƙa ta sashen Ilori,

  : Can ma na ga manyan manoma.

‘Y/Amshi: Amma basu aikin manoman Hausa.

 

Jagora: Na yi Kano da waƙa da yara,

  : Can ma na ga manyan mutanena.

‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen Hausa.

 

     Jagora: Birnin Bauchi na kwana roƙo,

  : Can ma na ga manyan manoma.

‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen Hausa.

 

Jagora: Na Gwambe na kwana wasa,

  : Can ma na ga manyan manoma.

‘Y/Amshi: Amma ba su aikin manoman Hausa.

 

     Jagora: Na je Borno na kwana wasa,

  : Can ma na ga manyan mazaizai[6].

‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen Hausa.

 

     Jagora: Na Koma ta sashen Arewa,

  : Can ma na ga manyan manoma.

‘Y/Amshi: Amma ba su aikin manoman Hausa.

 

Jagora: Lalle ba su aikin manoman Hausa,

‘Y/Amshi: Lalle  ba su aikin mutanen Hausa.

 

     Jagora: Na Rabi da Rabi manyan manoman Hausa,

‘Y/Amshi: Na Rabi da Rabi manyan manoman Hausa,

 

     Jagora: Na Abu da Abu manyan mazaizan Hausa

‘Y/Amshi: Na Abu da Abu manyan mazaizan Hausa,

: Sarkin daji sai in yaba mai hwama.

    

     Jagora: Ka ban zawara ‘yag garin ga,

‘Y/Amshi: Sarkin daji Mamman shina ban kwana.

  : Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

 

     Jagora: Amali kiɗinmu sai mai iyawa,

  : Kiɗinmu sai mai na kai nai,

  : Kiɗinmu sai mai riƙonmu,

  : Ba ni matce ma ƙato yanai man ƙarya.

‘Y/Amshi: Ba ni matce ma ƙato yanai man ƙarya,

  : Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

 

     Jagora: Ba ni matce ma ƙato yana ɗangwanno[7],

‘Y/Amshi: Ba ni matce ma ƙato yanai man ƙarya,

  : Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

 

     Jagora: Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

‘Y/Amshi: Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

 

     Jagora: Birnin Mailalle can za ni wasa,

‘Y/Amshi: Tunda Zubairu an ce yana nema na.

  : Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.

 

     Jagora: Na taho in buga mai ƙwarya,

  : Zubairu manyan manoman gero.



[1]  Kiɗa.

[2]  Sa’a/ ‘yan shekara ko ƙarfi ko tashi ɗaya.

[3] In mutum ya isa.

[4]  Aikin banza.

[5]  Ƙasar Sakkwato.

[6]  Mazaje/manoma/gwaraza

[7]  Sata Musamman ta hatsi/Ƙwalto/ kala.

Post a Comment

0 Comments