Ticker

6/recent/ticker-posts

Dantanaye

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma Ɗantanaye

 G/Waƙa: Ba gari daka yaron malam,

: Ɗantanaye mai tarin damma.

 

 Jagora: Na Audu duniya canji-canji[1].

 ‘Y/ Amshi: Waɗansu sun aje wasu sun ɗauka,

: Ba gari daka yaron malam,

: Ɗantanaye mai tarin damma.

 

 Jagora: Ko zamanin ana matsatsin[2] yinwa.

 ‘Y/ Amshi: Na samu mutunen nasarawa,

: Na sani basu tsoron Alhaji,

: Ba gari daka yaron malam,

: Ɗantanaye mai tarin damma.

 

 Jagora: Na tuna zamana da Ɗanduna.

 ‘Y/ Amshi: Ba abin da bai shirya mai ba.

 

 Jagora: Ya bashi kuɗi,

 ‘Y/ Amshi: Ya bashi hatsi had da riguna,

: Duk  ya bashi,

: Ba gari daka yaron malam,

: Ɗantanaye mai tarin damma.

 

 Jagora: Ina ganin  zuma da farar saƙa.

 ‘Y/ Amshi: Koda ban honi ban saran icce,

: Ba gari daka yaron malam,

: Ɗantanaye mai tarin damma.

 

 Jagora: Kai dai tunda ɗan tannin ya ɗauke ni.

 ‘Y/ Amshi: Sale sai ka ɗauki iyayen mu,

: Ba gari daka yaron malam,

: Ɗantanaye mai tarin damma.



[1]  Yau in ka samu gobe wani ya samu.

[2]  Abin da ya tsananta.

Post a Comment

0 Comments